Na Uku

2.1K 32 3
                                    

꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁

*MIJIN BAABATA*
꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁

~SEX AND ROMANCE~
*Farin Jini writer's Asso..*
_Na faso Fa! Hajiya da zafi Na , Kar Young lady tabi tawaga ta! Abin na Manyan Mata Ne! ₦300 Naira 2389596965 Aisha jubreel zenith Bank, or MTN , ku Tura shedar biya ta wannan number 09079740079.. Yan Niger zaku tuntub'i Maimuna Matar Abdullahi +22780229915.._
3️⃣ Kwace hannu Ameerah tayi tare da juya mishi Baya "Daughter.." juyowa tayi ta zuba mishi sexy eyes d'inta "Abba ka bud'e Maamah taje Aikinta kasan yanda take son Aikin bana so kullun kuna samun sab'ani bana jin dad'i ace kullun makota suna juyo Fad'ar iyayena Kayi hakuri da duk abinda take maka" d'an murmushi yayi Sannan ya rike hannunta "Princess ke yarinya ce bazakii fahimta ba, Amma kamar yanda kikace d'in zanyi hakuri sai dai yau Kan na rantse ne Babu inda Rabi'atu zataje" Bud'e motar shi tare da Shiga, Bayan i'tama ta Shiga a Hankali yake tukin har suka isa Gadon Kaya family house d'insu da Maman Bauchi sukaci Karo Yayar shi, sun isketa zaune tana karyawa a Falon Daada Mahaifiyarsu, Fuskanta d'auke da fara'a Tace "Lale marhaban da Bakin Anguwar can Zo Nan 'Yata" komawa jikin Mahaifinta tayi tare da noke kafad'a Ameerah Kenan Haka take bata da sabo iyayenta kad'ai take sakewa dasu kodan bata Saba zama cikin mutane ba ne, Hararanta Maman bauchi tayi Sannan ta mayar da dubanta Zuwa gareshi ganin baya cikin wal-wal "Man ya dai da sammako Haka?"

Jan Kujeran dake gefenta Yayi ya zauna tare da zuba Abinci Yana Kallon yanda Ameerah take manne da shi domin rashin sabo ne da i'ta "Barka Yaaya an tashi lafiya? Ya gida da kwanan Su Aayma?" Batare da ta Amsa mishi gaisuwar da yake mata ba, Tace "Au Daman Baku karya bane..." Daada dake fitowa ta karb'i maganar "Anzo cinye min Abincin Gida ko? Mijin Yar Boko da alama Halin nata ya motsa ne tunda Yau naga kishiyar" murmushi yayi Yana Sosa kai tare da rusunawa Yana gaisheta amsawa tayi tana Kallon Ameerah "Ina kwana kishiya me kananan i'do yau dai gaki a gidan da bakya Ƙaunar zuwa me Halin uwarta mutum Sam sam baya Ƙaunar shiga mutane sai kace kura.." turo baki Ameerah tayi "Toh zaki Fara daga Zuwa kin sako zance Maamah nide Ahir d'inki wlh dan kinsan na fiki kyau, wai kaka Kinga ma idonki kuwa Wallahi kaman Na 'ya'yan kifi" ta fad'a tana murkud'a baki

"Ahh! Naji dai Amma kinsan na fiki kyau ko? Mummuna da dakananne Hanci..." Buga kafa Ameerah tayi a k'asa "Abba kana jinta ko kullun bata da aiki in nazo Gidanta sai zagina ni wallahi tashi mu tafi mu Koma Gidanmu" ta fad'a tana jan Hanunshi dariya Maman bauchi tayi "Princess kyale Daada tana jin haushi ne dan mijinta yafi sonki maza zoki ci Abinci Uncle Nass ya kaiki makarantan"

Ganin ya tura mata plate gabanta yasata sakin ihu tare da wurgi da jakarta "Lahhaula fii sha'atullahi Eyyeh! Usmanu wani i'rin Tarbiya kuke yiwa 'Yar Nan Haka?" Cikin jin haushi Ameerah tace "to waini Ina ruwanki dani ne Kaka kin fiya Shiga abinda ba ruwanki fa Abba ni in ba Zaka bani ba, wlh ban Cin abincin Allah yasa ma yayi dad'i domin Daada Banda jagwal gwalo me ta i'ya "Kinci gidanku dan Ana wasa dake bawai zaki Raina Mana uwa Bane na fad'a miki maza saka hannu kici abinci lokaci na tafiya" Maman bauchi ta fad'a tana bud'e mata i'do komawa tayi Jikin abbanta ta b'oye fuskanta "Yi hakuri princess kyale su zo muci abincin mu"

"A'a na koshi bazan ci ba" Cike da rigima ta mike "Ni kazo mu tafi Allah bazan zauna Gidan Da ba'a Sona ba" lallashinta ya shigayi suna kallonsu ganin yanda yake Bata hakuri tana botsarewa da kyar dai ya shawo kanta taci abincin Nasiru ne ya shigo "Yau Manyan baki ne a gidan Namu Haka? Princess d'in Abbanta" d'an dariya tayi Sannan tace "Uncle ba Sallah ya gari? Ya tashi sallah tsakar Rana" Zama yayi kusa dasu "Lafiya lau Yan matan Abbanta ya karatu da Aunty Rabi'atu aikuwa jin an ambaci sunan Mahaifiyarta ya sata Kallon Maman bauchi dan tasan Abbanta Najin maganarta Marerece Fuska tayi Sannan ta kalli Abbanta Sarai Ya Gane nufinta makullin motarshi Ya bawa Nasiru "Maza hanzarta ka kaita makaranta tayi latti.." Kallon Maman Bauchi tayi Sannan ta fara Magana a Hankali "Maman Bauchi Dan Allah kice Abba ya bud'e Maamah taje Aiki ya kulleta a gida kuma kullun fad'a sukey..." Tashi Uncle ya kaiki makarantan Abbanta yace Yana tsareta da i'do zatayi magana Daada tace "Tafi makarantan Yanzun zai je ya bud'e ta"
"Yauwa Kawata Ashe Akwai sauran Kirkin.." Kama Hannunta Uncle Nass yayi suka fita "Ke ko? Ance miki ana Fadan matsalolin iyayene sai ki zauna ki tsuke bakin Nan kaman wacce bata Magana Nan kuwa surutun tsiya ne" rike K'ugunta tayi tana Hararan shi "Eh d'in ni surutu kai ba Sallah kullun sai An watsa maka ruwan sanyi Zaka tashi da tsakar Rana kana Sallah Allah uncle Nass matarka ta bo nu" ta karasa maganar tana dariya

MIJIN BAABATAWhere stories live. Discover now