Part 4

89 1 0
                                    

16.....

Ranan Friday Imaan suka gama exams din first term ss2, suna tsaye tare da Mariya a bakin gate din makarantar tasu ko wannensu na jiran driver, Ummi da Rahma ko fitowa cikin schl din ma basu yi ba, Maimoon dai na tare da wata Kawarta a waje ita ma, Mariya na ganin motar Sadeeq tace "Lahh ya Sadeeq ne ma ashe shi sa ya bata mana lokaci" Imaan dai bata ce komai ba, tunda yayi parking idonsa ke kan Imaan, suna had a ido gabanta ya fadi, siblings din sa duk suka shiga motar, Mariya bata taba sanin Yayan nata na interacting da Imaan ba don Imaan din bata gaya mata ba, Mariya tace "Mu je ku gaisa da shi, shine ya ta6a ajiye ki gida ko baki gane sa ba" Imaan ta d'an yi murmushi kawai, Mariya ta kama hannunta suka nufi gun motar, Mariya tace "Ya Sadeeq frnd dita da ka taba ajiyewa a gida..." Ya cire glass din idonsa Yace "Yea na gane ta" Imaan ta sauke idonta kasa tace "Ina yini?" yace lafiya lau, fatan an gama exams lafiya" tace "Alhmdllh" yace "Toh Allah bada result mai kyau" ta daga kai tana kallonsa tace "Ameen" lallausan murmushi ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u mana" ta girgixa kai tace "Aa yanxu driver din mu xai xo" Yace "Ohk then" ta saci kallonsa ya kashe mata ido daya, ta daga ma Mariya hannu ta juya da sauri ta tafi gun Maimoon, Sadeeq ya tada motar ya bar wajen, Ya Yusuf ne ya xo daukansu bayan tafiyar su Sadeeq da kusan minti bakwai, Maimoon na turo baki tace "Ya Yusuf driver din fa?" Yusuf yace "Ya kai su Umma kasuwa, M.A aka ce ya dauko ku tun daxu ya ki, ni kuma ynxu na dawo aiki" Maimoon ta kyabe baki tace "Da dai Anty Farida aka ce yaje ya dauko, jiya fa da yamma har Hayin d'an bushiya muka je daukota taje gidan aunt dinta, baka ga uwar wahalan da muka sha ba ga hold up sai kusan shidda da rabi muka dawo gida" Yusuf yace "Au suna tare har yanxu kenan?" Maimoon tace "Tab, sosai ma, gobe xata koma schl sai kaga tulin shopping da yayi mata" Yusuf ya sake baki yana kallonta, Maimoon ta kyalkyale da dariya tace "Amma fa wllh ya Yusuf kar ka ce masa komai, dama yace kar in fadawa kowa" Yusuf yace "Ae ko kin fada ma kowa tunda kika fada gaban Imaan da Ummi" Imaan ta hade rai tana kallonsa ta madubi tace "Ya Yousuf kamar ya?" Ya wara ido yace "Ke sai ki kwasa ki kai ma inna, Ummi kuma ta gaya ma Umma, saukin abun dai idan magana ya fita an san it's either Imaan or Ummi sae M.A ya ji dadin jibgarku da kyau" Imaan ta xumburo baki tace "Naji dai" Ummi kuwa yi tayi kamar bata ji sa ba dama, suna isa gida Maimoon tace "Dama ya Yusuf ka ja masu kunne ba ruwana idan suka fada ma kowa" wani kallo Imaan ta watsa mata ta fice daga cikin motar tana turo baki ta kara gaba. Satin da aka shiga banda shirye shiryen bikin Seeyamah babu abinda ake a gidan, tun ranan lahadi yan uwa suka fara xuwa daga nesa gida ya fara cika da jama'a, kowa ya xama busy a gidan barin Umma da Anty, Ammi kam baya baya ta dinga yi, tun a ranan lahadin dama ta kai nata gudunmawarta na tsadaddun manyan bedsheets biyu, da set din food warmer shi ma biyu masu kyau sosai, a walakance Umma ta dubi kayan aka bar su a nan parlorn. Ranan laraba Abba ya ba su Maimoon kudin gyaran gashi da lalli a kai su