21

588 6 0
                                    

2️⃣1️⃣
Kallonta yayi cike da mamaki tare da zare gilashin i'donsa “Ameerah kuma?” Gyad'a mishi kai tayi Hawaye na zubo mata “Wallahi i'ta nagani Amma Taki ta nuna ta sanni Karshe ma guduwa tayi” Hannunta ya kama Amma sai ta kwace tare da tsayawa tana waige-waige “Kefa kikace bata tsaya ba daman fatalwa yana tsayawa ne? Kode kinga wata daban de...” girgiza mishi kai tayi “Haba nida 'Yata Taya bazan gane ta ba? Wallahi i'ta na gani" d'aga kafad'arshi yayi alamar bai damu ba “Kinga zo mutafi tunda bazakiyi siyayyar ba”
“Wallahi babu inda zanje na tabbata Ameerah tana cikin Market d'in nan” tamke fuska yay  alamar ba wasa yace “Kinga banson iskanci wuce mu tafi" ya fad'a tare da Nuna Mata Motarsu jikin sanyaye ta Nufi motar juyar da kanta tayi gefe tana Kallon hanya tare da jan kwafa “Lallai abin mamaki har ni Ameerah zata dinga gudu? Toh me nayi Mata..” Juyowa yayi ya kalleta “Rabi  ,ki sakawa zuciyarki salama ba i'ta Kika Gani ba..” idanunta na Kallon gilashin motar tace “Humm Yallaɓai Kenan ka kaini Gurin Daadah tunda ka mayar dani mahaukaciya..”
“Eh toh yanayin ne yafi Kama da haka” yace Yana murmushin gefen baki aikuwa maganar ya bata haushi “dan na temaka na fito da kai Dole ka fad'a min b'akar magana” Girgiza kai yayi tare da manna Mata hauka Gida suka koma Yana faka motar ya juyo gareta “A matsayin ki na likita ya kamata ki binci lafiyar kwakwaluwarki” hararanshi tayi tare da fita a Motar a falo ta samu Serah “Maman Ameerah har Kun dawo?" A dak’ile ta amsa mata shima Dan ta ambaci sunan Ameerah ne , d'akinta ta shiga tare da kullewa ta kira Daadah tana sanar mata taga Ameerah tare da kallon mahaukaciya da Yallaɓai yake mata Hakuri Daadah ta bata Suna gama wayar Daadah ta kirashi kunna motar yayi tare da barin gidan
“Amma Manu baka kyauta ba, Rabi fa Abar a tausaya mata ne, ya Zata maka Magana ka manna mata Hauka in bazaka lallasheta ba bai kamata ka fad'a mata bakar Magana ba Kai K'anka kafi kowa sanin yanda Mutuwar  Nan ya tab'a ta har yanzun bata  warware ba” sunkuyar da kanshi yayi k'asa Sannan yace “insha Allahu za'a kiyaye” Nasiha ta mishi sosai Sannan ya sallameta daga Haka ya bar gidan...
   **
Bud'e motar tayi tana Shirin fita Bayan sun karaso kofar Gidan “Gimbiya lafiya kuwa kefa kikace za ayi siyayya amma.." dakatar dashi nayi bayan na d’auki Meead da take Shirin min rikici “Kaga brother gani nayi siyayyan bashi da Amfani shiyasa Bari na Shiga ciki zamuyi magana anjima”  fitowa nayi a motar shima ya fito “Amma wannan ba hujja bane domin Mun fita dake cikin Farin ciki Amma kalli yanda Kika firgice lokaci d'aya in Akwai wani abu ki sanar min mana” Kallon ’Yata nayi sannan na kalleshi “Yaya Al'ameen babu komai fa!”zai sake magana nace “Dan Allah ban i'ya tsayuwa ba, sai anjima" duk yanda yaso muyi Magana k’in sauraranshi nayi domin bana cikin nutsuwa 'yar maganar da mukayi ma daurewa kawai nayi Ina shiga cikin Gida na samu  Inna tana sauraron Radio “Har kun dawo ya naga kunyi sauri Ina siyayyar” kokarin sai saita yanayina nayi Cikin karfin Hali nace mata “Ai fasa fitan mukayi..” bud'e baki Meead tayi zatayi Magana na watsa mata harara take tayi shuru tana Turo baki “umma kefa kikace Kariya ba Kyau..” zare mata i'do nayi tare da cewa “Ungo Nan gidanku , ba na hanaki wannan karanbanin ba? Wayace kiyi Magana Anan!” dakatar dani Inna tayi “A'ah Meye zaki wani hayayyakoma yarinya? Barta tayi maganarta” mikewa nayi Ina jin wani i'rin b'acin rai da fargaba ya cika min zuciya “Toh Allah ya kyauta Zo Nan kawata" makalewa yarinyar tayi a jikin Inna tana lek'en Ameerah “Toh umma kiyi hakuri..” mikewa nayi na Shiga Amma sai na kasa zama “Me Kenan na aikatawa Maamah? Ai bata cancanci Haka daga gareni ba Tunda har yanzun cikin duhu take bata san gaskiya ba, Ga tashin Hankali dana ganshi cikin idanunta in banyi kariya ba, harda hawayenta lokacin da na nuna Sam, bansanta ba Amma ai bani da wata hanya face wannan shine kad'ai kwanciyar Hankali na dana iyayena bazai Yuwu na koma rayuwar Baya ba Allah kad'ai yasan Halin da take ciki a yanzun wayyo Allah Ni Ameerah Meyasa nayi mata Haka?..” dafata da Innarta tayi ne yasata juyowa da sauri tana sauke ajiyan zuciya “Tun shigowarki na biyo bayanki Lafiya kuwa domin tun bayan dawowarki Garemu ban tab'a ganinki cikin tashin Hankali i'rin wannan ba ko wani abu ya faru tsananiki da Yayan naki ne?” Bansan ta i'na Zan Fara sanar mata wannan lamarin ba, domin Hankalin ta sai yafi nawa tashi “Inna babu komai wata karamar matsalace Amma alhamdulillah!” bata takurata ba ta kyaleta
Washe gari A hanyar mu na Zuwa Makaranta Al'ameen ya kalleni tare da fad'in “Gimbiya har yanzun baki fad'a min abubuwan da kike bukata ba, gashi ban ganki da kawa ko d'aya ba, bikinmu Kuma Saura kwanakin da Basu wuce takwas ba" batare da na kalleshi ba nace “brother kenan , in an shafa fatiha ba shi Kenan ba?” Al'ameen yace “Ba wani Shagalin da za'ayi Kenan?” girgiza Masa kai nayi Bayan ya faka motar a farfajiyan makarantar Sallama mukayi  har ya juya sai Kuma ya dawo “Ki kula min da kanki” dariya abin ya bani domin zancen yazo min bambarakwai “Ok bye saika dawo" Tafiya nayi na barshi tsaye Yana bina da kallo sai da yaga baya hangota Sannan ya koma motar shi, Lokaci na cika ya dawo fitowa nayi rataye da jakata inna Kare Rana da Hannuwana sai ji kawai nayi An rumgumeni “Oyoyo Umma” d'agata nayi ina dariya “wato sai da kika biyo Uncle d’inki ko?” na fad'a ina jan kunninta “Toh ai Innace zata fita shine Nima na biyo shi mu dawo dake ba" ta Karasa maganar tana turowa baki gaba ina rike da hannunta har muka Karasa jikin motar a can Gefe na hangoshi yana waya Amma hankalinshi na kanmu domin juyowa yayi Yana Mun murmushi nima murmushi na mayar masa jinginuwa mukayi da jikin motar duba jakata nayi da niyar d'auko wayata sai ban gani ba Da hannu na mishi alama inna zuwa “Meead jirani bari in d'auko wayata” Ashe ta biyo bayana Ban lura ba kasancewar  Ina tafiyarne cikin Sauri na dawo jikin motar sai ban ganta ba “Ina MEEAD?” ya tambayeni Yana karasowa “Na barta Anan ai" Al'ameen yace “Tare kuka tafi ai domin Naga tana bin bayanki” juyawa nayi da sauri na koma Ina Waige waige shima biyo bayana yayi “Cikin fad'a nace shiyasa bana so kana Zuwa da i'ta dan Bata i'ya zama Guri d'aya ba, yanzun haka taje ta samu mutane tana zuba musu surutu Yarinyar Nan kiriniyarta yayi yawa” aikuwa can na jiyo K'yalk'yalewan dariyarta Juyawa nayi Ina Kallon Gurin..
Abba Yana cikin tafiya yaji an rik'e mai riga juyawar da zaiyi sai yaga Yarinyace tana kokarin kama igiyar da aka d'aure Mata kayan wasan ta “Ayya balon balon Na Wayyo ya fi re sama” sai Kama rigarshi take tana tsalle Kallon yarinyar Yay sai yaga kamar ya santa bud'e wayarshi yayi kasancewar hoton da Dr Halirah ta turo Masa shine a wallpaper nashi sai yaga kamannin sak shine kamota yayi Yana shafa kanta “Fine baby ya sunanki?” cikin ihu tace “Ni wallahi sai ka biyani abuna ya fire sama wayyo!” kamo igiyar yayi aikuwa tasa dariya “yauwa sankiyu” (Thank you..)
dariya yayi tare da jan kumatunta “ya sunanki 'Yan mata?” zare i'do tayi waje sannan tace “kai Niba Am mata bane” rike mata hannu yayi tare da tsungunawa a gabanta ji yake kamar ya rumgumi yarinyar Sabida tsananin soyayyarta da yaji yazo mishi lokaci d'aya “fad'a min sunanki Mana Yarinya..” k'anne i'do d'aya MEEAD tayi sannan tace “haka fa Giranfafa (Grandpapa) yake Kiran UMMANA ai wayo kayi mata to saina fad'awa umma ka kira sunanta” Rumgume yarinyar yayi a jikinshi tare da sauke ajiyan zuciya Yana jin wani nutsuwa da Farin ciki na lullub’eshi d’agota yayi Yana Kallon fuskarta da zagayayyen bakinta like Ameerah! Abinda zuciyarshi ya bashi kenan “Toh naji fad'a min mana kinji 'Yar Kyakkyawa” Dariya tayi wanda har Saida dimple d'inta ya lotsa “Sunana Meead kaifa ya sunanka?”
“Abba Zaki dinga kirana Haka princess take kirana” yamutsa fuska tayi tare da turo baki gaba “Toh aini ba princess bace Amma de Zance haka ABBA ko?” lumshe i'do yayi a Hankali sai ji yayi an zareta a jikinshi da sauri ya bud'e i'donsa baiga fuskar ba, Amma tabbas yanayin tafiyar da Nutsuwa kalan nata ne da sassarfa nake tafiya Ina jin zuciyata kaman zata Fad'o k'asa Dan tsananin bugawan da takeyi “Ameerah!!!” cikin murya me amo ya ambaci sunanta Amma i'na bata tsaya ba, taci gaba da tafiya cikin sauri Mikewa yayi Yana bin bayanta Amma ina Koda ya iso bai ganta ba, Babu i'ta Babu alamarta sai tashin mota dayaji Koda ya juya ya hango mayafinta ta waje kokari yayi ya d'auki Number motar tare da Shiga nashi motar Koda yabi Bayansu baiga motar ba, gangarawa yayi da motarshi gefen hanya tare da kifa kanshi saman sitiyarin motar “Hasbunallahu wani'imal wakeel” kalman daya ambata Kenan Yana Buga jikin motar “Da gaske Kenan Ameerah tana raye? To wannan yarinyar na waye tayi Aure Kenan ko Yaya? taya Haka ya kasance toh bani da Wannan amsar dole na nimo Halirah” da sauri ya kunna motar a 360 ya tashi motar direct gida ya dawo Amma Bai ishe Rabi ba, Kiran wayarta yayi bata d'auka ba, fitowa yayi da sauri Serah na mishi Magana Bai saurareta ba, Asibiti ya nufa tare da kwankwasa kofar Ofishin Dr “Shigo” aka amsa mishi daga ciki tana cikin duba files d'in Mara lafiyar da zata duba ya shigo “Yallaɓai yi hakuri Naga kiranka bana kusa..”
dakatar da i'ta yayi ta hanyar fad'in “Halirah tazo kuwa Dan Naga Office d'inta a rufe..” ajiye takardan tayi tare da fad'in “A'a sai dare zata zo”
“Ok Bari naje karna shiga Hakkin mutane duk da na taka doka na shigo Kai tsaye” d'agowa tayi tana murmushi tace “Babu komai"
“ok bye ayi aiki lafiya” hannu ta had'a alamun tagode fita yayi direct ya Nufi Gidan Halirah Koda ta ganshi sai da Taji fad'uwan gaba “Barka da zuwa gashi Sir Aminu baya nan..."
“Ba Gurin Aminu nazo ba aii tunda nasan baya gari” mikewa tayi tare da Shiga kichin ta kawo mishi kayan motsa baki tare da drinks Murmushi yayi tare da Fad'in “Humm! Duk bana bukatarsu amsar tambayata nake bukata Shin Ameerah tana raye?” Karasa maganar tare da tsareta da idanuwanshi “Ameerah kuma?” tace cikin mamakin tambayar tashi Mikewa yayi hannuwanshi na cikin Aljihun rigarshi
“wasan kwaikwayon ya i'sa Haka! Lokacin da Rabi'atu tace min taga Ameerah Mahaukaciya na maisheta Amma Nima yau gashi kina Shirin mayar dani mahaukaci Amsa zaki bani Eh ko A'a fak'at , banzo don muyi dogon magana dake ba”
Mikewa i'tama tayi Sannan tace “Bansan zancen da kake ba, domin a Gaban idonka kaga gawarta..!”
“Halirah Kenan” daga Haka ya fita a gidan sai dai yanayi na rashin gaskiya da yake Gani a kwayar i'donta yasa ya kasa barin anguwar domin yasan Tabbas zata fito Kuma hakance ta kasance Bayan minti goma da Fitarshi ya hangota ta fito tana Waige waige murmushi gefen baki yayi tare da bin bayanta d'an sahu ta tsayar ta Nufi anguwarsu Ameerah har kofan gidan shima ya bita Nan yaci Karo da motar daya gani juyawa yay ya bar anguwar yanaji lokaci yayi da kowa zai San Wacece Ameerah a gareshi domin bazai tab'a yarda wani abu ya sake nisantashi da i'ta ba, shi kad'ai yasan kalan azabtuwan da ruhin shi yayi da rashita Amma Kuma Rabi'atu fa? Bai Mata adalci ba domin kuwa yasan za'a Sha fama kafin ta amince sai dai tawani ‘Bangaren yasan zai samu kwarin Gwiwar Yar uwanshi da Mahaifinsa Amma ta fannin Daadah da Rabi'atu kan da Sauki yasan shi Mai Babban laifi ne a garesu Amma sai dai ba yin kanshi bane Zuciyarshi ce duk da Yayi kokarin dakatar da hakan Amma abin ya gagara Bayajin zai sake Bari Ameerah tayi Nesa dashi a wannan lokacin Sai damuwarshi d'aya 'Yar da ya gani toh 'Yar waye Aure tayi Kenan...? Yayiwa ƙanshi tambayar da bashi da Amsarta...

Maman Faruq

MIJIN BAABATAWhere stories live. Discover now