Chapter 1

56 4 0
                                    

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

Bismillahir rahamanir rahim wa sallallahu allan nabiyyil karim wa ahlihi wa sahbihi wa sallam.

  Dukkan godiya ta tabbata gun Allah sarki guda daya mai kowa mai komai a ko'ina, da ya bani ikon rubuta wannan littafin mai suna 'ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE'

Ban rubuta wannan labari don cin zarafi ko batanci ga kowa ba, idan kaga wani abun yayi kama da naka ko yayi dai dai da kai to kawai an samu dacen hakan ne.

Ban yarda wani ya daukar min littafi ko ya juya shi ta kowacce irin hanya ba tare da izinina ba.

Kuyi kokari ku dauki abu mai amfani dake cikin wannan littafin, abinda bai da amfani kuma kuyi watsi dashi.

   

                    *page 1 & 2*

    Suna zaune a dining suna karin kumallo, Alhaji Inuwa yana sanye da manyan kaya da alama yayi shirin fita ne, a gefensa ta dama Hajiya Sailuba ce a zaune, a facing dinsa kuma Aisha ce sanye da doctor coat a jikinta, suna cikin yin breakfast din sai Aisha ta duba agogon dake hannunta taga karfe takwas da minti ashirin da biyu, sai ta mike zumbur.

      Alhaji Inuwa ya kalleta cike da mamaki yace "Lafiya! naga kin mike haka, sai kace wadda kunama ta harba?"

       Aisha cikin shagwaba tace "Daddy wallahi na makara, tafiya zanyi kawai"

       Hajiya Sailuba tana kallonta tace "Ki zauna ki karasa cin abincin mana in kika gama sai ki tafi, amma sai ki tafi da yunwa"

       Aisha ta girgiza kai tace "Naci a can kawai idan naje aunty, sai na dawo"

      Alhaji Inuwa ya jinjina mata kai yace "To a dawo lafiya doctor, Allah ya kiyaye hanya"

      Aisha tana murmushi cikin yanayin jin kunya tace "Daddy tsokana ta ma kake yi? to amin"

      Hajiya Sailuba tayi murmushi tace "Sai kin dawo Ummi Allah ya tsare mana ke daga dukkan wani abin ki"

       Aisha tayi murmushi itama tace "Amin aunty na" taje kan kujera ta dauki stethoscope da jakarta ta fita tana dariya da farin ciki fal a fuskarta.

       Ta fito wajen motarta tarar babu driver a wajenta sai dauki wayarta ta kira, sai gashi da gudu yazo.

       Aisha ta kalleshi tace "Kana gani na makara amma ka tafi kana hidimar gabanka, bayan kasan yau akwai aiki kuma zan fito mu tafi"

       Driver yace "Don Allah kiyi hakuri shiga mu tafi"

       Sai ya bude mata baya ta shiga ta zauna shi kuma ya shiga gaba yaja su tafi. Ya kai ta har cikin asibitin yaje motor park yayi Parking.

      Aisha ta fita da sauri tana tafiya tana masa magana, tace "Kuma saura ka ki zuwa daukata da wuri"

       Driver ya daga murya don ta jiyo shi yace "Insha Allahu da wuri zan zo kafin ma ki tashi" sai yaja motar ya tafi.

       Aisha ta shiga ciki da sauri sai su hadu da kawarta Sabila itama likita ce, ta fito daga wani patients room.

     Sabila tace "Dr. Aisha sannu da shigowa"

     Aisha tace "Yauwa Dr. Sabila, Doctor ya shigo?"

     Sabila ta girgiza kai tace "A'a"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now