Chapter 6

10 1 0
                                    

         ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                   *page 11 & 12*

       
    ' Kwanci tashi asarar mai rai inji bahaushe' yau kusan shekaru biyu da kama aikin Alhaji Inuwa, Ya kama daya daga cikin ma'aikatansa da al'mundahana don haka sai ya hada taro na  duk ma'aikatan, aka bawa wanda yayi ha'incin damar yayi bayani, amma duk cikin jawabin nasa zancen banza ne da surutun wofi babu wani abin kamawa, don haka sai Alhaji Inuwa ya fara yi masa masifa.

         Alhaji Inuwa cikin bacin rai yace "Zancen banza zancen wofi! wallahi in har baka fito da kudin aikin nan ba, ko kuma baka karasa aikin ba sai na daureka!"

         Ma'aikaci yace "Afuwa ranka ya dade za'a karasa cikin ikon Allah"

         Alhaji Inuwa a fusace yace "To wallahi na baka mako uku matukar baka gama ba sai na sassaba maka"

         Ma'aikaci yayi shiru ya sunkuyar da kai kasa yana nazari.

         Alhaji Inuwa ya kalli sauran ma'aikatan yace "Kuma ina so wannan ya zama izina a gareku, domin duk wanda ya ha'inci gwamnati sai gwamnati taga karshen zalincinsa" da haka ya tashi ya bar wajen taron.

         ***           ***           ***          ***

        Bayan Alhaji Inuwa ya koma gida da daddare bayan sallar isha'i suna cikin farin ciki da annushuwa tare da Hajiya Sailuba da Aisha.

          Alhaji Inuwa ya kalli Aisha, yace "Ummina kina kula kuwa a makaranta idan ana koya muku karatu?"

          Aisha tana masa dariya tace "Tambayi Aunty ka ji labari Daddy"

         Alhaji ya bata rai yace "Wane irin na tambayi auntinki sai kace tare kuke zuwa makarantar, ke dai kice ba za ki gaya min ba, to shikenan ba ruwana dake!"

          Aisha ta bata rai tace "Yi hakuri don Allah Daddy zan gaya maka kar kayi fushi dani!"

          Alhaji Inuwa yayi murmushi "To fada min ina jinki 'yar lele"

          Aisha tana murmushi tace "Daddyna ka hakura? sai ka hakura zan gaya maka!"

          Hajiya Sailuba tana tayi musu dariya.

           Alhaji Inuwa yayi dariya yace "To na hakura fada min"

           Aisha tace "Daddy ina da kokari sosai, Uncle dinmu ma yace a text din da mukayi ni kadaice naci 60 marks, haka ma Aunty dinmu ta makaranta tace mu uku ne mukaci homework da tayi mana"

           Alhaji Inuwa yana murna yace "Ummina ashe kina da kokari sosai, to ki kara kokari kinji ki dinga zuwa ta daya"

           Hajiya Sailuba tace "Ai gaskiya  Ummi tana da kokari sosai tace min likita ma take so ta zama, ko?"

           Aisha ta gyada kai tace "Kuma ance za'a gidan radio da television da mutum ashirin har dani a ciki"

           Alhaji Inuwa cikin farin ciki yace "Kaiii! naji dadi bari in an jima zamu kai ki wurin shakatawa da gidan tarihi da gidan zoo ki sha kallo kiji dadi ko?"

            Aisha ta gyada kai tana murna tace "Daddy na gode kema Aunty na gode"

        Haka kuwa aka yi washegari suka shirya suka he je gurin shakatawa mai dauke da kujeru da tebura da kayan ciye ciye da shaye shaye, sannan ga kayan wasan yara a gefe iri iri, daga nan suka wuce gidan tarihi su je dakin kayan tarihi suna ta ganin abubuwa suna dariya, sannan suje gidan zoo suna ta kallon namun daji suna nunawa Aisha, basu koma gida ba sai dare.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now