episode 01

1.2K 21 2
                                    

RANAR WANKA.............
01
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Asubar ranar Jumma'a ruwa akeyi kamar da bakin kwarya, wadda hakan ya hana mutane dayawa zuwan masallaci.
Amma hakan Sam bai hana Alh Abubakar zuwa masallaci ba, saboda bai dau hakan uzuri ba.
Bayan an idar da sallah suka dauko hanyar dawowa Shida Mallam Bukar wadda ya kasance limamin masallacin ne, a hanyarsu ta dawowa ne Mal. Bukar yace" ashe mai dakinka ta sauka daren jiya, naso tun jiyan na shigo na maka barka sai Kuma nayi baki" murmushi Alh Abubakar yayi yace" babu komai wlh, ai komai sai Allah yayi" "hakane wannan, Allah ya raya abunda aka samu ya dayyabata" cewar Mallam Bukar yana kokarin mayar da carbinda aljihu, " Ameen ya Allah, daman nima inaso na sameka har gida haihuwar Sadiya ne yasa na jinkirta, anyi min transfer zan koma Kaduna da aiki" cewar Alh Abubakar, take jikin Mal. Bukar yayi sanyi da jin wannan maganar don yayi sabo mai karfi da Alh Abubakar bama wannan ba, Alh Abubakar mutum ne mai halin daddataku, bai da matsala ko kadan tunda yake shekararsa uku a inguwar bazaka ce ga abokin fadarsa ba kowa nasane, ajiyar numfashi Mal. Bukar yayi yace "Allahu Akbar, Allah mai iko, gaskia banji dadin wannan batun ba amma bbu yadda muka iya haka Allah yayi ikonsa" jimami shimfide a fuskar Alh Abubakar yace" nima banso haka ba kawai bbu mafita, ina rokon Allah ya sadani da makobci irinka" murmushi Mal. Bukar yayi yace "nima ina yiwa kaina fatan haka".
Haka dai sukaci gaba da tattauna abun alhinin nan har suka iso inda zasu rabu, Alh Abubakar ya kama hanyarsa haka ma shima Mal Bukar.
Alh Abubakar na shigowa gidansa kukan jaririya ya mishi sannu da dawowa, da marmarinsa ya shige daki.
Matarsa Sadiya ya samu tana yiwa jaririyar wanka, zama yayi a gefensu yace " Mamma jigo wanka da safiyar nan, ga sanyi bazakai bari sai rana ya daga ba" " idan banyi yanxu ba har yaushe zanyi, kuma ai ruwan zafi ne babu yadda  sanyi zai kamata, wai nikam wani suna zaka saka Mata ne" Sadiya ta karashe maganar da tambaya, bayan Sadiya ta gama shirya jaririyarta Alh Abubakar ya karbeta yana kallonta cikin kauna" wai nikam Abban Ahmad bakaji tambayar dana maka bane?" Sadiya ta sake tunasar da Alh Abubakar.
Yana shafa kan diyarsa yace " zan saka Mata sunan Umma wato Fatima" ta6e baki Sadiya tayi tace" gaskia sai dai kayi hakuri don na riga nayiwa Mama alkawarin zan Mata takwara duk sanda na haihu, ita Umman idan yaso daga baya sai ayi Mata" limshe idanunsa Alh Abubakar yayi cikin kunan rai, don gaskia abubuwan da Sadiya take masa ya fara isarsa, Amma ya ya iya da ita Amanar mahaifinsa ce dole ya rike, hararsa tayi da gefen ido tace" bakace komai ba" bude idanunsa yayi tace "me zance Kuma bayan Hajiya Sadiya ta gama magana" murmushi Sadiya tayi tace" Kuma yau su Anty Amina suna hanya, ya kamata ayi musu delicious" kama hannun jaririyar yayi yana shafawa yace " amma dai ba irin bikin da kukayi a sunan Nasir zakuyi yanzu ba" "kada kaji da wai ma biki za'ayi na kece raini, dagani har kai bbu wadda ya ta6a samun diya mace sai wannan karon, gwara nima ina dan jefawa akan wancan juyar ce ko me zan kirata ne ohoooo"Sadiya tayi maganar cikin izgilanci, wani Abu ne ya tokaresa a kirjinsa, ya danne yace" kenan ke da 'yan uwanki zaku hada bikin don ni yanzu banda isassun kudi a hannuna duk na zuba a ginin da nayi a Kaduna" tsaki Sadiya taja tace" babu damuwa zamu hada komai Allah yasa bamu gaji tsiya ba, ko Anty Batulu ta isa ta hada komai" yana kokarin bata amsa ne wayarsa tayi kara.
Wani sanyi yaji a zuciyarsa dayaga sunan jikin wayar, da sauri ya daga Kiran da Sallama, kunne Sadiya ta baza tana son jin me za'ace a wayar Amma bataji ba" Subhanallah gani nan zuwa" wayar ya katse ya kwantar da Jaririyar akan gado ya dubi Sadiya datayi kicin kicin da rai yace "babu lafiya can gidan Falmata, zanje na dubasu" dogon tsaki Sadiya taja tace " Allah raka taki gona"

Ta Bature ce

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now