Saloon, Har xa su fita ya dakatar da su ya ciro wani dubu biyar din yace "Na mance ban bada na mamana ba, gashi nan ta shirya ita ma ta je" Fita suka yi su hudu Ummi na cewa su yi wucewansu kawai don Imaan ba xuwa xata yi ba, Maimoon tace "Ba ruwana Abba cewa yyi mu je mu kira ta" A balcony suka tadda Anty tana magana da wa enda xa su yi girkin biki a biya su, Mujaheed ma na xaune balcony din sai Yusuf dake tsaye, Anty tace "Saloon din xa ku yanxu" Maimoon tace "Anty Abba yace mu je da imaan" Anty tayi wani dariya tace "Wace Imaan din tab, amma ku je dai ku ji abinda xata ce" Imaan na dakinta Maimoon ta shigo parlor, nan ta sanar ma Ammi abinda Abba yace Ammi ta kira Imaan, tana fitowa Ammi tace "sai ki dau Hijab ku wuce saloon" sosai gabanta ya fadi ta marairaice tace "Saloon kuma Ammi, aa ni dai xan wanke gashina da kai na" Ammi tace "Kee! dau Hijab ki fice min parlona, dama idan baki gyara gashin nan ba yau kar ki dawo min gidan nan" Imaan fa fashe da matsanancin kuka tana kallon uwar tata, ganin Ammi ta mike ta shiga daki da sauri ta dau Hijab dinta ta fita, Maimoon ta bi bayan ta tana dariya kasa kasa, Anty na ganinta tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" cikin kuka tace "Anty ni fa gashina bashi da wani datti kawai combing dinsa ne bana yi" Anty tace "Toh mu ga gashin" tana shesshekar kuka ta cire Hijab din ta cire hulan kanta,  Yusuf ya dauke kai bai son dariya ta fara wani sabon kukan, ga dai gashi har gashi amma duk an cukuikuye shi waje daya, Anty tace "When last kika wanke gashin" a hankali tace "Ranan nan" Anty tayi murmushi kafin ta ce komai Mujaheed ya mike fuska daure yace "Mu je in kai ku saloon din" Ta fashe da sabon kuka xata koma bayan Anty ya ja ta sai gun motarsa, Yusuf yayi murmushi  yace "Da yake Umma bata nan ba" Su Maimoon duk suka shiga motar bayan ya tura Imaan ciki, Suna isa saloon din Imaan ta hadiye kukan da take barin da taga yan mata kala kala cikin saloon din, Ita Mujaheed yasa a fara gyara ma gashin, da ruwa mai dumi sosai yace a wanke mata gashin nata bayan an sa mai, banda turo baki bbu abinda take tana runtse ido don ba daman kuka ga yan mata kar su mata dariya, lkci daya gashinta ya dawo sak na Indians sai sheki yake, ganin an kusa gama mata ya kalli kannin nasa yace "Sai ku samu napep da xai maida ku gida, coz I am a driver to none of you" daga haka ya fice saloon din, duk suka bi sa da kallo. Sai bayan magrib suka shigo gidan don har da lalle suka yi, dama Imaan direct part din inna ta nufa tun daga bakin kofa ta cire Hijab din jikinta ta shiga tana murmushi tace "Inna..." Inna tayi mitsi mitsi da ido tana kallon gashin nata tace "Ikon Allah kin ganki kin fito sak mace ko?" Imaan ta xaro ido tace "Toh da ni na miji ne?" Inna tace "Idan ba kallon isuhu nake maki wani lkcn ba shegiya nake" Imaan ta fashe da dariya har da kwanciya kan kujera, Inna ta kalli Mujaheed dake cin abinci tace "Ko kai baka gani ba Mujaheed?" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta mike xata shiga daki Inna tace "Dawo nan ana ma yar uwar ki gyaran jiki tunda can bangarensu ya dawo kamar wajen cin kasuwar laraba" Imaan tace "Anty Seeyama" Inna tace "Ehh kema da dai Allah ya fiddo maki da mijin nan kiyi aurenki da wuri ki haifi kanninki da uwarki taki haifo maki" Imaan ta hade rai tace "Yar karama da ni xaki ce min aure?" Inna ta kalli Mujaheed tace "Don Allah Mujaheed Imaan bata isa aure ba yarinyar da ke al'ada? Ga kirjinta cike da dukiyar fulani" Murmushi Mujaheed yyi kansa a kasa yana cin abincinsa, Imaan ta harari Inna ta juya ta nufi kofa inna tace "Ke kika sani, ni ba ruwana wllh, Allah na tuba lalurorin ki na duniya ma ai tsaye yake da kafafuwansa gun d'a na, ba gwara kiyi auren ko Bukar xai huta da kashe kashen kudi kije can kuma mijin shi ma ya d'an dana ukubar" Washegari alhamis Imaan ta tashi da ciwon ciki ga bak'i a part dinsu balle tayi raki yanda ranta ke so, duk magungunan da ta sha ba wanda taji ya mata, ta lallaba da kyar ta tafi bangaren inna, ita din ma dai parlon nata duk tsofaffin kawayenta ne a xaune, imaan ta gaishesu da kyar ta shige bedroom dinta ta kwanta, lkcn Azahar nayi dama inna ta lallabo ta shigo dakin ta sa ma bandakinta makulli don ba wanda xai shiga balle ya mata kazanta duk me son yin alwala ga pampo can ta bude, idan kuwa xai kama ruwa ne to yaje sashin masu biki, ganin juye juyen da Imaan take duk ta hada xufa duk da iskan fankan dake dakin ta wani xaro ido tace "Ke lafiya meye hakan, ni fa ba ruwana idan baki da lafiya ne ki tafi bangarenku kada a gigitani a nan, meye wani juye juye kamar macijiya a kan gado na" Imaan ta fashe mata da kuka tace "Wayyo cikina ke min ciwo" Inna tace "Auzubillahi, to rufa min asiri ki sakko ki tafi gun uwarki ba ruwana" Cikin kuka tace "Akwai mutane a can" a fusace Inna tace "Mutanen banxa ina ruwanki da su, idan wani abu ya sameki maganin me mutanen xa su yi banda su cika mu da surutu, dama ba komai ya kawo su ba sai kwadayin d'an shinkafar da xa a raba a kwano da kaji banda haka wani ma anyi shekara goma ba a gansa ba, ki tashi ki tafi tasan yanda xata yi dake idan ma asibiti ne ta kai ki, idan ko ba haka ba idan ban sa an dage bikin ba ace bani ba, biki ya fi rai ne" da kyar Imaan tace "Ni fa marana ke min ciwo" Inna tace "Wai jini?" Imaan ta gyada mata kai, Inna tace "Toh shi kuma wanda kika yi ko sati ba ayi ba fa?" Tace "Ba shi bane kawai alama ne" Inna ta xabga tagumi tace "Ke kam kina ganin jarabawa iri iri a rayuwa na lalura, banda haka jinin ma idan xakiyi sai kin ta fama, anya kuwa ba a sa maki hannu ba imaan?" Imaan ta xamo daga kan gadon tace "Wayyo ni dai ki kira min yaya " Inna tace "Waye kuma yaya?" Hawaye na sakko mata tace "Ni dai ki kirasa" Inna tace "Toh su wa encan tsofaffin duk tsami sun cika min parlor kamar ni xan aurar da 'ya sun ki tafiya, ni dai na gaji wllh ana damuna, wata ma ni nafi shekara talatin ban gan ta ba, ni dai gaskiya sun isheni suje can bangaren da ake biki kuma sun ki, duk parlona ya gauraye da warin tsofaffi, wannan fitina da mai yayi kama" Imaan na son yi dariya amma ciwo yaki barin ta tayi, Inna ta fita fuska daure ta kashe TV da ke aiki tace "Kada TV ya buga in ja ma Ahmadu asara gwara a bar shi haka nan ya huta" daga haka ta dau wayarta ta fita don neman me kira mata Mujaheed, wata ta samu a tsakar gida ta nufeta tana kallon mata yan gayu xaune tsakar gidan, tace "Toh dai gida ba na bitilman bane duk wanda ya xubda ko kwayar shinkafa yyi hakuri ya share fisabillahi, kar a tafi a bar mu cikin wari cuta ta kama mu" mika ma matar wayar tayi tace "Gashi Idan kin iya karatu ki duba lambobi xa ki ga ansa Dakta, lambar Mujaheed ne shi ya sa mun shi a haka, sai ki kira min idan kuma baki iya ba don Allah kar ki rikita min wayar in shiga uku" murmushi matar tayi ta nemo number tayi dialing ta mika ma inna, ta amsa ta kai kunne, sai da yayi ringing sau uku sannan Mujaheed ya daga, inna tace "Mujaheed??" Mujaheed yace "Ina ji, ya aka yi?" Inna tace "Toh ga yar uwar ka nan dai rai a hannun Allah, duk inda kake ka rufa mana asiri ka juyo ka dawo, ni sae in iya cewa a daga bikin ma wllh don idan ta mutu ni nayi asara...." Da mamaki yace "Wacece?" Inna tace "Wacece banda Imaan, tun safe Ashe tana dakina babu inda bata mirgina ba don ciwo, tun daga kan gadon har kasan tass, wai yanxu na shiga dakin don kulle bandakina saboda marasu hankali masu shiga bayin mutum suyi kaca kaca da shi kawai naga yarinya duk ta hada xufa a kan gado kai kana ganin ta kasan...." Mujaheed ya katse ta yace "Ina hanya" daga haka ya katse wayar, Inna tace "Atoh haka kawai, bikin banxa bikin hofi..." Daga haka ta nufi part dinta, tana durkushe bakin kofa tana watsi da takalman jama'a can gefe ganin duk ya cika mata bakin kofar ta ji muryar Mujaheed a bayan ta ta mike, tace "Wannan uban sauri haka kamar wanda ya biyo jirgi, to ka shiga tana can ciki ban san isilinta ba" Shiga parlon yayi ganin mutane ya sunkuyar da kansa ya gaishe su ya wuce dakin Inna, karasawa kan gadon yayi yana kallonta yace "Me ya faru?" Ta fashe da kuka sosai tace "Yaya cikina" hannu ya kai cikin yace "Tun yaushe?" Ta cire hannunsa tace "Ni ba cikin bane ke min ciwo, period ne" ya daure fuska yace "Toh me xan maki, ba kin sha magani ba" da kyar tace "Bai yi ba, doctor Habib allura yake min" yace "Toh me ya hanaki kiransa?" Tace "Yana Lagos" yace "Toh bani da allura a nan sai na koma asibiti" ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Toh ka tafi da ni asibitin plss" tana fadin haka ta fara kokarin sauka kan gadon, bude baki yyi ganin yanda tayi ma inna stain din kan gado, bai san lkcn da ya dauke kai yana murmushi ba don har ya hango inna, ita ma xaro ido tayi tace "Na shiga uku yaya" yace "Aa sai ta gani xaki ki shiga ukun ai, yanxu kina daya ne" ji tayi gaba daya ba ciwon ta sauko kasa da sauri jikinta na rawa tace "Wayyo yaya ya xan yi" Tana fadin haka ta nufi bathroom ta murda ta ji a rufe, tsayawa kallonsa tayi kamar xata yi kuka tace "Yaya ta sa makulli" parlor ya koma gun inna yace "Inna xata shiga bayi ina makullin" inna ta mike da sauri tace "Auzubillahi, wani bayin? Aa ta fito ta tafi nasu idan ma baxata iya tafiya ba ka goyata, haka kawai bayina fess ta shiga ta sa min k'arnin jini" Kunya ma yasa Mujaheed ya kasa cewa komai don mutanen dake parlon sun kai shidda, ganin inna xata shiga dakin ya rigata shiga da sauri, ya dau dankwalinta ya rufe saman gadon da shi, Imaan ta marairaice tana kallon inna da ta shigo tace "Don Allah ki ban makulli wllh xan wanke maki bayin" Inna tace "Ai uwata bata ce min je ki kya gani ba, don haka ba bayina xa a shiga a min kazanta da jini ba, ki daure ki tafi can bangaren ku idan ma tafiyar ne baxa ki iya ba sai Mujaheed ya goya ki" Kuka Imaan ta fara yi tace "Na fa ce xan wanke maki wllh" a fusace Inna tace "Kai ku fita ma ku bar min dakina kuje can bangaren ku karata, da na bar ki ma kika kwanta min saman gado duk da ban san al'ada kike ba" Mujaheed yace "Toh ki bata xan wanke maki bayin da kai na" Inna kamar xata rushe masu da kuka tace "Yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, wai ana dole ne, hypo uku na xuba bayin nan daxu da safe da nake wankewa, a kan wani dalilin xa aje a bata min da karni...." Ya katse ta yace "Ni kuma xan xuba maki hypo biyar" da kyar da kyar da sidin goshi inna ta bada makullin shi ma sai da aka yi yarjejeniyar baxa a bude mata drum din ruwa ba kada a xuba kazanta, Mujaheed ya dau buckets biyu ya fita debo ruwa a waje, Ita dai imaan na tsaye sai satan kallon saman gado take, Mujaheed na ajiye ruwan a bayin ta bi sa ciki tace "Wayyo yaya pant da pad da xan canxa fa?" Ya kalleta da mamaki yace "Ni ma kike tambaya?" Ta marairaice tace "Plss ko xaka je dakina...." Ya jefa mata wani kallo yace "You are stupid" fitowa bayin tayi ta bude gun kayanta a wardrobe din inna, ai ko taga panties dinta na nan, tace "Yaya toh saura pad"  Yace "Bari in xama pad din ki sa" Bata ce komai ba ta turo baki ta shiga bandakin ta rufe, juyawa yayi ya fita, ya tafi gun mai kiosk dake layin ya amso always daya ya dawo, inna dai na xaune ta daura kafa daya kan daya tace "Allah ni dai ya dubeni ya rabani da k'arni, komin xuba hypo da xa ayi a bandakin nan" Mujaheed bai ko kalleta ba ya shiga dakin, yana ta tsaye har Imaan ta fito daure da towel din inna, ya jefa mata pad din kan gado, ta turo baki tace "Thank you" komawa bandakin tayi ba a dau lkci ba ta fito, yace "Sai ki cire xanin gadon ki wanke" ta xaro ido tace "Yaya ya min nauyi fa" bude baki yyi yace "Toh ki bar shi haka nan" kamar xata yi kuka ta isa kan gadon ta shiga cire xanin gadon bayan ya dauke pillows din kai, Muryar inna suka ji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, jinin ta xuba min a kan gado ni Asabe????" Inna ta fashe da kuka tace "Me na maki xaki saka min da haka Imaan" Mujaheed ya dauke kai yana kokarin danne dariyarsa, imaan duk ta gigice, inna tace "Toh sai ki Kwashi xanin gadon don ubanki ki Bukar kai ma Aisha ta wanke min, kai kuma ka fitar min da katifar waje ka sa min shi a setin rana, Allah ubangiji ya saka min, daga taimako sai ta xuba min al'adarta a xanin gado k'arni ya kashe ni" Inna ta kara rushewa da matsanancin kuka tace "Sannan d'an walakanci tana yoyon xata dau tawul dina ta daura salon ta goga min gaibu, ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, tana cutata a gidan nan" Imaan ta wani hade rai kamar xata yi kuka, Mujaheed ya cire xanin gadon ya wuce bathroom da shi, Inna na matsar kwalla ta daga hannu biyu sama tace "Allah kaga xuciya daya nake xaune da kowa gidan nan, duk mai nufina da sharri ka min iyaka da shi" Tana fadin haka ta share idonta ta fita tace "Bari xanje inji ko Aishar ce ta sa ki xo ki cuce ni yau" Imaan ta murguda baki ta fiddo kayanta a press ta saka, bude kofar bathroom din tayi ta ga Mujaheed yana aikin wanke xanin gadon.

IMAANWhere stories live. Discover now