20

677 5 0
                                    

2️⃣0️⃣
Magani ta mika mata Amma sai taki amsa ta k'agu ta sanar da i'ta Labarin iyayen nata “Ungo Kisha mana zan sanar miki ai” karb’a tayi sai dai zata sake magana Dr Halirah tace “Ki kwanta ki huta...” da sauri ta dakatar da i'ta dacewa “wlh babu kwanciyar da zanyi sai kin Sanar min taya Kika samo su ya akayi Kuma Dr da Yallaɓai suka zama iyayena bayan Basu suka haifeni ba, idan na fahimce ki shi yasan ni ba 'Yarshi bace, Amma i'ta Dr fa?”
“Hakane i'ta har yanzun bata san bake bace 'Yarta domin ta rasa nata d'an ne bayan ta haihu domin sun d'auki Shekaru kusan shida bata samu ciki ba, to da Allah ya bata ta d'auki soyayyar Duniya ta d'orawa cikin sai dai, koda tazo Haihuwa d'an baizo da rai ba, ga wahalar da tasha domin sai da aka tsagata ganin Haka yasa Hankalin Yallaɓai tashi babu B'ata lokaci ya Nufi Gidan marayu a lokacin ke Kuma mahaifin ki ne, ya kaiki, domin suna cikin matsin rayuwa Basu da halin da zasu kula dake Shi Kuma Yallaɓai Usman ya karb’e ki ya kawo wa matarsa a madadin Abinda ta Haifa sai dai Kuma koda tazo Baki no-no sai kika ki amsa Rabi'atu bata damu ba, domin baso take halittan jikinta ya lalace ba, musammam ma nunuwanta..”
“Amma shi yasan bashi da halin kula dani ya samar dani? suna Raye  bawai sun mutu bane suka mayar dani marainiya wannan ba hujja bace Akwai dai abinda yasa Suka nisanta tsakani na dasu, bawai don talauci ba, ai Akwai hanyoyi dayawa da zasu bi ganin basuyi ciki ba...”
Daga bakin kofar Mahaifinta yace “Yarinya Bakiyi kariya ba, Amma a lokacin i'ta mahaifiyarki Bata da ishashshen lafiyar da zata shayar dake ni Kuma bani da hanyar da zan samu kudin da zan siya miki Madara da Sauran abubuwa 'Yan uwana kuma Basu bani fiskan da zan kaiki garesu ba, sai kawai na yanke shawarar kaiki Gidan marayu acan ne zaki samu duk wani kulawan daya dace sai dai Koda na kaiki, Yan uwana suka min caaa Akan me Zan yanke hukunci ni d'aya dana koma sai sukace wani yazo sun bashi rik'on ki Bayan wani lokaci na sake komawa Amma ba labari domin matar farko dana Kai Mata ke ba i'ta na samu ba, lokacin da hatsari ya had'a mu ganin farko nasan kece sai dai bani da karfin gwiwar da zan karb'e ki, Sabida Koda na bincika sai naga ba karamin soyayya da riritaki suke yi ba, dalilin dayasa ban tunkaresu da maganar ba Kenan, ina zaune sai ga Halirah kasancewar gidan Mahaifiyarta na makota da namu shine ta sanar min abinda ke faruwa domin tun baya da sukayi Magana da Yallaɓai Usman ta shiga bincike sai da ta samo mu sai naga Ashe ma mun San juna da i'ta wannan shine,   Abinda ya faru, sai kuma na samu Mummunan labari, wanda banji dad'insa, sai dai babu yanda zanyi domin bawa bai isa ya tsallake kaddararsa ba, wannan shine kalan naki kaddaran...” kallonsu nake ina jin Babu dad'i a raina ganin yanda suka wofantar dani nayi imani da Ina tare dasu hakan bazai faru dani ba, (Ni kuwa nace koda kina gurinsu baki i'sa ki tsallake hukuncin Allah ba) “Toh Amma menene dalilin dayasa aka yi sanarwan na mutu?” Asiya (Mahaifiyar Ameerah Kenan) tace “Sabida samun nutsuwarki da kwanciyar Hankali, Kuma muna bukatarki kusa damu shiyasa mukace Halirah tace kin mutu Bayan Kuma Dogon Suma kikayi da farko ke d’ince aka kai musu sai dai daga baya akayi musanya aka Basu wata gawar..."
“Allah me iko!”. Ameerah tace tana share gumin dake karyo mata Se kallonsu take tana godiya ga Allah sai dai, Zuciyarta cike take da kewar Maamah duk Randa tasan i'ta ba Yarta bace ya zatayi? Duk da babu mugun shakuwa a tsakaninsu kasancewar ba zaman gida take ba, Amma akwai fahimtar juna sosai a tsakaninsu a Hankali ta kwanta kasancewar cikin jikinta yazo Mata da matsaloli da yawa Karshe ma ana tunani in watan haihuwar nata ya tsaya tsaga za'a mata yanzun damuwarta d'aya ya-ya Makomar abinda zata haifa? Shege ne ko me...” zancen zuci ne ya fito fili domin ta d’auka a Zuciyarta take maganar sai dai jin Furucin Dr Halirah yasa ta d’ago tana kallonta cike da mamaki “Ki daina shegenta cikin dake jikin ki, domin da ubansa Kar na sake ji kinyi i'rin wannan furucin..”
“Aunty Kenan cikin da bata hanyar data dace aka same shi ba..”
“Hamm”. Kawai Dr Halirah tace sannan tabar mata d'akin tunda ta tsinci kanta a gidan ko leka falo Bata tab'a yi  b’oyeta ake gudun abinda zaije ya dawo bayan kwana biyu iyayenta suka d'auketa Zuwa Gidan su, Kallon gidan tayi taga da bambamci akan Kwanaki da suka zo “Amma sai Naga kamar an yi Gyara a gidan?” Mahaifiyarta wacce take kiranta da Inna tace “d'an Gurin Baffanki Al'ameen shi ya mana wannan gyaran” Gyad'a kai Ameerah tayi yanayin Gidan ya burgeta komai na dai-dai talaka akwai Extra d'aki Nan aka gyara mata murmushin tayi Sannan tace “Rayuwa Kenan babu yanda baya juya mutum yau nice zanyi Rayuwa Anan?" Kallon d'akin tayi tana tunanin Rayuwarta na baya da yanda d'akinta yake komai na more Rayuwa akwai shi duk abinda ake siyawa 'Ya'yan Gata Yallaɓai da Dr sun zuba mata, dafatan da Mahaifiyarta tayi ne yasata sakin ajiyan zuciya “Masu i'ya Magana suka ce wanda ya tuna bara be ji dad'in bana ba, wannan maganar hakane domin yau gaki a Kango zakiyi rayuwa cikin ahalinki wanda Basu da komai sai rufin asirin ubangiji kiyi hakuri, Kuma kiyi kokarin cire wancan rayuwar a zuciyarki, ki gogeshi ki manta da kin tab'a Rayuwa dasu” murmushi nayi sannan na zauna a bakin katifar batare da nace mata komai ba,
Bayan kwana biyu 'Yan uwa nata shigowa sai dai Duk wanda yaga tukeken Cikina tambayar Ina mijina ake min bana i'ya cewa komai Domin bani da amsar tambayar Inna takan ce musu Rabuwa mukayi Rayuwa cikin dangi Akwai dad'i domin ta ko'ina son faranta min ake cikin Kwanaki kalilan na saki jikina sai dai ban fiya Dogon surutu ba, Da Al'ameen yazo mun gaisa daga Gaisuwa ban sake cewa komai ba, kasancewar ina zaune a falo gashi babu kowa dan Inna ta Shiga makota barkan Haihuwa Baba kuma yaje inda yake Gadi ,  k'asa k'asa yake kallonta Yana murmushi “Sannu Ameerah ya karfin jikin?” K'aina na k'asa nace “Da sauki” Jinjina kai yay kafin yace “Masha Allah ko Akwai abinda kike bukata?”.
Da sauri nace Masa “A'ah” zai sake magana saiga sallamar Inna “Lale barka Al'ameen ya ka baro mutan Gida” Da murmushi ya amsa mata sannan suka gaisa Nan suka Fara Hira jefe jefe Yana Kallon inda nake tare da sako ni cikin hirar daga Eh sai A'ah  nake tankawa in Kuma abin dariya ne sede na murmusa kawai shima dan Inna na Gurin ne mikewa nayi tare da Gyara mayafin Abayan jikina domin bani da wani kaya sai shi ko na saka riga T-shirt da fallen zani sune suke d'aukan jikina “Ana Hira Ina zaki je dawo ki zauna Mana ko kin fi so Kita zaman d'aki kina saka gizo da koki”
d’an B'ata fuska na nayi Ina Hararan inda yake domin ya takura min da kallon tsiya  “Zanyi Sallah ne”. Ina Gama fad'ar Haka na wuce cikin Gida nayi alola Zama nayi saman sallaya domin Lokacin Sallah baiyi ba, Bansan tsawon lokacin daya d'auka a gidan ba, domin Ina idar da sallar la'asar barci ya kwasheni sai da Inna ta tashe ni domin Magariba ya gabato wanka na shiga, kafin na kammala har ta kimtsa min d'akin ta ajiye min abinci tare da Kayan fruit , banci abincin sosai ba, domin Nafi son Kayan fruit d'in , Sannu Sannu lokaci ke tafiya yayinda Cikina ke sake fitowa sai dai kullun cikin fargaba nake a gefe guda kuwa wani rawan kai Al'ameen keyi domin tunda ya lura Ban damu da Cin abinci ba Haka zai je ya jigo kayan marmari rigis duk inda yasan ana samun wani abin kwad'ayi na Masu ciki sai yaje ya kawo min ko kaɗan baya burgeni domin tsarinsa bai min ba, in yazo gidan gaisuwa ne kawai a tsakaninmu domin bana sake mishi. Yau tunda na tashi bana jin dad'i Amma sai daurewa nake dan banson d'agawa Inna Hankali ina kwance ta shigo d'akin “Ameerah lafiya de yau ko falon Baki leko ba?” ta fad'a tana kallon ta “Wlh Inna nagi Nan dai bana jin dad'i ne..” da sauri tace “Subahanalillahi Shine Bakiyi Magana ba? Kode haihuwar ne..” cije baki nayi sakamon murd'awa da naji marana yayi fita tayi can sai Gata tare da Baba ruwan rubutu ya bani nasha Nan take zufa ya karyo min “Sannu Allah ya Raba lafiya Asiya kin Kira Halirah kuwa...” bai rufe bakinshi daga Magana ba suka tsinkayo sallamarta “Ina ga muje asibiti zaifi…” Inna tace “Kai Halirah Abar zancen Asibitin nan insha Allahu zata i'ya” fita Baba yayi a d'akin yarfe hannu na shigayi ga zufa dake sake karyo min “wayyo Zafi wayyo zan mutu Abba ka cuce ni jikina sai bud'ewa yake Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alul hzana idha shi'ta sahlan” Addu'ar data dinga karantowa kenan Hawaye na zubo mata lallai Mata na kokari ta jin jinawa uwa taci uwar wahala kafin Allah ya Sauketa lafiya Yarinyar Na fad'owa kuwa da ihunta ajiyan zuciya Ameerah ta sauke tana kallon Inna dake share Hawayen tausayinta “Sannu Mamana Allah ya barmin ke wallahi Ina sonki...” cikin murya i'rin na wanda yasha wahala tayi maganar “Allah ya miki Albarka Ameerah Allah Kuma ya raya abinda aka samu”
“Humm" kawai nace Dr kuwa d'aga yarinyar tayi tare da kallon Ameerah bayan an gyara gurin d'aurata tayi a kirjin Ameerah “Sannu da kokarin Daughter Ga yarinya Nan Masha Allah tamkar Usman domin kuwa Photo copy d'inshi ce bakin ne de naki Allah yasa Kar ta Mana tsiwan nan..” ta Karasa maganar tana dariya rufe i'do Ameerah tayi ta rasa yanayin da take ciki Farin ciki ne, ko bak'in ciki i'ta de Gata Nan ne de shafa kan yarinyar tayi addu'ar Allah ya rayata a zuciyarta wani i'rin mugun tausayin yarinyar ne ya lullub'eta jin yanda take sauke a jiyan zuciya sai da Dr Halirah tayi mata duk abinda ta dace kafin tabar Gidan tana komawa gida ta kunna data tare da posted yarinyar a status a k'asan Hoton tayi rubutu kamar haka _“Masha Allahu, mun samu K'aruwa d'iya mace 'Yar da ba'asan da wanzuwarta ba, Ina fatan Allah ya shiryata Shirin addinin Musulunci i'ta da Sauran Yaran musulmai baki d'aya Meead kenan! Alkawari, Allah yayi sai kinzo gashi kuwa kin iso cikin k'oshin lafiya Allah ya bawa Mahaifiyarki lafiyar kula dake..”_ send tayi tana murmushi aikuwa kaman had'in baki mutanen da tayi don su suna online Dr na cikin Aiki taji massage alamar sako kasancewar Bata fiya rufe datar ba, kai hannu tayi tare da d'aukan wayar tana dubawa taci Karo da Hoton wani i'rin Bugawa zuciyarta yayi da sauri tayi mata magana tana mikewa “Tsarki ya tabbata ga Allah d’iyar waye haka Kyakkyawan?”
“d’iyar me shi mana haihuwa aka mana a gida ko zaki Zo Mana barka ne?” Halirah ta mayar mata da amsa da Emoji dariya (😀) , “Kai wallahi har naji  ina son Haihuwa zanzo ki duba lafiyata domin Ina son na haihu nima kalli 'Ya Kyakkyawan kamar a bani (😿)”
Halirah tace “Kai kawata wani haihuwa Kuma? Ai ki zauna kawai Serah ta haifo naji Kwanaki wai tayi b’ari Kila ma tana da wani mak’alalliya yanzun” tsaki Dr Rabi'atu tayi cikin jin haushi tace “Yade b’arar mata mutum da shegen jaraba” daga Haka ta sauka dariya Halirah ta dinga mata a falo kuwa Yallaɓai na zaune rik'e da waya shima Yana Kallon Hoton Yarinyar da aka nad’eta a Farin towel Kurawa lips d’in yarinyar yayi i'do Zuciyarshi ya tsinke “Sak Meerah!” yarinyar ta mishi kyau Kuma ta zauna a ranshi sa
Addu'ur barka ya tura Mata kamar Haka, “Barakallahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu.." fuska d’auke da murmushi ya tura sakon tana bud'ewa tayi dariya “Baban baby da kansa Allahumma Ameen Mungode..”
Da murmushi ya ajiye wayar Haka kawai ya tsinci kanshi cikin farin ciki fita yayi duk inda yasan zaiga mabukaci Nan yaje Yana raba kudin da baisan adadinsu ba kafin ya dawo gida ya Nufi d'akin Dr har yanzun tana bakin fama “Sannu agogo me batir d’inki baya lalacewa ne da bazaki huta ba?” murmushi kawai tayi tare da kallonshi “d’azun Naga Halirah ta saka yarinya wai an sun samu karuwa wa ya haihu?”
“Na sha'afa ban tambayeta ba wlh, yarinyar Kan tabar kallah tana da kyau”
..... Alhamdulillah Bansan me Zance ba, Bayan haka ta ko'ina alkhairi nake samu yarinya Kan tayi Goshi domin Al'ameen da Yan uwan Innata dana mahaifina sunyi abinda ya dace dai-dai karfin su Yarinya taci Suna MEEAD (Alkawari)  Gata mul-mul da i'ta gwanin sha'awa kowa sai yaba k'yanta yake (Ai kusan Aareef d'ina ko , to Haka meead take harda kumatun😂 d'an Beautyn Yarona)Mun samu jego me kyau daga Inna domin tana kula damu yanda ya dace Randa muka cika wata biyu Ina Zaune a falo Yarinyar tana cinyar Inna yayi sallama amsawa mukayi  “Barkan ku dai”
“Barka Aminu ya aiki da Kuma rana” Zama yayi a Kujeran dake fuskantata “Alhamdulillah Rana Kan gashi munasha da iska" karb'an yarinyar yayi yana kallona “Hi baby ya kike” Sarai Nasan dani yake B'ata fuska nayi kafin Nace “Barka Brother!" Daga Haka naja bakina nayi Shuru Kallon meead yake tare da fad'in “Gaskiya inda Hali a daina barin kowa na jagwal-jagwala min 'Ya naji labari da kukaje allura ta Sha jagwalgwalo Hannun mutane a dinga tofe ta da addu'a Sabida bakin mutane O'eezukuma bikalimatil lahittammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah” mikewa Inna tayi tare da barin Falon tana dariya “Aikuwa Gaka ga i'ta dan kowa jagwal-gwala min kawa yake watakil in kayi magana taji ta kiyaye” cike da shagwa'ba nace “Kai Inna..” Shagala yayi da kallonta ganin yanda tayi mishi bala'in kyau ga wani cika data sake kasancewa Bata saka mayafi ba, tana sanye da doguwan riga na leshi ina juyowa muka had'a i'do harara na maka mishi tare da kwance d'ankwalin K'aina inna lullub'e jikina d’auke i'donshi yayi daga gareta zuciyarshi na bugawa ya mayar da hankalinshi Kan Meead Yana Mata wasa i'ta kuwa sai dariya take zuba mishi “Allah ya huci Zuciyar Gimbiya a sassautamin a gaji Wannan gauron ya Shiga samun Hmm ki bani dama Ameerah i promise you zan baki farin ciki da soyayya yanda ya dace dan Allah Tun ganin farko da namiki naji na samu Matar Auren...”
“Sai akace maka ni kamin a matsayin mijin Aure? Lallai Gwara ka Bari maganar Nan ya tsaya Anan karka kaishi gaba, kar Kuma kaga Ina sake maka fuska shine Zaka kawo wani Zance bani da Wannan burin Na Auren dangi, Allah de ya baka wata Amma nikan Hahh!” mikewa nayi da sauri domin wani K'unci ne naji ya ziyarce ni Amma sai ya Sha gabana tare da marerece fuska kaman zai saka kuka sai lallashi na yake Amma ina naki sauraronshi Mika min Meead yayi na karb'e ta da sauri na shige d'aki a sanyaye yabar gidan Washe gari sai gashi yazo Yana sanar da Inna ya samu min Gurbin karatu a Jami'ar bayero Gaskiya naji dadi sosai sai dai ban wani nuna mishi ba, Amma na Masa godiya domin Yana hidimta Mana musammam ma Meead Yana kashe Mata kudi sosai Babu B'ata lokaci na Fara Zuwa sai dai kullun fuskata a rufe yake saboda Nikkap d'in da nake sakawa gudun karna had'u da idon sani bana tafiya da yarinya kullun shi yake jele Gurin kai ni ya Kuma dawo in Mun tashi ya d’auko ni A Hankali na fahimci shi mutum ne me saukin kai dason jama'a gashi ba ruwanshi Akwai bar kwanci sai dai ni  Sam baya zuciyata Ga nacin tsiya na mishi Wulak'ancin Amma bawan Allahn nan Yana nanuke dani Karshe sai da Inna ta zaunar dani tamin nasiha me shiga jiki kafin na Fara kullashi ai ya cancanci na bashi lokaci na kodan Saboda hidimar da yake yiwa 'Yata Sannu a Hankali muka fahimci junanmu Har i'yaye suka Shiga zancen iyayena sunji dad'i ganin na yarda zan aure shi , a nashi Bangaren ma kuwa haka ne Meead na cika Shekara da Wata hud'u na yayeta domin babu inda Bata Zuwa a cikin gida, Sannu sannu Bata Hana Zuwa sai dai a Dad'e ba'a je ba, Gyara de  Wanda ya amsa sunanshi gyara na samu domin tun Bayan yaye ake Kimtsa ni Nonuwana ma kuwa sune kan gaba,  Fitowata Kenan daga wanka Naga Meead Zaune tayi min d'add'aya da kayan turare “Kai kai to kuwa Sena Zane ki Uwar b'arna yanzun jakan turaren dana d'aga sai da kika sauko shi Zo Nan...”
Yarinya Yar Shekara Biyu da wata biyar sai b'arna Bata Gani ta kyale so Uku Al'ameen na kawo min waya tana lalatawa cinno baki tayi gaba tare da mikewa da gudu Zata fita “Ni fa Umma coki zanyi Yau Kawu Ameen yace zamuje anguwa...” dariya na saka domin yanda tayi maganar seya baka dariya “Allah ya shirya min ke tunda kinyi b'arna Babu inda zamuje dake sai dai kiji zaman ki da Inna” har ta fita sai Kuma ta dawo da gudu tana kwashe kayan “Corry Umma bazan sake ma Allah kuwa!"
“Oho Nide bazaki bini ba” aikuwa tasa i'hun daya fito da Inna daga madafi “Zo Nan Kawa meya faru? Ameerah dukan ta kikayi ko me?”
“wane ni zubar min da turare tayi shine nace Babu inda zanje da i'ta shine fa take wannan ihun kaman Wanda aka dake ta, tayi zamanta a gida kawai..” aikuwa ta sake saka i'hu mayafi na d'auka tare da fitowa falo na iske Al'ameen a tsaye i'ta Kuma sun fito da Inna hannunta rik'e da Himar d'inta “Zo Nan Yarinyata waya tab'a min Kyakkyawana?”
“ba Umma bace wai baran je anguwa ba saboda na zubar Mata da turare.." goyata yayi a bayanshi “kyale mamanki zan siya Mata wasu muje” Kallon Inna nayi nace “Sai mun dawo"
“Allah ya yatsare a dawo lafiya" da Ameen muka amsa kafin muka nufi Shopping tun a mota ta ishemu da surutu Koda muka Shiga shagon siyayyan ta tab'a wannan ta tab'a wancan Juya baya nayi ban ganta ba, na Kalli Shashin Al'ameen Naga Yana waya ajiye basket d'in nayi na Shiga nimanta can na hangota da wata mata tana ta zuba Mata surutu “Baiwar Allah yi hakuri fa kin had'u da aku...” mak'ale Sauran maganar Yayi sakamakon arba da nayi da Maamah Dr Rabi'atu baki na rawa ta nunani tare da fad'in “Ameerah!” Hannun Meead naja da sauri ban nuna Mata nasanta ba na juya kayana “Ameerah”
“A'ah baiwar Allah lafiya kike bina?” cike da alamun mamaki nake kallonta “Dan Allah sake Ni nifa ban sanki ba" Rike mayafina tayi da karfi tana Magana Nan Hankalin mutane ya Fara Dawowa kanmu hannunta na rawa ta kara waya a kunninta shammatar ta nayi na kwace jikina da sauri na bar Gurin “brother mu tafi gida” Jan hannunshi nayi da sauri muka fita “Ameerah lafiya to kayan kuma fa?” da sauri na bud'e motar na Shiga inna matse Meead a jikina Shiga motar yayi cikin tashin Hankali na Fara mishi Magana sakamon hango Abba da nayi tare da Dr Suna dube dube, “Muje muje..." Taka motar yayi da sauri yabar Gurin ajiyan  zuciya na sauke inna Kallon Meead Wanda kamanninta ya b'aci da Abba,
“A'a Wai Meye haka kin d'aga Hankalin ki meke faruwa?”
“Wallahi Yallaɓai Ameerah na gani kalli muje karta gudu...” Jan hannunshi tayi suka fita waje sai dai Babu i'ta ba alamarta..
“Wallahi Ameerah na gani yanzun Nan tana Raye Ameerah Bata mutu ba...”

Maman Faruq

MIJIN BAABATAWhere stories live. Discover now