Part 21

169 4 0
                                    

106.....











Har Umma ta iso kusa da Inna Inna bata dago ba ta wani tsuke fuska tana ci gaba da abinda take, Umma tace "Sannu Inna" Inna tace "Sannu" Umma ta d'an risina tace "Ina yini Inna" Inna tace "Lafiya lau..." Umma tace "Ya gida ya aiki" Inna tace "Lafiya lau" Umma tace "To madallah, sannu da aiki" Inna tace "Toh ga dai kofar a bude..." Umma ta kalli kofar parlon Inna ta nufi parlon ta shiga ciki ta xauna, sai da Inna ta shafe minti sha biyar bakin tap din sannan ta mike murya can kasa tace "Uwar me ta xo min toh? Ni dai ba ruwana, bari ma dai...." Part din su Imaan ta nufa ta tadda Ammi xaune parlor, tana kallon Ammi bayan ta kulle kofa tace "Kina ji na Aisha?" Ammi ta mike tace "Ina ji Inna, sannu da xuwa" Inna tace "Bacci imaan take?" Ammi tace "Ehh yanxu ta kwanta" Inna tace "Toh ko da wannan mata Rukayya xata shigo nan kada ki kuskura ki yarda ta yi ido hudu da Imaan, a gaskiya idan kika yarda ta ga yarinyar nan wani abu ya sami jikata bayan tafiyarta to xan rufe ido in mance kina auren d'a na in dau mummunan mataki, babu wanda bai san Rukayya axxaluma bace, to banda wani sharrin mai xaman kansa ya kawota uban me xata shigo mana gida tayi kuma? Ni dai ba ruwana ki tafi ki makala ma kofar dakin jikata makulli iyaka idan Allah yasa ta shigo nan ku tsaya iya nan parlor kuyi tadin ku ta kara gaba, idan tace maki imaan fa kice ai tana can bangarena tun safe, don gaskiya idan wani abu ya sami jikata da cikin dake cikinta har Bukar sai abun ya shafa ba ke kadai ba, kai gwara ma abu ya same Imaan a kan wannan ciki na jikinta don ma ki ji" daga haka ta fice daga parlon, Ammi ta girgixa kai ta koma ta xauna, Inna na komawa part dinta ta shiga parlor tana kallon Umma dake xaune tana kallo, tace "Daxu wani almajiri na da muka dade tare tun ina gidan mijina ya xo na kawo masa swan water da ya rage a fridge, abinci kuma ba a kawo min na dare ba tukun" Umma tace "A'a ba komai dama na xo duba Imaan da jiki ne..." Da sauri Inna tace "Wace imaan din kuma? Ai Imaan ta warke garas tana ma ciki tana bacci bata son damuwa, A'a wllh ta warke tun yaushe ma, ai dama laulayi ne ba wani abu ba, dama baki yi asaran kudin motar ki ba duk da ban san daga inda kike ba amma jikata kam Alhmdllh tana ma ciki tana bacci abun ta" Umma tace "Toh shkkn Allah ya kara lafiya ni xan koma" Inna tace "Toh mun gode, Allah yayi albarka" Umma ta mike tace "Ameen nagode..." Inna tace "Har xa ki tafi?" Umma tace "Ehh xan koma" Inna tace "Toh yanxu wajen yayar taki mai shinkafa da wake a kasuwar tasha kike ko kuma wajen Hadiza a kano" Umma tace "A'a ina Zaria" Inna tace "Ayyoo, kuna da yan uwa a Zaria kenan?" Umma tace "Ehh" Inna tace "Toh madallah, sai dai kiyi kokari kiyi aure shine mutuncin ki da rufin asirin ki tunda dai kin ki xaman gidanmu, Allah ya hada ki da na gari dai" Umma tayi murmushi tace "Toh nagode" Inna tace "Toh kamar ina da canji bari in baki kudin mota" Umma tace "A'a ki bar shi Inna nagode" Inna ta bude jakarta ta fiddo hamsin biyu ta mika mata tace "Gashi nan kya yi kudin mota Allah ya kiyaye" Umma ta amsa tace "Toh Allah amfana" Inna tace "Ameen" leda dauke da can malt shidda ta ajiye ma Inna tace "Gashi ba yawa" Inna tace "Ke da kike fama da kanki kuma kya siyo mantina ki kawo min, Toh Allah yayi albarka" Umma tace "Ameen" Inna tace "Imaan din na ciki tana bacci da sai ince ki shiga ki ganta, amma bacci take" Umma tace "A'a ba komai, a gaisheta idan ta tashi" Inna tace "Toh xata ji" daga haka Umma ta fita parlon, Inna ta ta6e baki tana fito da malt din da daddaya da daddaya. Umma na isa part din su Imaan tayi sallama bakin kofa, Ammi dake parlon har sannan ta amsa sallaman, Umma ta shiga parlon, Ammi tayi mata sannu da xuwa, umma ta xauna tana amsawa, nan suka gaisa, Ammi ta tafi kitchen ta dau tray ta daura mata ruwa da lemo sannan ta fito ta ajiye kusa da ita tana tambayarta ya gida, Umma tace "Alhmdllh, Alhaji fa" Ammi ta xauna tace "Yana Abuja kuwa" Umma tace "Toh Allah ya taimaka, ya Imaan da jiki" Ammi tace "Jiki Alhmdllh, tana ciki ma" daga haka ta mike ta wuce dakin Imaan, Abinci Ammi ta sameta tana ci tana kallo a tv dake dakin, Ammi ta bude warmer din abincin tace "Yanxu wani abincin kike kuma ci Imaan?" Imaan ta marairaice tace "Na kasa baccin fa, yunwa kuma nake ji" Ammi ta tabe baki tace "Sai ki shiga kitchen da kanki kiyi wanda xa ki ci anjima baxan iya ba, ki fito ku gaisa da Hajiya Rukayya" Imaan ta xaro ido tace "Ta xo Ammi?" Juyawa Ammi tayi ta fita daga dakin, Imaan ta ajiye plate din abincin da ta cika dam bayan wanda ta ci ko awa daya ba ayi ba, ta rufe abincin, sannan ta sakko daga saman gadon ta bude press dinta ta dau ironed hijab dinta har kasa ta saka ta fito parlor, dukawa tayi har kasa bata yadda su hada ido da Umma ba tace "Ina yini Umma?" umma tace "Lafiya lau Imaan, ya karfin jiki" Imaan tace "Na ji sauki" Umma tace "Toh madallah, Allah ya kara lafiya" Imaan tace "Ameen, ya gida" Umma tace "Lafiya lau" Umma na kallon Ammi tace "Tun daxu na shigo Ina bangaren Inna" Ammi tace "Allah sarki, bari a xubo abinci" Umma ta mike tace "A'a Alhmdllh, xan shiga mu gaisa da Amina sannan in wuce, dama nace dai bari in daure in fito yau in duba jikinta" ledan hannunta ta ajiye kusa da Imaan, Ammi tace "Toh Allah ya amfana, Allah ya saka da alkhairi" Umma tace "Ameen sai da safe, Allah ubangiji ya kara mata lafiya" Godiya Imaan ta kara yi ma Umma, Ammi ta rakata waje, Imaan ta mike ta koma dakinta. Haka rayuwa ya ci gaba da kasancewa Imaan ta ji sauki sosai, bata da wani takamaiman aiki sai ci, komai ta samu ci take, da wanda bata ci a da, da wanda take ci, ita dai ta ci, son jiki kuma ya karu kan nada, ko kadan bata son stressing kanta, har wanka sai tace Ammi ta cuda mata bayanta,  Dama da Hajiya Inna ta ji footstep ta leka da sauri taga imaan ce ke xuwa boye duk wani abinta na ci take yi karkashin gado da gudu ta dawo ta xauna a parlor ta fuske, bbu abinda Mujaheed ya rage ta da shi na abubuwan ciye ciye da kayan makulashe, komai tace masa tana so ko karfe sha biyun dare ne sai ya fita ya siyo mata don yawanci a gidan yake kwana, wani lkcn kuma ya tafi gidansa, ganin irin kunyar Ammi da yake ji dake sa shi bai iya shigowa yasa Imaan da taga lkcn dawowarsa ya kusa daga gun aiki take wucewa gun Inna, duk Ammi na lura da ita amma bata ta6a ce mata komai ba, shi kam Mujaheed duk ya xuba masu ido a gidan ganin bbu wanda ke da niyyar cewa ya dau matarsa ya tafi ko suna nufin tana gida har sai ta haihu ne shi dai bai gane ba. Inna ce tsaye parlor sai mita take tana masifa tana cewa "Ni dai ba ruwana a daina xuwa ana 6ata min waje ana takurani, ke dai baxa ki iya xama bakin ki bai yi motsi ba ki wani shigo min parlon da na sha wahala na tsaftace da shegen bak'in gyada kina ci kina tara min 6awo a parlor salon parlona yyi wari, ita Aishar ce ta turo ki ki cuce ni ko Mujaheed din? Don nasan Bukar baxai turoki ki xalunce ni ba" Imaan dai sai cin gyadan ta take tana tara 6awon, Inna tace "Ni wannan wahala ya isheni wllh, wani da maki ciki ni kuma da cutuwa da wahala da cikin, kullum ayi ta cutata ana matsa min ana kazantar min da parlor, wlh na gaji, ni ba abinda na hada dake gaskiya balle mijin ki, shi mujaheed din da yayi miki cikin ki tafi dakinsa mana ki ci gyadan idan ba rashin tsoron Allah ba xaki yo min nan...." Mujaheed dake tsaye bakin kofa xuwan sa kenan yana cire takalmansa yana murmushi ya shigo parlon, Inna ta kallesa ta wani hade rai ta shige daki, imaan ta bi ta da kallo tana taunar gyadarta tana tabe baki, Xaunawa Mujaheed yayi kusa da ita yace "Wa ya siya maki gyada?" Ta wara masa ido tace "Xaka ci?" Yace "Aa na bar maki da babies dinmu ku ci ku koshi" Imaan ta 6ata fuska tace "Ni dai sai ka ci..." sakkowa yyi ya xauna gefenta ya jawota kusa da shi yace "Toh sai ki tauna ki sa min a baki" dariya tayi ta 6are daya ta kai masa baki, ya make kafada yace "Chew it first" Tace "Aa ni dai" lumshe ido yyi ya fara kissing lips dinta dai dai fitowar Inna daga daki.... Da sauri Imaan ta kauda kanta, Inna tayi kamar bata gansu ba tana kakkabe kujerunta ba tare da ta sake kallonsu ba tace "Ni dai a fita a bar min parlona ni ba yar iska bace, ni ba gantalalliya bace, kawai jaraba yayi yawa a duniya dai ga shi nan, Banda haka meye kuma xa a xauna min parlor ana tambada ba kunya ba tsoron Allah, ni dai ba ruwana, ban ma ta6a ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, meye kuma mutumi xaka xauna gun yarinya kamar xaka shige jikinta tana fama da kanta, a gaskiya ban san me kake nufi ba, ita kuma jarababbiya tayi mukus... Kai jama'ahhh naga abinda ya isheni ni patuu" mikewa Mujaheed yyi bai son yayi dariya yace "Ke dai baxa ki daina sa ma mutane ido ba a gidan nan" da sauri Inna ta kallesa tace "Maxa ku fitar min daga parlor ba ruwana, maxa maxa ku fita, kuma wllh kada in sake ganin kafafuwan ku a nan, bari kuma Ahmadu ya dawo, ni dai ba ruwana, tunda uwata ta haifeni ban taba ganin iskanci haka ba, haka ranan ka shige daki ka latse yar mutane saman gadona, wancan ranan kuma ka bi ta har bandaki ban san me ku ke yi ba, idan kuma kitchen ta shiga shi ma ka bita ka datse kofa, to wannan wani irin fitina ne, to kai baka da tsoron Allah ne? Ni dai ba ruwana wllh" Mujaheed na dariya yace "Idan kina sa min ido da ni da matata sai idonki ya tsiyaye nima ba ruwana" d'aga Imaan yayi suka fice daga parlon Inna ta bi su da kallo baki bude. Da daddare Abba ya shigo gaida Inna, ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tace "Ahmadu kana ji na??" Abba yace "Ina ji Inna..." Inna tace "A gaskiya ka yi ma d'an ka Mujaheed magana ya dauke matarsa su bar gidan nan, ko kuma in har xa su xauna gidan nan su daina shigo min ni ba gantalalliya bace, don abubuwan da nake gani sun isheni haka, ni dai ba ruwana baxan ce komai ba amma gaskiya ya dauketa tunda mun gama bauta da ita ta samu lafiya sai ma wani tashen fitsara da take min, ko mi ta ci ta bar min shi kaca kaca a parlor duk wari sai dai ni in dauke in share, shi kuma Mujaheed na yi masa uxuri don tun ba yau yake min rashin kunya ba dama can ya rainani, wllh ce min yyi idona xai tsiyaye, to idan idona ya tsiyaye ina lafiya Ahmadu? Naka xai kalli tsabagen idonka ya maka wannan mugun alkaba'i? To ba ruwana kowa yyi ta kansa wllh ba don kai da Bukar ba ni dai babu abinda na hada da Imaan da mutumin nan Mujaheed" Abba dai bai ce komai ba kansa na kasa. Daren ranan Abba ya kira Mujaheed parlonsa yace masa washegari dama ya tabbatar ya dau matar sa su wuce gida tunda mahaifiyarsa suke renawa, sosai Mujaheed ya ji dadin jin haka har ransa amma bai dago kansa dake kasa ba, Abba yace "Sai ka ci gaba da kula da ita, coz abinda take bukata kenan yanxu, if possible a samar mata yar dattijuwa immediately sbda house chores, if there is anything you let me know" kasancewar Washegari lahadi ne da safe Mujaheed ya tafi part din Inna don yasan da kyar Imaan bata can, Xaune ya sameta parlor tana shan shayi da bread leda guda, Inna dake share bakin kofarta tace "Jiya na ajiye maka fura da nono shiru shiru baka dawo ba kuma" yace "Ni da kika kora da matata kuma me xan yi da furan ki" daga haka ya shiga parlon yana kallon Imaan dake kokarin boye bread din da take ci da sauri, yyi dariya yace "I caught you..." Kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba duka xan cinye ba fa, nawa ne da na Inna" Inna tace "Karya take Mujaheed, daga wajen uwarta ta taho da shi, ba ruwana tass xata cinye shi, Ni wllh kada ma ta tsiyace min kai da wannan uban cin da take, ni gani nake ma ba na lafiya bane" Mujaheed yace "Toh Ina ruwanki?" Tsayawa Inna tayi tana kallonsa daga bakin kofa. Karfe sha biyu saura Imaan na saka Hijab dinta Ammi ta shigo dakin, tana kallonta tace "Ba abinda xaki tafi da shi" Imaan tace "A'a Ammi" Ammi ta xauna gefen gado tace "Toh na dai gaya maki ki rage ciye ciyen kayan xaki, sannan kuma ki daina wannan shegen son jikin kina kwanciya Kamar ruwa, try and be doing little works, ko da an kai maki mai aikin, sannan wanka kuma da kike yi da ruwan sanyi ki daina" Imaan tayi murmushi tace "Toh Ammi ai na daina" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" Imaan ta dau handbag dinta tace "Ameen, ai xan dinga xuwa fa bayan kwana biyu ki dinga min irin dambun da kike min" Ammi ta ta6e baki ta mike ta fita dakin, Imaan ta bi bayanta, gun mota ta tadda Mujaheed na jiranta, sai da ta shiga part din Aunty tayi mata sallama tukun tana bobboye cikinta da hijab kamar yanda take yi idan ta ga Aunty, duk gidan banda Aunty da Abba sai Yusuf babu wanda take boye ma ciki, da farkon fitowar cikin tana d'an jin kunyan Amminta tayi ta saka hijab tana takure kanta, amma daga karshe kuma kawai ta sake, amma Inna from day one take tsirara ma a gabanta da cikin, Aunty na murmushi tace "Toh Allah ya kara lafiya daughter, Allah ya kiyaye" Sabbin turaren humra da aka kawo ma Aunty ta debar mata da yawa sannan ta rakota har parlor imaan tayi mata godiya ta fita. Suna hawa saman titi Mujaheed ya kamo hannunta yace "Babu abinda xa a siya maki sweet?" Imaan ta langwabar da kai tace "Ni Ice-cream nake so plss Yaya, Ammi bata bari na sha wanda ka siya min shekaranjiya ba" Mujaheed yace "Toh amma karami xan siya maki sbda kinga garin da sanyi, bana son kina shan ice-cream din nan" Tace "Toh na ji, sai ka siya min har da pizza" ya shafa lap dinta ya kashe mata ido yace "Toh mum twins" ta turo baki tace "Bana so" murmushi yayi bai ce komai ba har suka isa babban eatry din Mujaheed yyi parking ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka a hankali, still tayi tana kallon motar da ya shigo yayi parking gefen motarsu a haraban eatry din...





IMAANOù les histoires vivent. Découvrez maintenant