Chapter 2

20 1 0
                                    

          ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA *
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223
 

                     *page 3 & 4*

 
    Rahina tana zaune a tsakar gida tayi jigum tana tunani, sai malam Buba ya shigo.

      "Salamu Alaikum"

       Rahina ta mike tsaye tace "Amin wa alaikas salam, dama tun dazu nake jiran shigowarka!"

        Malam Buba  cikin mamaki yace "Lafiya dai ko?"

        Rahina tace "Eh lafiya dai amma ba kalau ba"

        Malam ya zauna itama Rahina ta zauna.

        Malam Buba yana kallon ta cikin yanayin kaguwa yace "Me yake faruwa ne?"

        Rahina ta fuskanceshi tace "Malam dazu da muka je barkar nan a hanyarmu ta dawowa wallahi naga wata yarinya budurwa kamar Aisha 'yar Rahima data bata!"

         Malam Buba cikin mamaki tace "Ya aka yi kika san itace har kika ganeta? yarinyar data bata shekaru goma sha biyar da suka shude!"

         Rahina ta daga murya da karfi tace "Malam wallahi zan iya rantse ma da Allah itace! naga kama da tsagun nan na fuskarmu ni da Rahima da yaya Rahila"

        Malam cikin Al'ajabi yace "To in har haka ne tana iya yuwuwa itace bari na fito daga bandaki na kira Alhaji Ahmed mu tattauna akan maganar koma kawai su zo nan sai muje ayi bincike" sai ya dauki buta ya nufi bandaki.

        Rahina itama ta mike tace "Nima bari na garzaya gidan yaya Rahila na sanar mata" sai ta zari mayafi ta fita.

       
       ***           ***           ***           ***

     Rahila tana zaune a tsakar gida tana tankaden garin tuwo, sai Rahina ta shiga cikin gidan.

      Rahina ta shiga da sallamarta "Salamu Alaikum"

       Rahila ta daga kai ta kalleta tana amsa mata sallamar "Wa Alaikumus salam"

       Rahina ta jawo wani karamin turmi ta zauna jiki a sanyaye tana kallon Rahila, tace "Yaya ina yini"

       Rahila tana mata kallon rashin fahimta, tace "Lafiya kalau! lafiya kuwa na ganki da almurun nan? ko daga unguwa kike?"

       Rahina tace "Eh, daga unguwa nake amma naje ma gida, wani abu ne yake ta min yawo a rai shi yasa nace sai nazo na sanar miki a yau!"

       Rahila cikin mamaki tace "Me yake faruwa ne?"

       Rahina tace "Akwai wata makociyarmu Saliha nasan kin santa gidanta yana kallon gidan Jazila"

       Rahila tace "Eh na ganeta babar dan Amir uban surutu"

       Rahina tace "Ita kuwa, to ita ce babbar 'yarta wadda aka yiwa aure bara ta haihu, sai mukaje barka ni da Jazila dazu dazun nan, bayan mun fito daga gidan mun zo titi, sai Jazila tace na rakata wani supermarket a kusa da  kwanar shiga layin, tace zata siyo madarar nan 'yar nijar wadda ake iloka tace ta layin namu bata da afki, munje zamu shiga supermarket din kenan sai muka hadu da wata yarinya budurwa kamar Aishar Rahima data bata, mukai mukai da yarinyar nan ta tsaya ta sauraremu amma ta ki don haka sai muka bita muka ga inda ta shiga wani gida a tudun yola"

        Rahila tace "Tirkashi! to yanzu ya, za'ayi kenan? kin sanar da Rahima?"

        Rahina tace "Malam dai yace zai yiwa Alhaji Ahmed waya"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now