Chapter 53

17.2K 1.2K 168
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ!!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*Wattpad*
@fatymasardauna
#romance.

*(Gabaki ɗayan wannan fejin sadaukarwa ne agareka HAMEED, ina maka fatan farinciki me ɗorewa a iya ka tsawon rayuwarka.!❣️)*

*Chapter 53*

Sosae duka motoci biyun ke fitar da hayaƙi, kasancewar ba kaɗan ba motocin sukayi mummunan buguwa, hayaƙi ne ke cigaba da fita sosai ajikin motar kowannensu, cikin matsanancin sauri, haɗi da gaggawa, ƴan sandan dake gadin area'n, suka taho domin bawa waƴanda ke cikin motar taimakon gaggawa, domin kuwa nanda wasu lokuta idan wani bai taimaka ba, lallai gaba ɗaya motocin zasu iya kamawa da wuta, cikin sauri da dabara haka ƴan sandan nan suka shiga ƙoƙarin fito da kowannensu daga cikin motar, gaba ɗayansu babu wani wanda yake da alaman numfashi ajikinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata fuskokinsu, har takai ga baka iya tantance kamanninsu, Ambulance ƴan sandan suka ƙira take cikin ƴan mintuna ƙalilan aka zo aka kwashesu dukansu, Kaitsaye babban privet hospital ɗin dake cikin garin Abuja wato Nizamiyye Hospital aka nufa dasu.
Direct Emergency aka wuce dasu, lokaci ɗaya aka soma basu taimakon gaggawa.

Zaune take akan stool ɗin dake aje gaban dressing mirror, sanye take da towel ajikinta, yayinda jikinta ke ɗauke da danshin ruwa, da dukkan alamu fitowarta daga wanka kenan, ahankali take murza sassanyan body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi ajikinta, harwani ɗan lumshe idanu takeyi, saboda sosai ƙamshin body lotion ɗin keyi mata daɗi, har takai tanajin batason daina goga maiɗin ajikinta, koda ta kammala sama sama ta shafa powder akan kyakkyawar fuskarta, wani ɗan light pink lipstick ta goga akan ƴan madaidaitan laɓɓanta, black eye pencil ta ɗan goga acikin idanunta, mascara tasanya taɗan taje eyelashes ɗinta, take suka ƙara mimmiƙewa sukayi zara zara dasu.
Kallon kanta tayi amadubi naɗan wasu sakanni kana ta lumshe idanunta, moment ɗinsu na ɗazu ne kawai ke yawo acikin brain ɗinta, sosai takejin daɗin kasancewa dashi, domin aduk sanda take tare dashi takanji wani abu na musamman na yawo cikin jikinta.

