episode 9

247 12 0
                                    

RANAR WANKA........
Ummu Subay'a
09
flask Zahra ta dauko ta siyaye ruwan dumi ta surkashi ta dauki towel ta saka a ruwan ta matse tana shafawa Haydar a jikinsa, limshe ido Haydar yayi yanajin ddin abunda Zahra ke mishi Kuma a lokaci daya zazzabi na sauka me shi, ido Zahra ta zuba mishi tana kallon irin baiwar kyaunshi ji take kamarta hadiyesa, sanda taji jikinsa yayi sanyi kan tabar share mishi jikin, cikin sanyin murya tace" Noory tashi kaci abinci" kafad'a Haydar ya dage Mata kamar yaro yace "uhmmmm........ uhmmmm...... baxan iya cin komai ba" shagwa6ewa Zahra tayi tace" don Allah ka tashi ni xan baka a bakina idan da halima da nizan tauna maka na Kuma hadiye maka" murmushi Haydar yayi yace" tallafamin na tashi" babu musu Zahra ta tallafa mishi ya tashi tayi serving dinsa ta Kuma yi feeding dinsa, yana kallonta yanaci yana murmushi, itama murmushi taketa wankesa dashi, bai wani ci ssai yace ya koshi ya koma ya kwanta yanata kallonta "ka daina min irin kallon nan don Allah, kana tsinkamin zuciya ance wadda ya kusan mutuwa ne ke irin kallon nan" yake Haydar yayi yace "banason canfi, insha Allah kafin na mutu sai na aureki kin haifamin kyawawan yara kamarki, masu shegen surutu irinki" dariya Zahra tayi ta gyara zamanta tace" Allah ya amsa Noory"  jikin Haydar ne ya fara rawa alamun sanyi yakeji, da hanzari Zahra tazo ta zauna gefenshi tana mishi sannu, batayi auni ba kawai taga ya jata inda yake kwance a rumgumeta a jikinsa tayi ta kwace kanta amma abun ya gagara don ya sakar Mata da dukkan nauyinsa a hankali yace "ki natsu bbu abunda zan Miki duminki kawai nakeso" ajiyar zuciya Zahra tayi ta kara rumgumesa inda zaiji dumin ssai, sun dau lokaci a hakan kafin Haydar yayi bacci Zahra ta kwace jikinta ta tafi.
Kwanan Haydar hudu ya warke Kuma duk Zahra ce ke daukar dawainiyarsa, Malam ne ya Kira Taheer ya mishi bayanin zai aurarwa Khadija dalibinshi yayi hakuri da ita, Taheer baiji dadin haka ba Amma bbu yadda zai iya haka yanaji yana kallo ya rabu da Khadija, Zahra da Haydar ko cin soyauyarsu suke da tsinke hankali kwance, "wai yaushe zakaje gomben ka taho da iyayenka ayi maganar aurene, nafa kusan komawa Kaduna Kuma idan na koma abubuwa zasuyi maka wuya" Zahra tayi maganar tana wasa da yatsun Haydar, shiru na wani lokaci Haydar yayi yace "insha Allah na kusan komawa" murmushi Zahra tayi ta lankwasa yatsar Haydar yayi Kara Haydar yace "wasssh zata balla min yatsa don taga sunfi nata kyau" murmushi Zahra tayi tace "afuuwan Noory, yawwa naji jiya Ya Mala yana magana a waya wai jibi xa'a kawo musu kaya su Kuma zasu aika Chadi, sai ka fadawa hukumar suzo su kamasu red handed" baki Haydar ya tabe yace "wlh nikam har na mance wannan maganar" fuska Zahra ta had'e tace" Kai fah kace inyi taimako Amma Kai har ka manta" hakuri yayita bata dakyar ta hakura.
Duk wani Abu mafi mahimmanci Zahra ta sanarda Haydar akan gidansu Khadija a cewarta zai kaiwa hukuma
Ranar wata bakar Lahadi Zahra na zaune da Khadija a gidansu suna hira Yakura na Dan saka musu baki cikin hiran Khadija tace "jiya Mama ke fadamin wai karshen watan takwas aurena da Yaya Gana" Yakura da Khadija duk sunji mamakin maganarta Yakura tace "abun da wuri haka, kan lokacinma kawarki ta koma" fuska Zahra ta hade khadija tace "meyasa zata koma Anty?" sanda Yakura ta gama shan ruwa ta ajiye kofin tana hararan Zahra datayi kicin kicin da rai tace " munyi magana da Abbanta yace a turata an fara sayarda form" cikin damuwa Khadija tace "Ya Maganarta da Haydar fah" tsaki Yakura taja tace "idan yana sonta sai ya bita Kadunan, nifa shirme na dauki abun sun nan da Kuma yarinta irin na Zahra" kumbura baki Zahra tayi tace "wlh Anty yana Sona fah, Kuma yace yana komawa garinsu zai dawo da iyayensa ayi maganar aure" tsaki Yakura ta Kuma ja tace " rabo Dani da zancen nan lafiya yau Uncle dinki bai dawo ba har tara saura, bara na kirasa" Yakura Bata Kai ga daga wayaba Mammadu kanin Khadija ya shigo gidan da gudu yana haki yana cewa "Ya Khadija kizo ki gani sojoji da police sun kewaye gidanmu sun hanani shiga wai zasu tafi da Baba" a firgice Khadija ta tashi tace "Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un" ta fice da gudu Mammadu yabi bayanta, Yakura ma mayafinta ta dauka ta fice da gudu Zahra kam tana zaune kamar mutum mutumi ta kasa mikewa zuciyarta na bugawa "Anya tayiwa Khadija adalci? Anya bataci amana ba" tambayar da ta dinga yiwa kanta Amma babu amsa, babu laka a jikinta ta mike ta fice don duba abunda ke wakana.
Bugun zuciyarta ya karune lokacinda taga yadda jami'an tsaro suke cike a unguwar kamar yakin basasa, Bata sammaci abun yakai haka ba, tanaji wasu Mata a gefenta suna cewa "wannan abun shunene an shuna shine" sojojine suka fito da boma bomai da bindigogi daga cikin gidan tareda almajiran Mallam din da wasu daga 'ya'yanshi maza hadda Matarsa uwargida  Maman Khadija da Kuma shi Malam din duk da ankwa a hannunsu, limshe ido Zahra tayi hawaye ya shiga bin kuncinta don tasan wannan duk bayananta akayi amfani dasu" Taheer, Haydar daku aka had'a baki aka Mana haka, daman ku ba leburori bane ko jami'an tsaro ne" take Zahra ta bude idanunta dataji Kalman Khadija inda  khadijan take takai dubanta aikuwa nan tayi arba da Taheer da Haydar cikin shiga ta alfarma wani uniform ne jikinsu wadda batasan sunan force dinba, duk sun kara kyau kamar basuba, jiri Zahra ta faraji na daukarta don ta kasa gaskata kallonta.

Ta Bature ce✍🏻

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now