Chapter 8

5 1 0
                                    

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin✍️ 📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                      *page 15 & 16*

    Salman da Suhail suna dauke da Priya suna gudu, bodyguards din Khodaram Moham kuma suna biye dasu suna ta gudu a cikin daji wani wajen ma har faduwa suke sannan su tashi su dauke ta su cigaba da gudu, Priya kuwa tuni ta suma, a haka dai har suka kai bakin titi cikin sa'a kuwa suna zuwa sai ga wata motar kaya ta zo wuce babu kaya a ciki irin ta kai kayan ta dawo, suka tsayar da ita cikin sa'a direban ya tsaya suka hau suka dora Priya suka sa ya figi motar suka nufi cikin gari. Sai a sannan Salman ya lura da Priya bata numfashi nan fa hankalinsa ya kara tashi ya shiga jijjigata cikin dimuwa da tsoro, a haka har suka kai asibiti aka zo da stretcher aka dorata aka turata da gudu har zuwa ICU nan likitoci suka dukufa akan don ceto ranta, a tsaye Salman da Suhail suka kwana suna jimami da farbaga har dai likita basu damar zuwa su dubata, bayan sun shiga ne sun dubata duk bata san ana yi ba, Salman har da kuka ganin duk abinda ya sameta a kansa ne sai yaji sonta ya karu a ransa, bayan sun dan dade a dakin ne suka yanke shawarar kiran mahaifiyarta su sanar da ita saboda mahaifinta baya nan yana can New York yana aiki a can, haka kuwa aka yi suka kira mahaifiyarta suka ce mata wasu 'yan ta'adda sun harbi 'yarta Priya yanzu haka suna nan a asibiti, haka uwar ta hawo jirgin zuwa Goa cikin tashin hankali da zullumi.

                       Wannan Kenan!

_______________

NIGERIA

     Alhaji Ahmed da Rahima suna zaune a falonsu suna hira yayin da Aisha take a cikin daki amma tana jin abinda suke tattaunawa akai.

        A hirar ne Rahima ta kalli Alhaji Ahmed, tace "Alhaji na manta fa ban gaya maka kayan abincinmu ya kare saura na wannan makon kawai"

       Alhaji Ahmed yayi farat ya kalleta cikin mamaki yace "Wane irin ya kare? amma tun kwanakin baya baki gaya min ba bayan kuma kina ganin ina ta wadaka da kudi baki fada ba min ba sai yanzu da kudin suka kare zaki fada min!"

       Rahima ta kalli fuskarsa jiki a sanyaye tace "Haba Alhaji amma kasan.......!"

       Bata gama maganar ba sai suji sallamar Rahina da Rahila, Rahima ta tashi da sauri ta rungumesu cikin farin ciki su karaso ciki su zazzauna su gaisa da Alhaji Ahmed.

       "Sannunku da anty" Rahima tace.

       "Yauwa sannu da gida Rahima ya aiki?"

        "Lafiya kalau ya hanya?"

        "Hanya lafiya kalau" ta kalli Rahila tace "Sannu yaya"

         "Yauwa Rahima ya gida ya aiki da fatan komai lafiya?"

        "Duk lafiya kalau wallahi" sai ta kalli kofar daki ta kwallawa Aisha kira "Aisha! Aisha!"

        "Na'am umma" ta amsa tana daga cikin daki, sai ta fito.

        "Iyayenki ne suka zo, ki zo ku gaisa"

          Sai Aisha ta karasa kusa dasu ta zauna a kasa su gaisa.

       "Ki kawo musu ruwan sha mana"

       "To umma" ta mike ta nufi inda ruwan yake.

        Rahila ta kalli Alhaji Ahmed, tace "Amma Alhaji Ahmed yanzu Aisha ta saki jikinta ko?"

        Alhaji Alhaji ya gyada kai yana murmushi yace "Sosai ma kuwa fiye ma da tunanin mai tunani, kai idan ba gaya maka aka yi ba, baza kace ba'a wajenmu ta girma ba"
      
        Rahina tace "Ah to Alhamdulillahi"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now