episode 12 to 17

457 17 8
                                    

[12/5, 22:29] +234 902 579 1170: RANAR WANKA..........*

             *NA*

*UMMU SUBAY'A*
*_Wattpad: Ummu subaya_*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*Page 12*
kwanaki kadan Anwar yayi matukar kokari wajen cirewa Zahra dukkan damuwanta, Zahra ta sake ssai ta daina kuka da kunshe kanta a daki saidai har yanxu tana fama da kunan zuciya Amma tana kokarin dannewa.
Jin Maryam ta dawo yasa Zahra tashi takanas har dakinsu ta sameta a falo da Mama cike da Mamaki Zahra ke kallon Maryam " Mama Maryam ce kuwa nake kallon" Zahra tayi maganar tana shafa fuskar Maryam, Murmushin Izza Mama tayi tace " itace dai Zahra, kin mancene Abuja fah ta fito Kuma ba gidan Matsiyata ta fito ba" dariya Zahra tayi don tasss ta gane manufar Maman tace "laifin dadi dai karewa gashi ta dawo zamuci gaba daga inda muka tsaya" dariya Mama tayi tace " idan badon wani uxuri ba dasai dai kuje aure Abuja ai, Amma insha Allah shekara mai xuwa sai Abuja xakuje aure" da Mamaki Zahra ta dubi Maryam ta dubi Mama tace " wai Miji Maryam din ta samu a Abuja" " ya wuce wai ai Zahra Maryam dai aure xatayi a Abuja, nasan kina karanta jarida kina Kuma jin sunan Shatteema Abdallah Shema young billionaire" Mama ta karashe maganar tanajin kanta, tabbas Zahra na ganin sunan a jaridu da dama Amma dai bata ta6a kallonshi ba sai dai labarinsa ya watsu ta ko'ina Dan gidan manyane masu madafun iko na companies a Nigeria harda kasashen ketare, jinjina Kai Zahra tayi tace "Allah ya tabbatar da alkhairi" Mama na ganin ta kunsawa Zahra bakin ciki ta tashi tabarsu da Maryam, Zahra ta dubi Maryam tace " shine babu labari" murmushi Maryam tayi tace " jira nake na huta gajiya na leka wajenki" shiru sukayi na wasu dakiku Zahra ta mike tace " ahuta gajiya" ta fice
Ita Maryam yanzu gani take tafi karfin Zahra ita ba class dinta bace, gashi ma taga Zahran ta wani rame ta kode, ita tunda taje taga gidansu Shatteema take ganin gidansu ma ya Mata local lokaci kawai take jira ta haye karagar girma, aikuwa Zahra ta fahimci hakan yadda taga Maryam din ke shashake Mata tana amsa Mata magana yasata Jan jiki da ita ta kama matsayinta
" wai meyasa bakya xuwa wajen Maryam ne Zahra" Mami ta tambayi Zahra da tayi matashi da cinyar Mamin, kwafa Zahra tayi tace " wai ni Maryam keson wulakantawa don zata auri Shatteema, kawai na sharesu da tsiyarsu" Murmushi Mami tayi tace " Zahra ki dinga daukar komai a cikin sauki, idan ta shareki ki bita watarana sai labari" ta6e baki Zahra tayi tace " wlh Mami baxan bita ba, suje can su karata, idan taga dama ta auri Dan Bill gate" dariya Mami ta dinga yi tana jinjina lamarin Zahra.
                                ABUJA
Kafar Shatteema da Umar a Maiduguri uku babu Zahra babu dalilinta gidansu ma an rushe an xamar dashi shagona, gashi su Khadija kakanansu sun daukesu balle suji wani details a kanta, haka suke hakura su dawo Abuja, tun Shatteema na saka rai har ya daina saka ran sake ganin Zahra, yayi duk yadda zaiyi ya cireta a ransa ya gaza haka ya shiga rokon Allah babu dare bbu Rana daya cireta a ransa Amma inaaa sai kara karuwa kaunarta keyi a cikin ransa, da wannan kaunar ya tafi America yin course wadda daga ya dawo sai aurensa  da Maryam, Hajiya Babba dai sai shirye shirye take tana ganin kamar ranar baxata zo ba.
                             KADUNA
Jerawa Maryam da Zahra sukayi suna dawowa daga islamiyya, babu wadda yayiwa wani magana har suka iso gida kowa ya nufi part dinsu, Zahra na shiga cikin parlour taga Anwar ya fito daga bedroom din Mami idanunsa cike da hawaye kamar xaiyi kuka, da sauri ta karaso tace " Ya Anwar lafia kuwa" gefenta Anwar yabi ya wuce bai ce Mata komai ba, bedroom din Zahra ta shiga don tambayar Mami mike faruwa, fuskar Mami data gani damuwa shimfide a kanta ya kara kidima Zahra tazo ta zauna gefenta tace "Mami lafiya naga Ya Anwar kamar zaiyi kuka, gaki Kuma damuwa shimfide a fuskarki" yake Mami tayi tace " kada ki wani damu matsalace tsakaninsa da Yayanki Nasir ba wani abu bane" tsaki Zahra taja tace " Ya Naseer nan halin Mama ya dauka baida dadi, idan da nice Ya Anwar koya masa hankali zanyi wlh, nikam yaushe ne zai koma aiki ko har yanxu bai samu sauki ba" mikewa Mami tayi ta nade Sujud tace " next week zai koma bai fad'a Miki bane" baki Zahra ta ta6e tace " tun lokacinda nace ya hakura da aikin bai karamin maganar aikin ba, da Kuma na kara cewa nikam banzan auri Soja ba shikenan abun ya ta'azzara" dariya Mami tayi tace " Kinga ke kika jawowa kanki ashe, Abbanku na nemanki maganar jamb fah" Mami ta batarda Topic din, cikin xumudi Zahra tace " tohm bara na sameshi" Kai tsaye falon Abba Zahra ta nufa, ta sameshi yana karanta Jarida tazo ta zauna kusa dashi tace "Abbana Mami tace kana nemana" murmushi Abba yayi yace " an fara registration na Jamb ki shirya gobe insha Allah zamu je na Miki" " Abba Maryam fah, ita bazatayi bane" Zahra ta tambayi Abba bayan ta tsaresa da idanuwa, murmushi ya kara Mata yace " Maryam ai aure zatayi don jibi nake saka ran za'azo tambayar aurenta, kema ba kwanki akace wani Shuwa yaso ya kwace mana ke ba" rufe fuska Zahra tayi tana dariya tace " laaah Abba duk shirmene fah, kabar maganar kawai, insha Allah zanyi karatu ssai na zama likitar da kakeso na zama na sakaka alfahari" shafa kanta Abba yayi yace " Insha Allah Mamata, Amma fah dole zakiyi aure kada kima cire aure a ranki" murmushi Zahra tayi tace " Abba ga Ya Anwar baiyiba Kuma bakwa matsa mishi sai Mata" ajiyar zuciya Abba yayi yace " komai lokacine Zahra"

RANAR WANKAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin