Chapter 43

13K 1.2K 265
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

                *WATTPAD*
          @fatymasardauna
#romance

               *Chapter 43*

Juyi take tayi akan ɗan madaidaicin gadon, yayinda gaba ɗaya nutsuwarta ke neman yin ƙaura daga gareta,   ahankali take buɗe idanunta har ta sauƙesu akan Nina wacce ke zaune akan gado tana faman lumshe idanunta,  wayarta ƙiran iphone ne kare akan kunnenta, waya takeyi me ratsa zucia, kasancewar ɗakin ya ɗauki shiru, sannan ta ƙure volume ɗin wayan, hakan yasanya gaba ɗaya maganan da akeyi mata acikin wayan yake fitowa fili, kalaman soyayya saurayin nata ke zazzaga mata, yayinda gaba ɗaya maganganun nasu ya ƙare akan maganan aurensu da kuma ɗokin burinsu nason kasancewa tare daya kusa cika.
Ahankali ta janye idanuwanta daga kan Nina tare da ɗaura hannunta akan maranta dake yi mata ciwo, kusan kwana biyu kenan tanajin mararta na ɗaurewa, gawani irin baƙon yanayi da takejin kanta aciki,  idanunta ta sake lumshewa tana mejin daddaɗan ƙamshin jikinta na  cakuɗa da numfashinta, ita kanta yanzu ƙamshin da takeyi na matuƙar yi mata daɗi, gefe guda kuwa ga skin ɗinta daya ƙara kyau yayi santsi da laushi,  zuwa yanzu rabin rayuwarta cike take da kewa, wani irin son ganinsa takeyi, akullum gizo idanunta keyi mata na ganinshi, bata taɓa mantawa da kyakkyawar fuskarsa, kyawawan idanunsa masu ɗaukar hankali, harma da kyakkyawan nagartarsa, komai nasa me kyau ne, tanason komai daya dangance sa,, ahankali wasu siraran  hawaye  suka gangaro daga cikin idanunta, kana suka biyo ta gefen ƙuncinta,  ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da wani irin numfashi, bata iya seccond 1 batare da ta tunasa acikin ranta ba, da tarin tunaninsa acikin rai da zuciyarta bacci ɓarawo ya sace ta..

Yau ta kama saura sati guda aurensu, sosai take shan gyara awajen Hajiya Arabi, zuwa yanzu idan kaga Zieyaderh sai kasha mamakin irin kyaun da tayi, fatarta tayi smooth yayinda duk wata halitta ta cikar ƴa mace dake jikinta suka sake ciccikowa, fatarta takoma milk colour wato kalan madara, ita kanta tasan ayanzu kyawunta ya ƙara bayyana, kuma ayanzune takejin kanta cikakkiyar mace.

Shirin biki ake sosai yayinda Oummu ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayawa amarya kayan da zata sanya alokacin biki, gaba ɗaya ahalin Oummu da Abba cike suke da farinciki saboda auren, kowa ka gani acikin Familyn burinsa shine yaga anyi auren lafiya.
***
Cike da masifa Inna Ma'u ke duban Malam Garba, cikin tsananin Mamaki tace.
"Kasan mekace kuwa? aure fa kake cewa zakayiwa Zieyaderh!"

Kallonta Malam Garba yayi cikin nutsuwa yace. "Ƙwarai Aure zanyi mata kuma saura kwanaki shida aɗaura mata aure inaso kisan da haka, yanzu ma na faɗa miki ne saboda karkice ban kyauta miki ba"

"Kam bala'i lallai Malam kacika butulu,  yanzu ni Ma'u ni zakayi wa butulci? Har kasa auren ƴarka ka kuma karɓi kuɗin auren ka cinye batare da sanina ba? to wallahi bazai taɓa yiwuwa ba!" Cikin tsananin masifa Inna Ma'u ta faɗi haka.
Cikin nutsuwa Malam Garba yace "Ki kwantar da hankalinki Ma'u, auren Zieyaderh babu fashi Insha Allah za ayishi, yanzuma burina shine na saida gona ta don na saya mata ƴan abubuwan buƙata kama daga kan kayan ɗaki dadai sauransu"

Cikin mamaki Inna Ma'u tace "Gonarka kuma? Lallai ma Malam, akan auren wannan gantalalliyar yarinyarne har zakace zaka saida gonarka, to bazai taɓa yiwuwa ba!"

Kallonta kawai Malam Garba yayi tare da yin shiru, don acikin abun da yayi niyya babu wani wanda zai fasa, dole zai sauƙe haƙƙin Zieyaderh dake kansa amatsayinsa na uba.

Ganin yaƙi kulata yasanya tasa masa kukan munafurci  tare da cewa.
"Nagode ae saboda banice na haifi Zieyaderh ba shiyasa kakemin haka"  
Shidai har yanzu idanu kawai ya zuba mata, don sarai yasan kukan munafurci takeyi, don ahalinta babu wani abu ɗaya wanda baisani ba, ganin da tayi cewa yaƙi kulata ne yasanya tasake taso da wani sabon borin inda tashiga haɗa kayanta wai lallai sai dai ya kaita birni ayi bikin da'ita.
Shidai ƙala baice mata ba baikuma sa aransa cewa zaikaita ba don yasan zuwanta bazai zama alkhairi ba.
***
Oummu ce zaune akan gado tana ta faman har haɗa kayan ɗinkin Zieyaderh wanda aka kawo mata ɗazun, Abba ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, Oummu naganinsa ta saki murmushi tare da ƙarasowa garesa, murmushin dake kan fuskar nata ne yaɗan gushe, ganin yanayin yanda fuskar Abba ta sauya, alamun akwai damuwa.
Cikin kulawa tare da ƙaunar mijin nata ta kamo hannayensa, haɗe da dubansa tace
"Lafiya kuwa?"

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now