episode 11

268 13 1
                                    

RANAR WANKA............
Ummu Subay'a
11
Kwance yake da alama tunani yakeyi babu zato babu sammani yaji an yayyafa mishi ruwan sanyi a jikinsa, ajiyar zuciya yayi mai karfi kafin yaga wacce ke gabansa kamar yadda yayi sammani Hajiya Babba ce tsaye a kansa fuskarta bbu alamun wasa tace "inaji ai daxun nace maka ka shirya yarinyar da Hauwa ta za6a maka tana xuwa ka kalleta shine ka maidani shegiya" mikewa Shatteema yayi ya rumgume Hajiya Babba a shagwa6e yace "Yumma ba haka bane wlh gajiyace tamin yawa, bafa hutu naje ba aiki naje nayi fag" tsaki Hajiya Babba taja tace" Kai ba namiji bane, Yalla sakeni kaje ka shirya tun kan Abbi ya 6ata maka rai" cikin shagwa6a ya saketa ya nufi bathroom,  da kanta ta cire mishi kayanda zai saka ta fice
Hajiya Babba na zaune a falonta na alfarma Shatteema ya shigo cikin tafiyarsa ta izza yazo ya zauna a gefen Hajiya Babba ya kwantarda kansa akan kafadarta yace " I miss my Yumma" shafa gashinsa irinta ta larabawa Hajiya Babba tayi tace "she's also missed you" shigowar Hajiya Hauwa da Maryam ne ya sakasu duk xubawa Maryam din ido, tashin farko Maryam ta burge Yumma daga natsuwarta har shigarta, shiko Gogan kallo daya ya Mata ya dauke kai, durkusawa Maryam tayi a kasa ta kwashi gaisuwa Hajiya Babba tace "taso ki zauna akan kujera" cikin sanyin murya Maryam tace "a'a nan ma yayi" babu yadda Hajiya Babba batayi ba Amma samm Maryam taki hawa kan kujera murmushi Hajiya Hauwa tayi tace "Maryam din kenan akwai hankali ga kunya" itama Hajiya Babba murmushin tayi yace "ai nagani da idona" yan aikine sukazo suka cika gaban Maryam da kaya motsa baki amma Maryam taki cin komai Kuma kanta na kasa taki dagowa, shiko Shatteema latsa wayarsa kawai yake yana ta6e baki, da ido Hajiya Babba tayiwa Hajiya Hauwa nuni da su basu waje, babu musu Hajiya Hauwa ta mike ta fice, Hajiya Babba ita ma ta mike ta fice.
Babu abunda kakeji a falon sai karar message dake shigowa wayar Shatteema da alamu chatting yake hankalinsa kwance, daga ido Maryam tayi ta saci kallonsa, nan zuciyarta ta fara bugawa don bala'in kyaunsa ya birkitata, nan take kibiyar sonsa ya harbeta taji kawai ya Mata 💯 , duk yadda Mommy ke Mata kwatancensa ya zarta haka kyau da kwarjini, na mujiya ta xuba mishi Bata ko kiftawa" Ban fiyason kallon maita ba" Shatteema yayi maganar a dakile, cikin kunya da tsoro Maryam tayi kass da kanta, tashi Shatteema yayi yabar falon ko kallon inda take baiyiba.
Hajiya Babba tayi na'am da Maryam don ta yaba da natsuwarta da hankalinta data tambayi Shatteema yace idan ta Mata Shima tayi mishi, ssai Hajiya Hauwa tayi murna da amincewarsu.
Hajiya Babba na zaune kan sofa tana kallon peace Tv murmushi ta shigayi tareda da amsa sallamar da aka mata " Bin Affan kaji abunda ya faru kenan" murmushi ya shigayi yana tsotsa keya yazo ya durkushe gaban Hajiya Babba "Eh wlh dazun ya kirani yake ban labari, zanso naga wannan yarinya mai sa'ar nan" dariya Hajiya Babba tayi tace " rufemin baki duk hakinku daya saura kaima kwanan nan zan taya Hajiya Binta yaki akanka" mikewa Umar yayi yana dariya yace " nikam basai kunsha wahala ba da kaina zan kawo" dakuwa Hajiya Babba ta mishi tace " mara kunya" dariya yayi ya fice.
Shatteema na kwance kan resting chair yana jin wakar Muhammad Daudi na Habibi yana ratsashi idanun shi a limshe Umar ya shigo ya sameshi, tsayawa Umar yayi a kansa na wani lokaci kafin ya bugi kafadarsa, ware idanunsa Shattema yayi yaga Umar ya kuma limshewa zama Umar yayi a gefensa yace "Man kamar Yarinyar nan ta tafi da zuciyarka gaba daya?" tashi Shatteema yayi ya zauna ya ware idanunsa ya kuma kashe wakar da yakeji  ciki ya dubi Umar kamar zaiyi kuka yace "Anya Man yarinyar nan ba aljana bace, wlh ban isa na rintsa ba sai nayi mafarkinta, tunaninta ya addabe ni, a sanadin hakan ne yasa na amince da zabin Yumma may be idan nayi auren zan mance da ita" ajiyar zuciya Umar yayi yace " tun farko sanda na fad'a maka we should not involve innocent soul amma kace idan bada itaba we can't achieve our goals, to gashi we achieved our goals gaka cikin damuwa, Zahra tayi yarinya da zakayi wasa da feelings dinta, wlh babu ko tantama Allah ne ya kamamu" jinjina kansa Shatteema yayi yace " Tabbas Allah ne ya kamani, Wlh sonta nake kamar zan mutu, ina mafita?" shiru sukayi na dan wani lokaci Umar yace " mezai hana mu koma Maidugurin mu sameta, nasan Zahra na sonka kuma Yarinya ce kodon sonda take maka zata yafe maka" girgiza kai Shattema yayi yace " idan mun koma ita wannan fah Maryam ce ko me sunanta fah, kasan baxansawa Yumma hope akanta a banxa ba" tsaki Umar yaja yace " be a Man don Allah, kaifa mijin mace hudu ne" dariya Shatteema yasa yace " you're not serious Man kasan bazan iya auren mata biyu ba, let me take a shower mu leka company".
Mommy taso ayi auren cikin gaggawa amma wani aiki daya tasowa Shattema na gaggawa yasa aka saka auren wani shekara Maryam ta koma Kaduna

                              KADUNA
Tunda Zahra ta dawo ta rufe kanta a daki taki fitowa sai kuka take tayi babu irin bakinda Mami bata bataba amma sam Zahra taki daina kukan, yadda abun ya gudana ya matukar firgita Zahra idan ta tuna yadda Haydar ya yaudareta sai taji kamar ta hadiye kanta.
Anwar ne ya shigo falo ya samu Mami ta xabga tagumi, cire hannunta yayi akan kuncinta yace" Haba Mami yau ke kike tagumi, me yayi zafi haka?" cikin damuwa Mami tace " lamarin Zahra ke damuna Anwar, kasanta da saka abu a rai ta saka wannan shaidanin a ranta yaki fita" limshe idanunsa Anwar yayi yace" kada ki damu Mami xan sameta na lalla6ata" tashi Anwar yayi ya shiga dakin Zahra da sallama.
A ciki ciki Zahra ta amsa cikin muryan kuka, zama a bakin bed Anwar yayi ya dubi Zahra yace " Fatima yanxu akan wani dan iska can daban zaki dagawa Mami hankali, yaushe kika hadu dashi yaushe ta dasa miki sonsa har ya goge namu a cikin ranki, ki tuna fah yaci amanarki ta cuceki ya kuma yi amfani da so ya tafi ya barki, haba Zahra ki tausayawa Mami mana" kuka mai karfi Zahra tasa ta fado jikin Anwar tace " Ya Anwar ka taimakeni, na rasa mekemin dadi a rayuwa, inama da zan mutu dana huta" rumgumeta Anwar yayi sosai a jikinsa yace " kiyi shiru insha Allah zan cire mikishi a zuciyarki amma sai kin bani hadin kai, yanzu tashi kiyi wanka ki shirya mu fita outting" janye jikinta Zahra tayi tace " tooh".

Ta Bature ce✍🏻

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now