Chapter 33

11.4K 1.2K 111
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

         *WATTPAD*
   @fatymasardauna

#romance

*This page is dedicated to my Brother HAMEED ALI (@Hameed29) I really ❤ You Brother*

              *Chapter 33*

Wani irin jiri ne ke ɗibansa, duhu shine abun dake neman mamaye ganinsa,  jin duniyar yake gaba ɗaya tana juya mai, da ƙyar ya iya buɗe ƙofar ya fito hannunsa dafe da kansa.  Jefa ƙafafunsa kawai yakeyi batare da yana kula da inda yasa gaba ba,  da ƙyar ya iya kawo kansa wajen motarsa,  yana shiga yayi mata key.     Sam baya wani iya ganin gabansa da kyau, yanayin yanda gateman yaga yayo kansa da motar ne yasanya babu shiri da sauri ya buɗe masa gate, mamaki kwance akan fuskarsa na irin tuƙin gangancin da yaga yanayi.

Da wani irin speed yake tuƙa motar shikansa baisan wani irin gudu yakeyi ba,  babu babban abun tashin hankali da tsoratarwa kamar yanda ƙwayoyin idanunsa suka rikiɗe suka zama jajur dasu, gaba ɗaya jijiyoyin dake jikinsa duk sun tashi sunyi raɗo raɗo, mussamman forehead ɗinsa wanda jijiyoyi suka fito sukaɗi raɗa raɗa.   Irin gudun da yakeyi akan hanya ne, yasanya  mutane da yawa ke kauce masa,  da ƙarfi ya daki gate ɗin gidan wanda don kansa saida ya buɗe,   aguje mai gadi ya fito don kowa yaji irin dukan da akaiwa gate ɗin yasan ba lafiya ba.  Da gudu yashigo cikin gidan kodamuwa da gaban motarsa da ya lotse baiyi ba.  Wani irin bahagon parking yayi. 

Ummu da Almustapha ne suka miƙe atare sakamakon  jin yanda aka buga ƙofar falon da ƙarfi, waigawansu yayi daidai da shigowansa cikin  falon,  ƙirjin Ummu ne yashiga bugawa da sauri ganin yanda yake tafiya yana gauraya hanya tamkar wanda ke cikin  maye, sannan kuma ga hannunsa  dafe da  forehead ɗinsa.

"SOORAJ!" Ummu taƙira sunansa aɗan razane.

Bai waiwayo ba baikuma tsaya da tafiyan dayake ba kana kuma bai amsata ba, ya nufi hanyar da zata sadashi da ɗakinsa.

"RAJ!" Almustapha yaƙira sunansa,   kamar yanda bai amsa Ummu ba haka bai amsawa Almustapha ba, haka  ya buɗe ƙofar corridor ɗinsa ya shige.  Da sauri Ummu tarufa masa baya,  baifi saura taku uku tsakaninsu ba ya shige cikin ɗakinsa tare da murzawa kofar key,   mamakine ya kashe Ummu hakan yasa ta tsaya cak, don tunda ta haifeshi bata taɓa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba. 

Ajikin ƙofar ya zame tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa.    "Me yasa bazaka fito ka faɗawa duniya cewa kai ba Namiji bane?  RAGO!"   waƴannan kalaman suke ta yawo acikin brain ɗinsa suna me hautsina duk wani lissafin nutsuwarsa.   Idanunsa da suka kaɗa suka zama jajur ya buɗe tare da sauƙesu akan mirror, zumbur kamar wanda akawa allura haka ya tashi ahankali yashiga takawa har ya ƙarasa gaban mirror'n,  tsayawa yayi yana me kallon kansa, da sauri sauri yashiga cire rigan dake jikinsa, take murɗaɗɗen surar jikinsa da buɗaɗɗun muscles ɗinsa suka bayyana acikin madubin, 6 packs ɗin dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa yakai hannu ya shafa,    ɗauke hannunsa daga cikinsa yayi ya taɓa fuskarsa da tayi jajur tsaɓan tsananin ɓacin rai da yake ciki.

"DA GASKE KAI BA NAMIJI BANE!!"
Zuciyarsa tafaɗa masa haka batare daya shiryawa jin hakanba, wani irin ihu yayi tare da sanya hannunsa ya naushi madubin, take ya tarwatse awajen,  hannunsa ne ya shiga ɗigar da jini amma ko ajikinsa,  wani ƙaton glass wanda yake kamar madubi ansanya rose aciki ya ɗaga tare da wurgi dashi,  ƙaran fashewan Glass ɗin take ya cika ɗakin,    tamkar wani zararre haka SOORAJ yaci gaba da wurgi da duk wani abun daya gani, gaba ɗaya ya watsar da kayan shafan dake kan mirror'n sa, kalmar da akace shiba Namiji bane, ita ce kawai keta yawo acikin brain ɗinsa, haka yakeji kamar zai haukace.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now