Chapter 29

11.7K 1K 82
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

            *SOORAJ !!!*

     *Written By*
phatymasardauna

*Dedicated To My life (Sardauna)*

               *Wattpad*
        @fatymasardauna

#romance

            *Chapter 29*

"I love you!!!"  ya faɗa slowly yana me murza yatsun hanunta dake cikin nasa.

Da sauri ta ɗago golding eyes ɗinta ta kallesa, wani irin abune taji yana yawo acikin jikinta,  sam batasan me yasa wani yanki na zuciyarta ke ƙoƙarin  accepting ɗinshi ba,  hannayenta dake cikin nashi ta soma ƙoƙarin zarewa, babu musu yasake hannun nata, sai dai kuma be janye mayun sexy eyes  ɗinsa daga kanta ba.    Murmushin daya bayyana kyawunta tayi tare da miƙewa tsaye,  batare da ta kalleshi ba tace  "Zan koma class"
Shima miƙewa tsaye yayi tare da ɗan sakin murmushin daya sanya dimples dinsa loɓawa,  wani farin envelope yazaro daga cikin aljihunsa, wanda aka ƙawata bayan envelope ɗin da zanen flowers masu sheƙi, gwanin burgewa, miƙa mata envelope ɗin yayi,    ɗago ɗara ɗaran idanunta tayi ta ɗan  kalleshi,  mumushi yayi mata kamar zai shige jikinta haka ya sake matsowa gaf da ita, yanayin idanunsa ne suka sauya, take taji wani sabon abu na sauƙa ajikinta.   "Pleaseee!!" yaja maganan tare da ɗan ƙanƙantar da idanunsa.   Adaburce tashiga kakkare jikinta, sam bata sabayin irin wannan kusancin da wani namiji ba, gaba ɗaya duk abun da Farouk keyi mata ganinsu take wasu daban, kowacce kalma da zata fito daga bakinsa jinta take tayi mata nauyi,  takan rasa nutsuwarta idan taganshi akusa da ita sosai, domin wani irin faɗuwar gaba takeji,    ganin irin mood ɗin data shiga yasanyashi sake kamo soft hand ɗinta, envelope ɗin ya ɗaura mata akan hanunta, tare da bin kyakkyawar fuskarta da ido,    sam batasan da yaushene kuma ya akayi taganta tana tafiya ba, sauri tashiga yi burinta ɗaya taganta acikin class, gaba ɗaya ma ta manta da cewa basuyi sallama ba.  Shikuwa Farouk wani killer smile ya sake bayan yaga shiganta cikin class, baisan me yasa ba hakanan yake losing control ɗinsa idan yana kusa da ita,   ayanda ya fahimce ta  yarinyace wacce take real innocent, batasan komai agame da soyayya ba, da wannan daman zaiyi amfani wajen koya mata sonsa, zai koya mata yanda zata sosa fiye da kowa, daga ƙarshe kuma zaiyi ƙoƙari wajen ganin ya sameta amatsayin Mallakinsa,  sosai yake sonta, sosai yake kuma son kasancewa tare da ita.  Da wannan tunanin ya ƙarasa wajen da yayi parking motarsa.

Kamar wacce aka jefo haka ta faɗo cikin class ɗin, ko izinin  shiga  ajin bata nema ba.    da yake a bencin gaba suke kuma malamin dake cikin class ɗin,  gaba ɗaya hankalinsa naga board yana rubutu, shiyasa bai kula da shigowanta ba harta zauna,    kallonta  Shukra da Nasmah sukayi,  cikin ƙasa ƙasa da murya Nasma tace.  "I hope ba wani abun kikayi ba, naga jikinki duk yayi weak"

Sai alokacin taɗan soma dawowa sense ɗinta, murmushi ta ƙaƙalo tare da girgiza kanta alaman babu komae. Nasmah bata sake cewa komai ba ta maida hankalinta ga karatun da ake musu.

Duk abunda Malamin Chemistry ɗin ya koya musu ta bayan kunnen Zieyaderh yabi ya wuce, sam ko kaɗan hankali da tunaninta ba akansa suke ba, tunaninta yayi nisa ne izuwa wani waje daban, Farouk shine wanda yayi tsaye aranta.

"I love you!!!"
kalmar daya furta  mata shiketa dawowa  cikin tunaninta, lumshe beauty eyes ɗinta tayi tare da sakin wani murmushi wanda batasan da bayyanarsa ba,  hakanan taji wani sanyi aranta, sosai daɗin kalman ke ratsata,  kulawa shine abun da ta rasa tun tana ƙarama, kalmar Soyayya kalmace da babu wani wanda ya taɓa furta mata shi, hakan yasa takejin ayanzu tamkar wani kyautan farinciki Farouk ya bata,  duk da cewa  kai tsaye bazata iya tantance me takeji agame dashi ba, amma tabbas zuciya koya take tanason me kyautata mata,  tana a wannan tunaninne har malamin chemistry ɗin yafita batare da ta saniba, kasancewar period ɗinsa ya ƙare,  dafa ta da Shukra tayi shi yayi sanadiyar ɓacewan tunanin da take.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now