episode 3

361 14 0
                                    

RANAR WANKA............
03
                      CIGABAN LABARI
Wasu Matasan 'yan matane da bazasu wuce shekara sha shida suka jeran akan titi suna tafiya gwanin ban sha'awa, dayar farace sol mai madaidacin fuska da manyan idanuwa tareda hanci shi ba dogoba Kuma baza'a ce mishi guntu ba, la66unanta masu kauri da kyau, ita ba doguwa hakanan ba guntuwa ba amma za'afi sakata a layin marasa tsayi, dukiyar fulani da kuqu tareda da shara6a da take dasu ne zaka ga kamar tanada jiki amma Sam batada jiki don cikinta kamar zai manne da baya, kallo daya zaka mata kasan ta hada jini da shuwa ko kanuri, ZAHRA kenan 'yar wajen Falmata.
dayan Kuma black beauty ce mai dogon fuska da masakaitan idanuwa, hancinta dogone sosai, la66unanta daidai masu kyau, gata dogowa Kuma Bata da jiki irin Coca-Cola shape nan, Maryam kenan yar wajen Sadiya.
"nifa wlh na tsani komawa gidan nan, yanzu zakaje ka tararda masifan Mama yana jiranka lodi lodi" cewar Maryam had'e da rai, dariya Maryam ta saka tace "aikuwa ya zama dole mu koma don babu wajen xuwa" tsaki Maryam taja tace" Allah Allah nake mu zana weac na tafi Abuja wajen Anty Batula" sanda suka shari kwanan gidansu kan Zahra tace "nikam Maiduguri zanje" wani kallo Maryam tayiwa Zahra tace "amma ai Mami tace Funtua zakije wajen Goggo Zainab" "mun gama magana da Abba yace Maid zanje" Zahra tayi maganar tana bude kofar gidansu.
Suna shiga falo suka samu Mama (Sadiya) na zaune tana kallon TV fuskarta a daure tamm, da harara ta musu maraba "uwar me ya zaunar daku a islamiyar" ta tambayesu rai 6ace " Ustaz Ali ne ya aikemu duba Farida batazo yau ba" Maryam ta Bata amsa, Zahra ta Dora da "Kuma ai bamu wani jimawa ba, bai wuci minti 20 muka kara ba" tsawa Mama ta daka Mata" tohm sarkin iya magana, ki tafi ki ban waje anan, ke Kuma Ummata kije bedroom dina akan bed Abdu Tela ya dawo Miki da dinkinki"
Wajen Mami (Falmata) ta nufa ta sameta tana dama fura da Nono, rumgumeta ta baya Zahra tayi tace "Mamina na dawo, inata kewarki" kin kulata Mami tayi taci gaba da aikinta, rau rau da ido Zahra tayi ta dawo gaban Mami ta zauna "Mamina laifin me nayi Miki" harara Mami ta hurga Mata tace" ina zuwa kikayi wajen Abban ku kikai karata wai nace kije Funtua" dariya Zahra tasa tace" to ai kene Mamina kin kafe" sanda Mami ta gama abunda take ta maida hankalinta kan Zahra tace" bazaki gane meyasa nace kije Funtua bane, Kinga ko wani hutu Maiduguri kike zuwa bakison zuwa Funtua, me kike tunanin yan uwan Abbanku zasuce? bakiga Maryam na zuwa ba" maganar ya shige Zahra ssai tace "hakane Kam, na fasa xuwa Maiduguri zanje Funtua, Amma wlh banajin ddin zaman wajen ne, Mama Babba tayita hantaran mutum wai bakin halinki na dauko, tohm ki naki ko naso ita kakata ce" dariya Mami tayi tace" tsufa ne ai Zahra" baki Zahra ta tura tace " ba wani tsufa iskanci dai" buge bakinta Mami tayi tace" kaifin bakinki yayi yawa, kullum abunda nake fad'a Miki kenan ki rage kaifin baki don Allah" cikin shagwa6a Zahra tace "zan rage" Furan da Mami ta gama damawa ta mikawa Zahra tace " tashi ki kaiwa Anwar" babu musu Zahra ta kar6a ta fita dashi.
Da Sallama Zahra ta shiga dakin Anwar, murmushi dauke a fuskarsa ya amsa Mata, ajiye kofin tayi ta zauna kusa dashi tace "Ya Anwar namu" dariya yasa yace "Zahra tamu, me kikeso don bakya kirari a banza" kaikaya keyarta tayi tace "Daman laptop nakeso zan karasa kallon film din nan" Jan kunnenta yayi yace" sanin hali yafi sanin kama ai, kije idan na gama abunda nakeyi zan kai Miki har bedroom dinku".
" nifa wlh na gaji Mama" Maryam tayi maganar tana hararan Ahmad dake cin abinci a gefenta, tsaki Mama tayi tayi tace" tun safe aikin uwar me kikayi idan banda bin gantaleliyar nan yawo" " idan badon Abba ba wlh dana mata iyaka da Zahra, shegiyar Yarinya gashi ta fara koya Mata rashin ji" Ahmad yayi maganar yana hararan Maryam, baki Maryam ta murguda masa, Mama tace "ai Abbanku na hana ruwa guda ta ko'ina a gidan nan Amma zanyiwa tufkar hanci" Sam maganganun basawa Maryam dadi mikewa tayi ta bar musu parlour.
Durkushe Zahra take a gaban Abbanta ta kaskantar da murya tace "Abbana" Abba (Alh Abubakar) dake karanta jarida ya dubi Zahra yana dariya yace "Mamata yau kuma waya ta6amin ke" murmushi Zahra tayi tace" Daman cewa nayi na fasa zuwa Maiduguri Funtua zanje" shiru Abba yayi na wani lokaci yace " Falmata ce ta hanaki Koh" da sauri Zahra ta girgiza kanta ma'ana "a'a" kenan, "Kinga Zahra nasan halinki nasan halin Falmata, tanaso ki nuna karamci ne baicin tasan ba ddin zaman Funtua kikeji ba, ki tashi kije ba wani Funtua da zaki, Maiduguri zakije" Abba ya karashe maganar yana daukar jaridansa "Amma Abba" "shiiiiiit" Abba ya Mata nuni da hannusa a bakinsa datayi shiru, babu yadda Zahra ta iya ta tashi ta fice
"wato Falmata kema yanxu kin fara bijirewa maganata Koh" Mami dake kwance kan kirjin Abba ta tashi a razane tace "Sweetheart ni kuwa Falmatarka me nayi" Jan hancinta yayi cikin kauna yace" calm down, nothing serious" maidata makwancinta yayi yace" kin Hana Mamata zuwa Maiduguri ba" murmushi Mami tayi tace "laah nifa ba hanata nayi ba, kawai ce mata nayi mutanen Funtua ma na bukatarta" "ita Kuma tafi bukartar Maiduguri, Sweety inaso ki gane wani abu duk yadda kika tunanin halin Mama tafi hakan wallahi, duk sanda Mamana taje Funtua banida kwanciyar hankali har sai naga ta dawo, don Allah Sweety ki daina takurawa Mamana zuwa Funtua" cikin kissa Mami ta lankwasa murya tace" Inshallah na daina ranka shidade" sumbatarta yayi a goshi yace "tare da naki

Ta Bature ce

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now