Chapter 3

13 1 0
                                    

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                       *page 5 & 6*

      Can jimawa kadan sai ya fito da wata karamar akwati a hannunsa yazo ya zauna a inda ya tashi.

       Alhaji Inuwa ya kalli Alhaji Ahmed, yace "Kuna da hotonta a lokacin da take karama, ko wanda aka yi mata a shekarar data batan?"

        Alhaji Ahmed ya gyada kai yace "Muna dashi, don kwana ashirin da yin hoton ma ta bata"

       Alhaji Inuwa yace "Ko kun taho dashi yanzu?"

       Rahima ta gyada kai jiki na rawa tace "Mun taho dashi!"

       Sai ta buda jakarta ta dauko hoton ta mikawa Alhaji Ahmed shi kuma ya karba ya mikawa Alhaji Inuwa ya karba ya gani sannan ya bude wannan karamar akwatin da ya dauko ya bude ya dauko wani hoton Aisha a ciki a lokacin da take karama ya hada da wanda suka bashi, ya kalli wannan ya ya kalli wannan, can kuma ya jinjina kai yayi shiru kamar yana tunani.

       Can sai Alhaji Inuwa ya sake tashi a karo na biyu ya kallesu yace "Ina zuwa" sai ya sake hawa sama.

       Rahima ta kalli Alhaji Ahmed, tace "Wai me mutumin nan ne? naga ya sake hawa sama!"

       Alhaji Ahmed ya girgiza kai yana kallonta yace "Wallahi nima ban san abinda yake nufi ba!"

      Malam Buba ya kallesu yace "Me kuke ci ne na baka na zaba! alamu sun komai ya kusa zuwa karshe, mu tsaya dai mu ga iya gudun ruwansu ko"

        Rahila ta jinjina kai tace "Eh gaskiya ne mu tsaya mu ga yadda zamu karke dasu"

        Rahina rausayar da kai tace "Hakan ne, amma dai zahirn gaskiya yarinyar nan itace wallahi......!" bata karasa maganar ba suka hango su suna saukowa.

        Su zo su tsaya Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba da Aisha.

         Alhaji Inuwa ya kallesu yace "Wacece Mahaiyarta?"

         Rahima ta mike tsaye zumbur tace "Gani nan nice!"

         Alhaji Inuwa ya kara tambaya yace "Waye kuma mahaifin nata?"

         Alhaji Ahmed ya mike shima yace "Gani nan!"

         Alhaji Inuwa ya kallesu a nutse ya kalli Aisha, ya kuma kallonsu ya kalli Aisha, ya kara kallonsu a karo na uku ya kalli Aisha, yace "Ummina"

         Aisha a tsorace ta kalleshi tace "Na'am daddy!"

        Alhaji Inuwa hawaye su zubo masa yace "Ummina ga iyayenki!" ya fada yana nuna mata Rahima da Alhaji Ahmed.

         Aisha ta dafe kirji tana magana da karfi tace "Daddy me kace!?"

         Hajiya Sailuba ta zazzare ido tana kallonsa tace "Alhaji meye haka? wacce irin magana ce wannan?"

         Alhaji Inuwa ya bata rai ya daga mata hannu alamun tayi masa shiru.
       
         Aisha cikin mamakin maganarsa tace "Dama ba kune iyayena ba? dama ba kune ku ka haifeni ba? wallahi ba zan yarda ba! ni ba wadannan iyayena ba! wallahi kune iyayena!" tana gama fada sai ta fashe da kuka ta koma bayan Hajiya Sailuba tana rusa ihu.

      Rahima ta zazzare ido ta dafe kai da hannu biyu tayi hailala da karfi sai ta fadi kasa, duk matan suyi kanta da sauri, Hajiya Sailuba ta debo ruwa a zuba mata amma taki tashi don haka sai Alhaji Inuwa yace musu su kaita asibiti, nan take ya dauko mota su dauketa su nufi asibiti.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now