Chapter 49

15.4K 1.3K 149
                                    

  🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ!!!*

      *Written By*
  Phatymasardauna

*Dedicated To My Life Sardauna*
   
               *Wattpad*
        @fatymasardauna
#love

Kuyi hakuri nasamu mistake wajen yin update amma yanzu na gyara.

               *Chapter 49*

Idanunsa ne  suka kad'a sukai ja,  lokaci guda gargasan dake kwance  ajikinsa suka mimmik'e,  idanunsa ya rumtse,  yana  mejin wani irin abu da ya taho ya tokare mak'oshinsa.
Cikin yanayi na tsoro ta shiga girgiza kanta,  da k'arfi ta fusge hannunta dake cikin nasa, hawayene suka shiga gangarowa daga kan fuskarta,  cikin sauri ta juya da niyar barin wajen,    idanunta ne suka sauk'a akansa, inda yake zaune cikin motarsa yana kallonsu, wani irin bugawa k'irjinta yayi, take wani irin mummunan fad'uwar gaba ya rusketa, wasu sabbin hawayene suka kwaranyo daga cikin idanunta,  zuwa kan fuskarta.

Wani  k'awataccen murmushi Pharouk yasake,  tare da d'an satan kallon SOORAJ wanda ke zaune acikin motarsa,  inda ya d'auke kae yayi kamar ma baigansuba,  murmushin mugunta Pharouk yayi, yana mejin wani irin sanyi na ratsa zuciarsa,  komai da gangan yayi, don kawai ya k'untata zuciyar SOORAJ d'in,  yanasane da Zuwan SOORAJ d'in shiyasama ya rik'o hannayenta,  duk da cewa sha'awar da yakeyi mata nada yawa, amma kuma awani b'angare na zuciyarsa yanajin soyayyarta,  hannunsa yakai da niyar sake tab'a hijab d'inta, saidai yayi rashin sa'a don kuwa tuni tasoma tafiya, hannayensa ya zura cikin aljihun wandonsa inda ya k'urawa bayanta ido,   tsoro fargaba sune abun da suka cika zuciyarta, cikin yanayin sanyin da jikinta yayi ta k'araso jikin motar,  cikin tsoro ta bud'e murfin motar,  Sassanyan k'amshin turarensa da ya bugi hancinta ne yasanya tsikar jikinta mimmik'ewa, cikin rashin kuzari ta shiga cikin motar,  kafunma tayi yunk'urin daidaita zamanta yafigi motar da wani irin speed,  kan Pharouk dake tsaye yayi da motar, ihu Zieyaderh tasanya tare da rumtse idanunta, don taga dagaske kan Pharouk d'in ya nufa,  saida yakawo gaf da Pharouk d'in sannan ya taka wani irin birki Wanda yasanya harsaida kanta ya bugu da gaban motar,   Ido cikin ido suke kallon juna shida Pharouk d'in,  wani irin kallo Wanda ke k'unshe da zallan gargadi SOORAJ ya watsawa Pharouk, tare saying wani irin reverse, murza steering mota yayi,  cikin wani irin speed yanufi hanyar fita daga cikin makarantar yayinda ya bud'awa Pharouk k'ura, daga kan jikinsa harzuwa kan fuskarsa,  da gudu masu gadin gate d'in makarantar suka mammatsa gefe, sakamakon ganin yanda motar tayo kansu.

Da k'arfi Pharouk ya rumtse idanunsa,  yana mejin wani irin bak'in ciki na ratsa zuciyarsa, kallon jikinsa yayi,  gaba d'aya kayan jikinnasa sun b'aci da k'ura,  ransa ne ya b'aci,   saidai kuma tunawa dayayi cewa ya isar da sak'on da yakeso na bak'in ciki azuciyar SOORAJ, yasanyashi jin sanyi a ransa, haka yashiga motarsa yabar makarantar, zuciarsa na k'issima masa abubuwa da yawa.

Sosai ta tsorata da irin gudun da yake shararawa akan babban titin, cikin rufewar ido yake tuk'i, gaba d'aya jikinsa rawa yake, matsanancin b'acin rai ne kwance akan kyakkyawar fuskarsa,  sosai zuciyarsa ke tafasa, wani irin d'aci yakeji amak'oshinsa,  idanunsane suka sake kadawa sukai ja,  yayinda jijiyoyin dake kansa suka mimmik'e  inda suka fito sukayi rud'u rud'u.

Sam bayako iya ganin gabansa da kyau, dayawan motoci ke kauce masa ahanya, don kuwa kowa yaga irin tuk'in da yakeyi yasan bana lafiya ba.

Wani irin mahaukacin horn yake dannawa kamar zai dage unguwar bak'i d'aya,  da wani irin hanzari maigadi ya wangale masa gate d'in gidan,  dan shi kansa ya tsorata da irin yanda maigidannasa ke danna horn kamar zai tashi sama.

Dagudu yatura hancin motar ciki,  wani mahaukacin parking yayi,  inda ko second d'aya bai k'ara acikin motar ba ya bud'e murfin motar ya fice,  wasu sabbin hawayene suka silalo daga cikin idanunta, sosai tahango matsanancin fushi akan fuskarsa , jikinta amatuk'ar sanayaye ta bud'e murfin motar ta fito.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now