Chapter 5

8 1 0
                                    

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                      *page 9 & 10*

       Da misalin karfe tara aka daura auren Hauwa da Aliko, bayan an daura auren 'yan daurin aure wasu sun tafi duk kusan an watse sai abokan arziki da 'yan'uwa na jiki, sai mai unguwa ya kira Malam Buba can gefe.

        Mai unguwa yace "Alaramma yarinyar nan data bata diyarku ko?"

       Malam Buba ya zabura yace "Yallabai an ganta ne? tana ina ko tana gidanka?"

       Mai unguwa yace "Ba'a kawota ba, sai dai nan ko Allah zai sa a kawota"

       Malam Buba yace "To Allah ya bayyanata"

        Mai unguwa yace "Amin amin, dama abinda zan gaya maka kenan sai ka sanarwa da matan"

       Nan suka yi sallama mai unguwa ya tafi ga harkokinsa, su kuma suka cigaba da nemanta ba tare da gajiyawa ba, ba dare ba rana.

        ***          ***           ***           ***

   Da suka tashi da safe Hajiya Sailuba ta yiwa Aisha wanka tayi mata kwalliya tasa mata wasu sabbin kaya, sannan suka nufi dining suka yi breakfast bayan sun gama sai suka zauna suna kallon film din india a gidan talabijin din ctv da yake lahadi ce, a karshen program din sai suka ji sanarwa "Ana cigiyar iyayen wata yarinya mai Aisha, Aisha fara ce shekarunta baza su fi bakwai ba, tana da tsagu a kumatunta kuma tana sanye da riga da siket 'yan kanti. Idan iyayen wannan yarinya sunji wannan sanarwa sai su nemi 'yarsu a gidan Alhaji Inuwa Muhammad Bello dan takarar shugaban karamar hukumar Dala dake unguwar goron dutse, ko kuma gidan mai unguwar madabo, ko kuma a zo gidan talabijin na ctv kano don karin bayani"

        Alhaji Inuwa ya kalleta yayi murmushi yace "Kin gani ko Ummina duk nasa ayi cigiyar iyayenki, don haka ki kwantar da hankalinki za'a gansu"

        Aisha ta gyada kai tace "To"

 
             BAYAN MAKO GUDA

        Alhaji Ahmed da Rahima sunyi shirin komawa Kaduna suna tsaye a kofar gida suna bankwana da juna.

         Alhaji Ahmed ya Malam Buba, yace "Malam Buba don Allah a cigaba da cigiya anan, mu ma a can zamu ci gaba da cigiya Allah ya bayyanata"

          Malam Buba yace "In Allah ya yarda zamu cigaba da cigiya har lokacin da za'a ganta, ku kara hakuri!"

          Rahina ta kalli fuskar Rahima wacce take ta faman hawaye, yace "Rahima ki kara hakuri don Allah ki dawo da rayuwarki kamar da, kalli yadda kika koma, kinki ci kinki sha gashi bakya barci kullum sai kuka karfa wata cutar ta sameki!"

       Rahima cikin yanayin kuka tace "A duk lokacin da nazo zan gudanar da daya daga cikin abinda kika lissafa, sai na tuno da Aisha sai na kasa yi kawai sai naji kuka yaci karfina!"

        Rahila cikin tausayawa yace "Addu'a zaki dinga yi Rahima ki daina kuka bashi da wani amfani"

        Rahima wani zazzafan hawaye mai dumi su zubo mata tace "Wallahi bana ma sanin lokacin da hawaye yake fitowa, sai dai kawai naji shi a kumatuna nayi nayi na daina amma abin ya faskara"

       "Addu'ar dai ita kadai ce garkuwa daga duk yanayin da kike ciki, ki dinga yawaita ta" Rahina ce ta fada gami da dafa kafadar 'yar'uwartata"

        "Na gode yaya, na gode anti Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara zumunci" Rahima ta fada tana goge hawaye cikin sanyin jiki.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now