Chapter 10

22 3 1
                                    

         ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                    *page 19 & 20*

      Alhaji Inuwa ya danyi turus yana shafa kai sai kuma ya fara rarrashinta yace "Ina so in nuna miki rabuwa da Aisha daidai yake da rasa rayuwata, ba zan iya rabuwa da ita ba!"

       Hajiya Sailuba ta nunashi da yatsa tace "To ka sani Alhaji idan har ka auri Aisha sai dai ka zaba ni ko ita domin ba zan taba zaman kishi da 'yar dana raina da hannuna ba, nayi dawainiya da ita nice kashinta nice fitsarinta amma yanzu kace itace zata zama kishiyata, to wallahi a'a! dama tunda ta dawo naga salonka ya canja akan ta nasha jinin jikina, don na sanku mazan yanzu baku da tabbas"

      Alhaji Inuwa cikin sanyin jiki ya kalleta yace "Haba Hajiya bai kamata ki rika fadin irin wannan furuci ba ai abinda ya wuce ya riga ya wuce, wai ina sauran soyayyar taki take? idan zaki iya tunawa a zauren gidanku kin taba ce min duk abinda zan miki ba zaki taba yin yaji bare har akai ga saki....... "

       Hajiya Sailuba ta tari zancen da cewa "Au to! dama saboda haka ne kake yi min irin wannan cin fuskar? kuma idan ana maganar karya alkawari ai kai ka fara kuma ka yarda girmanka na take shi!"

      Da yaga tana neman daga masa hankali sai ya fita ya bar mata dakin, koda ya fito sai yayi tunanin zuwa dakin Aisha don ita yaji yadda zata dauki al'amarin, ya shiga ya sameta ta saka kayan barci tana shirin kwanciya.

      Aisha ta kalleshi cikin mamaki tace "Daddy lafiya kuwa?"

      "Samu guri ki zauna wata magana nake son yi dake"

       Aisha ta zauna a gefen gado shiru tana sauraronsa, ai lokacin da taji bukatarsa ko gama fada baiyi ba tayi zumbur ta tashi tana fadin "Wallahi haka ba zata taba faruwa ba, har duniya ta tashi to wai da wane ido zan kalli Aunty a matsayin kishiyata kai kuma a matsayin mijina, kai! wallahi wannan daidai yake da a ce yau jaki yayi kaho, da haka ta faru gara na rasa raina!"

      Ya rausayar da kai yana magana cikin sanyin murya yace "Haba Ummina ya kike fadin ne? ke kamar bakya kaunata kiji tausayina mana"

       Hawaye su zubo daga idonta tace "Bazan taba iya kasancewa da kai a matsayin mata da miji ba! zuciyata ta riga ta aminta da kai a matsayin uba! bazan taba aurenka ba wallahi! bazan taba yin abinda zuciyarka take raya maka ba daddy!" ta fashe da kuka mai ban tausayi.

     Aisha a wannan rana kwana tayi bata yi barci tana ta kuka, tana ta tunanin ko me ya shiga jikin daddyn nata oho? idonta duk ya kumbura fuskarta ma duk ta tashi kana ganin ta kasan tasha kuka, don haka gari na wayewa ta hada kayanta a trolley bag ta dauki jakar da mayafinta ta fita daga gidan su ko tashi basuyi ba. Koda ta fito bata zame ko'ina ba sai tasha ta hau motar Kaduna, da yake safiya ce nan da nan motar ta cika suka tashi suka kama hanya suka nufi Kaduna. Bayan sun isa can Kaduna bata zame ko'ina sai gidansu na can wato Alhaji Ahmed, tana shiga gidan ta tarar da mahaifiyarta Rahima a zaune a falo kawai sai Aisha ta fada jikin Rahima ta rusa kuka.

      "Ke lafiyarki? me ya faru dake? ina mutanen gidan naku?"

    Aisha tana kuka ta sanar da Rahima yadda suka yi da Alhaji Inuwa da bukatarsa.

      Rahima cikin fada tace "To yanzu da kika dauko kafa kika taho kina tunanin nan ma kin sha ne?"

      Aisha tana kuka tana magana cikin shesshekar kuka tace "Wai Umma ya ake so nayi da rayuwata ne? shin ina tunaninku da hangen nesanku na iyaye ya tafi ne?"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 22, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now