Chapter 7

5 1 0
                                    

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin 📚✍️📚
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

 
                   *page 13 & 14*

       Salman ya kallesu shima cikin harshen turanci yace "Ku su waye? kuma me kuke cewa? ban fahimci abinda kuke cewa ba!"

        Mutumin yazo ya dafa kafadar Salman, yace "Kada ka damu zan maka bayanin komai, amma yanzu bari mu gama da wani dan karamin uzuri, babu wata matsala kada ka damu kanka, ku jiramu mu dawo"

        Salman da Suhail suna tsaye suna kallonsu su shiga wani lungu wasu daga cikin bodyguards suna biye dasu yayin da wasu suka tsaya tare dasu Salman, sun jima kafin su dawo ganin haka yasa su Salman suka yunkura da niyyar tafiya amma sai bodyguards suka hanasu tafiya, suna nan jigum sai gasu sun dawo.

       Mutumin ya kalli Salman yace "Ku biyo mu muje gida zan muku bayani" yana gama maganar ya shige motar shi da Lakshmi.

        Salman da Suhail kamar ba zasu shiga motar ba amma sai bodyguards din suka musu kwarjini haka dole suka shiga ba don son ransu ba. Tafiya suke ba mai cewa komai har suka fara barin cikin gari, a gefen gari suka nufi wani katafaren gida shi daya tak a wajen, kai tsaye cikin gidan suka shiga suka yi parking sannan suka shiga cikin gidan, tsananin kyawun gidan da tsaruwarsa tasa su Salman suka zama kamar kauyawa sai kalle kalle suke, a wani babban kayataccen falo suka zauna yayin da masu hidimar gidan suka shiga kawo musu kayan ciye ciye da kayan shaye shaye, amma su Salman sai suka ki cin ko shan komai don su gaba daya hankalin su ba'a kwance yake ba.

        Mutumin ya kallesu yace "Ku ci abinci mana ga abin shan ma"

       Salman yana kallonsa ya girgiza kai yace "Ba bukata! kawai ina son sanin dalilin kawo mu nan ne"

        Mutumin yayi dariya yace "To dai da farko ni sunana Khodaram Moham ni mahaifin Lakshmi, bani da kowa a duniyar nan sai Lakshmi don haka duk abinda na mallaka a duniyar nan nata ne, saboda mahaifiyarta ta mutu tun tana karama shi yasa duk wani abu da take bukata bana taba bari tayi kukan rashinsa. Mako biyu da suka wuce Lakshmi ta dora a shafikanta na Twitter Instagram Facebook Tiktok da Whatsapp cewa tana gayyatar duk wani saurayi dake a fadin kasar India, zata zabi miji cikin su kuma duk wanda yayi dace ta zabeshi a matsayin wanda zata aura to zai samu kyautar makudan kudade da gida da mota da kuma ita kanta Lakshmi din, ta bada mako uku ne yanzu kuma sauran mako daya lokacin yayi, sai gashi yau kwatsam tayi tozali da kai kuma taji duk duniya babu wanda take kauna sai kai babu wanda zata iya zaman aure dashi sai kai"

     Cikin mamaki Salman ya kalli Suhail yaga shima shi yake kallo, ya kalli yarinyar yaga tana kallonsa gata mummuna gata baka ga wata uwar kiba kamar bauna idan har ka kalleta baza so ka kara kallonta ba, ya kalli mutumin.

      Salman yace "To ai ni bana sonta don akwai wadda nake so, kuma ko babu wadda nake so ma ni bazan aureta ba saboda bata yi min ba!"

      Khodaram Moham ya kalli Salman rai a bace, yace "Ka sani tunda Lakshmi take bata taba neman abu a duniyar nan ban samo mata shi ba kuma ba za'a fara a yau ba!"

       Salman shima rai a bace yace "Ka nema mata wani mana amma bani ba, don ni zuciya ta wata ce bata Lakshmi ba!"

       Khodaram Moham yace "Kai yaro gwara ma ka mika wuya ka amince don in har kaki babu kai babu barin gidan nan har abada!"

       Salman gabansa ya fadi ya kalli Suhail cikin tashin hankali sannan ya maida hankali ga Khodaram Moham, yace "Karfa karfa za'ayi min kenan?"

      Khodaram Moham fuskarsa ba annuri yace "Matukar kaki amincewa ba!"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now