Ahankali ta tashi daga kan stool ɗin inda ta nufi gaban babban drawer ɗinsu, ɓangaren kayanta ta buɗe inda ta zuba musu ido, tunanin wanda zata saka take, nan dai ta zaro wata doguwar rigar atamfan ABC, wanda take da kalan blue wato shuɗi, sosai zanin keda kyau, yayinda aka shumfuɗa mata wata haɗaɗɗiyar straight gown me kyaun gaske, rigar irin doguwar nance, sosai kuma aka fitar da shape ɗin ta, yayinda gefe da gefen rigar dama da hagu suka kasance atsage, tun daga ƙasa har gefe da gefen cikinta abuɗe suke, wani dogon pencil crazy jeans ta sanya, tare da ɗaura tsagaggen doguwar rigan akai, sosai tayi kyau, musamman yanda haɗaɗɗen shape ɗinta ya bayyana ta cikin tsagun rigar, dayake jeans ɗin yakama jikinta sosai, parking dogon gashin kanta tayi yayinda ta naɗeshi a tsakiyar kanta, wani ɗan madaidaicin blue vail ta yafa akanta, wanda ya kawo har kan cikinta, sosai tayi kyau cikin shigarta ta, ƙarasawa gaban mirror tayi tare da ɗaukan body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wanda akullum ƙamshinsa ke ƙara zautar da ita ta fesa ajikinta, wani flat shoe tasanya aƙafanta, cikin nutsuwa ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta fice, kaitsaye ɗakin da zai sadata da babban falon na Oummu ta nufa, taku biyu ya rage mata taƙarasa zuwa cikin falon taɗan tsaya, daidaita nutsuwa haɗi da tafiyarta tayi, sannan ahankali tatura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Zaune ta samu Oummu acikin katafaren falon nata, fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata sallaman da takeyi, cikin ladabi haɗi da biyayya ta ƙaraso har gaban Oummu, durƙusawa tayi tare da gaisheta, cikin sakin fuska Oummu ta amsa mata, tare da tambayanta ya take, cikin yanayi naɗanjin kunya Zieyaderh tayi ƙasa da kanta, haka Oummu ke ta janta da hira, itakuwa har cikin ranta kunyan Oummu takeji musamman idan ta tuna abun daya faru daren jia atsakaninta da Mr.Helper. Wayar Oummu dake aje bisa kan dinning table ne tasoma ruri alaman shigowar ƙira, Da sauri Zieyaderh ta tashi don ɗauko mata wayan, sam tamanta cewa agaban Oummu take hakan yasa take taka ƙafarta ahankali, duk dama bawani zafi takeji sosai acikin jikinnata ba.
Da kallo mai ɗauke da tsantsar nazari Oummu ta bita, wani tunani dayazo cikin ran Oummu ne yasanyata sakin murmushi mai ɗauke da tsananin jin daɗi, daidai lokacin Zieyaderh ta dawo hannunta ɗauke da wayar Oummu'n, cikin ladabi ta miƙawa Oummu wayar tare da dawowa ta zauna, da sallama Oummu ta amsa wayar, saidai jin abun da ake faɗa mata acikin wayar yasanya ta miƙewa tsaye, cikin tsananin fargaba haɗi da tsoro tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!." Wayar dake saƙale akan kunnen nata ne ya sulale ya faɗi ƙasa, take idanunta suka cika tab da ƙwalla, cikin fargaba Ziryaderh ta kalli Oummu'n, ji tayi gabanta ya faɗi take wani irin tsoro ya shiga jikinta, hakanan tunaninsa ya faɗo mata arai, jikinta na rawa taƙaraso kusa da Oummu'n, kallonta Oummu tayi take kuma saitaji wasu irin hawaye mssu ɗumi sun gangaro daga cikin idanunta, wani irin matsanancin tausayin kansune ya kamata, ganin hawaye na fita daga cikin idanun Oummu yasanya taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta.
Hannu Oummu takai ta dafa kafaɗan Zieyaderh wacce itama idanunta sun cicciko da hawaye, duk da kasancewar ma batasan menene ke faruwa ba, daidai lokacin akaturo ƙofar falon aka shigo, Mas'oud ne ya shigo shima fuskarsa ɗauke da tsananin damuwa haɗi da tashin hankali, Oummu naganinsa taƙaraso garesa cikin sauri da ruɗewa takamo hannunsa, murya ɗauke da rauni tace.
"Mas'oud, SOORAJ!."
Idanu Mas'oud ya lumshe cike da tausayinsu, cikin son kwantar wa da Oummun hankali yasanya hannunsa ya share hawayenta,murya ƙasa ƙasa yace.
"Muje mu dubasa Oummu."
Da sauri Oummu tajuya ta haura sama don ɗauko mayafinta.
Zieyaderh kuwa gaba ɗaya kanta ya kulle, jin an ambaci sunan SOORAJ,yasanya jikinta ya ɗauki rawa, sosai wani irin tsoro ya shigeta, bata fatan jin cewa wani mummunan abune ya sameshi, bazata iya jurewa ba, sam bazata iya jure abun da zai cutar mata dashi ba.
Oummu ce ta sauƙo daga kan mattakalan cikin sauri, ƙoƙarin yafa ƙaton mayafinta tayi, cikin kulawa ta dubi Zieyaderh dake zaune idanunta cike da ƙwalla, hannayen Zieyaderh'n ta kamo, duka suka ɗunguma sukayi waje, cikin motar Mas'oud suka shiga, dawani irin speed Mas'oud yaja motar, kai tsaye Nizamiyye hospital suka nufa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now