Chapter 4

10 1 0
                                    

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

*page 7 & 8*

Suna cikin tafiya a cikin mota Aisha tana zaune a jikin Alhaji Inuwa sun nufi gidan mai unguwar Madabo.

Alhaji ya kalli Aisha, yace "Yaya sunanki?"

Aisha tana shashshekar kuka tace "Sunana Aisha"

Alhaji Inuwa yayi murmushi yace "Ashe ma sunan mommy nane dake? kiyi hakuri ki daina kuka!"

Aisha ta gyada kanta tana share ido.

Alhaji Inuwa ya sake dubanta yace "Yaya sunan babanki?"

Aisha tace "Abba"

Alhaji Inuwa yana kallonta yace "Yaya sunan mamanki?"

Aisha tace "Umma"

Alhaji Inuwa cikin yanayin tausayawa yace "Baki san sunansu na gaskiya ba?"

Aisha idonta ya ciko da hawaye ta gyada masa kai.

Alhaji Inuwa yana kara tausayinta yace "To ina ne unguwarku, ya sunan unguwar?"

Aisha ta kalleshi tana hawaye tace "Ban sani ba nima!"

Alhaji Inuwa yana ta mamakinta yace "Baki san sunan unguwarku ba ma?"

Aisha ta sake gyada kai.

Alhaji Inuwa ya dafa kanta yace "To kiyi shiru ki daina kukan, Insha Allahu zakiga iyayenki, kinji! ki daina kukan haka"

Suna tafiya har su kai bakin layin sai suyi Parking a bakin titi sannan su sauko daga motar su shiga lungun su nufi gidan.

*** *** *** ***

A gidan Rahila kuwa ana ta hidindimun aikin abincin biki, Rahima tana zaune tana yanka alayyahu, Rahina kuma tana kusa da ita tana ferayar kabewa, suyi suna hira. Rahila kuma ita da wata mata makwabciyar ta suna ta tsintar shinkafa, can gefe kuma wata tsohuwa ce daga dangin mijin Rahila take tankaden garin tuwo, sai Salisu da Magaji su shigo daga waje suna rike da dinkin da sukaje karbowa.

Rahima ta daga kai ta kallesu tana cewa "Ku ina kuma Aishar ku ka barota, ko tana waje ne?"

Salisu yace "Bamu ganta ba, tun a hanya ta bace mana"

Rahima ta mike tsaye a razane tana cewa "A daidai ina ne ta bace muku?"

Magaji yace "Muma bamu sani ba, mu dai mun duba kawai bamu ganta ba"

Rahima ta jawo mayafinta akan igiya tayi hanyar kofar fita waje da saurinta.

Rahina itama ta mike tace mata "Tsaya Rahima mu tafi in rakaki kada ayi biyu kinga kin dade rabonki da garin nan kada ayi biyu babu"

Sai Rahina ta dauko nata mayafin su saka yaran a gaba su fita, su bar su Rahila anan suna ta salati da sallallami tare da addu'ar Allah ya bayana ta.

*** *** *** ***

Alhaji Inuwa da Aisha da jama'arsa su karasa gidan mai unguwa, su sameshi a zaune akan tabarma shi kadai, bayan sun gaisa.

Mai unguwa cikin kaguwa yace "Lafiya kuwa?"

Alhaji Inuwa yace "Dama wannan yarinyar ce ta bata, kuma anyi mata tambayoyi daidai misali amma cikin ikon Allah ba'a gano iyayenta ba ko inda take, to shine naga ya dace in kawota gareku tunda kune manya ku kuka san hanyar da zaku bi wajen gano mata iyayenta"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें