episode 7

273 11 1
                                    

RANAR WANKA...............
Ummu Subay'a
Wattpad: Ummu Subaya
07
Zaune Taheer da Khadija suke akan tabarma a zaurensu Khadija suna hira "wai nikam Zahra ta koma bbu sallama ne" Taheer ya tambayi Khadija, Khadija tace" a'a tana kawai Antynta ce ta hanata fita" zaro ido Taheer yayi yace "amma dazun da na tambayi Mustapha cemin yayi wai ta tafi Bama duba kakanenta" tsaki Khadija taja tace "bara na fad'a maka gaskia kaga Ya Mustapha nan ba karamin munafuki bane, maganar gaskia anan Kuma son Haydar yayiwa Zahra mugun kamu har yana so ya nakasata, shine sai Mustapha ya fahimta ta hanyar yawan tambayarta ku datakeyi, yazo ya sami Anty Yakura ya fad'a Mata ita Kuma tace bazatabar Zahra ta janyo Mata abun kunya ba sai ta hanata fita, dazun danaje ma cemin tayi wai Mamanta tace zata koma Kaduna wannan satin" kallo daya zakayiwa Taheer kasan maganar ta shiga jikinshi tausayin Zahra ya lullubeshi ssai a sanyaye yace "yanzu Khadija kin San mayuwacin halinda Zahra ke ciki baki sanar Dani tuntuni ba" baki Khadija ta tabe tace " banga amfanin sanar dakai bane ai, tunda na fuskancin Haydar halin yahudu ne dashi ko yasan Zahra na sonsa ba sonta zaiyi ba, kaga bbu amfani badi bbu rai, yanxu ma ina fad'a maka saboda tafiya Zahra zatayi" har yanxu jikin Taheer a sanyaye yake yace "shikenan, wato na Miki tambaya shine kikaki ki bani amsa Koh" had'e rai Khadija tayi tace" wai maganar kayanda aka shigo dasu daren jiya?" daga kai Taheer yayi alamar "eh" kamar bazatayi maganaba Khadija tace "litattafai ne aka kawowa Baba daga Saudia abunda yasa kaga an rufesu kada suyi kura ne, Amma meyasa ka matsa sai kaji mene?" murmushi Taheer yayi yace "zuciyata ta tsinke ne, na zata kayan aurenki aka kawo don kada na gani aka rufe" dariya Khadija tasa tace" bakada damuwa wlh" .
Ana washegari Zahra zata tafi cikin dare tana had'a kayanta taji muryan Khadija a falo, Bata damu da ta fita ba ba don tasan xata shigo, aikuwa sai gashi ta shigo fuskarta cike da fara'a ta kama hannu Zahra "ke don Allah bar had'a kayan nan muje Taheer nason ganinki" harara Zahra ta hurga ma Khadija tace" ki rabu Dani uwar me zanyiwa Taheer" murmushi Khadija tayi tace" kizo mana muje don Allah" badon Zahra naso ba ta bi Khadija, "ina Kuma zaku?" Anty Yakura ta tambaya, Murmushi Khadija tayi tace " zatayi sallama da Taheer ne" tsaki Yakura taja tace " kada ku jima" suna fita Zahra tace " Matarnan akwai cin rai" dariya kawai Khadija tayi.
Kamar a mafarki Zahra ke kallon Taheer da Haydar a gefensu, uku uku zuciyarta ya dinga bugawa tace" Khadija me Kuma ya kawo Haydar nan" Khadija dai bata bata amsaba har suka iso inda su Taheer suke, a bayan Khadija Zahra ta boye suka gaisa Taheer yace " Anty Zahra haka zaki tafi babu sallama" murya a sanyaye Zahra tace " tafiya da sallama neman guzuri" dariya Taheer yayi yace" naji a gari ance so ne zai koreki daga Maiduguri" leko fuskar khadija Zahra tayi tace" wayace" magana Haydar yayiwa Taheer a kunne Taheer yace" Khadija mu basu waje Koh" babu musu Khadija ta bi Taheer suka jera.
Zahra ji take kamar ta nitse don kunya tareda fargaba, bugun zuciyarta karuwa yayi lokacinda taga Haydar na kokarin kusantota, limshe ido tayi ta waresu taga ya wuce ya zauna a bakin dakalin kofar gidansu ya Mata nuni tazo ta zauna, babu musu Zahra taje ta zauna gefenshi kamar mafarki take ganin abun, limshe ido Zahra tayi tana sauraren muryanshi mai zaki da natsuwa yana Mata bayani " Zahra kina Sona meyasa baki fadamin ba? bakisan hakan cutarda kanki kikeyi ba" hawayene ya shiga gangarowa akan kuncin Zahra a sanyaye tace "nayi yunkurin hakan amma yadda naga yanayinka shiyasa na hakura" kara sanyaya muryansa yayi yace " Zahra mutane namin mummunar fassara akan halina, ni mutum mai saukine kawai banason hayaniya ne" murmushi Zahra tayi tace "gashi cikin kankanin lokaci na fara fahimtar hakan" ajiyar numfashi Haydar yayi yace "Zahra tun kafin ki fara Sona na fara sonki, tun ranar da kukazo shago da Khadija nake dakon sonki" kamar a mafarki Zahra take Jin wannan kalaman dakyar ta saita kanta tace "to meyasa baka sanar Dani ba" "saboda akwai bambanci tsakaninmu, ni ba kowa bane Kuma ba d'an kowa bane, ni leburane mara galihu Kuma Dan cirani, can cikin rugan fulani a Gombe dangina suke, bana zaton akwai macenda zata soni a haka" Haydar yayi maganar yana duban Zahra wacce itama shi take duba, cike da shagwa6a Zahra tace "daman wanna dalilen da basu da ma'ana ko tushe ka hananin samun sanyin zuciya na tsawon lokacin nan, Zahra tsakani da Allah take sonka bada wani dalili ba, Nima ba d'iyar kowa bace indai xaka soni ka Kuma kula Dani ya wadatar" Zahra ta karashe maganar cikin yanayin natsuwa, haka sukayita fallasa sirrikan zukatansu har dare yaja sukayi sallama, Zahra ji take kamar anyi Mata bushara da gidan aljanna, tsawon dare tana tufka da warwarar yadda xata watsar da tafiyarta ta gobe ne, sanda ta samawa kanta mafita kafin ta iya bacci cike da annushuwa
Da Asuba Zahra ta samu Bukar mijin Yakura ta kora mishi bayani daga farko har karshe, ssai Bukar ya tunxura ya Kira Yakura ya Mata tatas, ya Kuma Kira Falmata a waya yace Mata shi ya amince da zabin Zahra Kuma sai tsaya mata, Mami batayi musuba tace" Allah ya xa6a mana mafi Alkhairi"

Ta Bature ce✍🏻

RANAR WANKAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt