Part 12

92 1 0
                                    

61



Mikewa Mujaheed yyi da sauri ya wuce sama, Safeenah ta wani tabe baki ta ki tashi sai ma kwanciyarta da tayi kan kujerar, Inna na kallon Imaan da ke tsaye tana kallonta tace "Lafiya kika fito ko basa nan ne?" A hankali Imaan tace "Nima ban sani ba" Inna ta kutsa kai ta shiga parlon tace "Ina kuma xa su ranan lahadi su bar kofa ba makulli kamar tababbu, ko dai baccin asaran suke..." Suna hada ido da Safeenah dake kwance Inna tace "A'a Safara'u, to tace min ba kowa, anya Imaan na da lafiya ma kuwa, Ina Mujaheed din?" Safeenah ta mike tana kirkiran murmushi tace "Sannu da xuwa Inna" Inna ta xauna tace "Yauwa sannu Safara'u, ana ta shan iska kenan, to ba kya sha ba gari duk xafi don ma dai akwai Ac, ai nima idan naji xafin yayi yawa dama daga ni sai yar shimi da xani nake xama na parlor, kar xafi yyi min illa..." Mujaheed ne ya dawo parlon sanye da jallabiya milk color kansa a kasa, Inna na kallonsa ta washe baki tace "Ina kwana Mujaheed" ya karaso ya xauna yana dube duben parlon yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, yau ba aikin kenan" Yace "Sai da yamma" tace "Toh ai jiki da jini, in gaya maka daga gidan ta Rasulu nake mun je mun yi sirrin mu shine nace bari in biyo mu gaisa kafin mu koma gida" magana take masa amma gaba daya hankalinsa na kan kofa, Inna tace "Sai kuma wannan yarinyar tace min baku nan, kai kaji walakanci..." Bata rufe baki ba kamar jira yake yace "Tana Ina??" Inna tace "Oho ni dai ba na shigo ba, dama tun da muka fito take min walakanci tana ganin mai adaidaita xai min rashin kirki ta gudu ta bar mu..." Mujaheed bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa Safeenah ta bi sa da kallon gefen ido, Bai ga Imaan a waje ba ya karasa gate yana kallon mai gadi yace "Warce suka shigo yanxu da kaka ta fita ne?" Yace "Ehh ta fita" Mujaheed ya fita gate din, can ya hangota har ta kusa titi, ya fi minti daya tsaye yana kallonta kafin ya juya a hankali ya koma cikin gidan, Inna na kallonsa tace "Ta ki shigowa ne halan? Rabu da ita ban iya wahala ni dai ai ta aan hanya" Bai ce mata komai ba ya wuce sama Safeenah da ta wani daure fuska ta bi sa da wani kallo. Bayan kusan minti talatin Mujaheed ya sakko downstairs sanye cikin kananun kaya hannunsa rike da makullin mota, Inna na xauna ga plate din farfesun kaji gabanta tana ta yaga tana ma Safeenah hira, Safeenah dai na xaune sai kallonta take uninterested, Inna na kallon Mujaheed tace "Ina kuma xa ka?" Yace "Ba dadewa xan yi ba...." Daga haka ya fita parlon, da sauri Safeenah ta mike ta dau Hijab ta bi bayansa, Inna na cewa "Maxa je ki ku yi sallama" Har ya shiga mota Safeenah ta samesa cike da shagwaba tace "Ina kuma xuwa sweetheart, bayan ka min alkawarin baxa ka fita ba yau" Ya tada motar ba tare da ya kalleta ba yace "Ba jimawa xan yi ba" Tace "Ohk then, bari in raka ka" sai a sannan ya kalleta yace "I don't think it's necessary Safeenah" da wani expression take kallonsa, yace "Forget about the previous plan on what to cook, tunda grandma na nan kiyi tuwo kawai with vegetable soup, I will be back soon" tana masa wani kallo bluntly tace "Wllh baxan yi ba, sai ka taho da tuwon daga inda xaka yanxu..." shi dai ba kulata ba ya rufe motarsa ya gama warming mota ya danna horn mai gadi ya bude masa ya fita. Mujaheed na isa gida yyi parking a waje, ya shiga compound dinsu, tun da ya shiga yake kallon part din su Imaan, gently yake tafiya, ya kalli apartment dinsu sannan ya wuce, yana isa part din su Imaan ya danna bell, sai kuma ya bude kofar yyi sallama ya shiga, Ammi ta leko daga kitchen taga ko wanene, gaisheta yyi ta amsa tana welcoming dinsa ta fito, Bai xauna ba yace "Dama kawai na shigo mu gaisa ne" tace "Toh nagode, ya gida?" Yace "Alhmdllh" tace "Maa sha Allah" ba tare da ya kalleta ba yace "Imaan na ciki ne?" Tace "A'a" da sauri ya juya yana kallonta, tace "Yanxu na aiketa taje kai ma Aunty sako" Bai san lkcn da ya sauke ajiyar xuciya ba yace "Toh, sai anjima" tace "Allah ya bamu alkhairi" fita yyi parlon ya wuce part din su, Umma na xaune parlor da Rahma suna magana kasa kasa, Umma na kallonsa da murmushi tace "A'a sannu da xuwa Mujaheed, yanxu ko nake cewa bari driver ya dawo xa mu je can gidan Hajiya Balaraba daga nan sai mu biya naka, tunda ku ka tare ban je ba" ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Toh ina Safeenar?" Ya mike yace "Tana gida tace a gaishe ku" Umma ta bi sa da kallo ganin sama xai wuce tace "Ina kuma xaka?" Yace "Xan dau wasu takardu a daki" Daga haka ya haura sama, murya can kasa Rahma tace "Ita fa Mariyan ma ba kowa take kulawa ba wllh Umma, bari dai Ummi ta dawo ki ji, ai ajinsu daya har schl" Umma tace "Toh ita Imaan din ta ta6a xuwa gidansu Mariyan ne?" Rahma tace "Suna xuwa da Maimoon sosai ma" Umma tace "Atoh, Da bata xuwa ai baxa su santa ba har su mata kyauta gun sauka, har fa da yin hoto da uwar yaron da kishiyarta" Rahma tace "Imaan da bata kula maza amma saboda taga d'an mai kudi ne she didn't think twice kafin ta fara kulasa, kila ma a gidan nasu suka hadu" Umma tayi wani murmushi, murya can kasa tace "Toh xa ki yi abinda nace maki din?" Rahma tace "Toh umma ai ba shiri muke da ita ba fa, gwara ma Ummi" Umma tace "Toh yanxu ai xata dawo..." Dakin Aunty Mujaheed ya bude yana kallon ciki, Maimoon ce xauna kasa kusa da Aunty dake xaune kan stool tana mata kitso, Imaan kuma na xaune kasan rug tana kallonsu, Imaan na ganinsa tayi saurin dauke kai, ya shiga ya rufe kofa idonsa a kanta, Maimoon ta gaishesa ya amsa, Aunty ta sake kitson da take tace "Welcome son" Mikewa Imaan tayi tace "Toh Aunty ni xan wuce" Aunty tace "Au kin fasa kitson kenan, dama nasan baxa ki yi ba, kice ma Ammi xan shigo nan da anjima" Imaan dake murmushi don ita kanta tasan kawai dai tace Aunty ta mata kitson ne amma ba yi xata yi ba, lokaci daya murmushin fuskarta yyi fading ganin Mujaheed ya fita dakin, tana ganin haka ta hade rai ta koma ta xauna tace "Toh tunda xa ki je shikenan, sai mu koma tare" Aunty tace "Toh shkkn" Mujaheed ya fi minti biyu tsaye corridor ganin bata fito ba ya bude kofar dakin, Aunty tace "Yau dai yan miskilancin na kusa ne ko doctor, Ina yini toh?" D'an murmushi yyi yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Atoh, ka shigo Ina welcoming dinka kayi kamar baka ji ba kuma ka fita" ya shafa kai a hankali yace "An kira ni ne a waya na fita" Aunty tace "Ohk, ya amarya?" Yace "Tana gaishe ku" Aunty tace "Toh muna amsawa" duk irin yanda ya kafe imaan da ido bata yarda ta kalli direction dinsa ba, har ya juya ya fita, Imaan bata bar part din Aunty ba sai da ta gama ma Maimoon kitso suka koma part din su tare da Auntyn, har sannan kuma Mujaheed na xaune parlor, ya bi su da ido har suka fita Imaan ta saci kallonsa suka hada ido da sauri ta dauke kai ta shige gaban Aunty tana turo baki. Daren ranan Imaan na part din Inna suna dakinta, Inna sai famar rura wutan dake kasko take da baki, Imaan kuma na tsaye kamar xata yi kuka, Inna ta ajiye wutan tace "Ke dai ki daina haka imaan, ni wllh idan kina bani wahala xan tattara lamarin ki in xubar a kwandon shara, ya xa ki dinga ban wahala ina taimakon ki? Baxa ki cire kayan ba ki xo ki durkusa, kai wllh Bukar dai ya haifi jaraba" Imaan tace "Toh wai ni kin manta bana son hayaki ne, yanxu idan asthma dina ya tashi fa?" Inna tace "Meye kuma asma? Kiyi ta kira ma kanki ciwo, Ke dai ki ji tsoron Allah, abinda nace d'an minini xan yarfa a wutan ki shaka ko kadan ne sai ki fita da gudu, idan fa aka kashe ki ko digon hawaye na baxan yi asara ba wllh" Imaan ta rungume hannu tace "Wllh bana so ni dai, gwara inyi wanka da shi, haka kawai inje asthma na ya tashi inyi ta wahala" Inna tayi tagumi tace "Kai ina shan wahala ni patuu, ni dai ba don ki kadai Allah ya halitto ni ba wllh" tana fadin haka ta mike ta dau kullin magani ta wuce bayi tana cewa "Sai ki cire kayan, idan ya kama ma in cuda maki maganin da kai na sai in cuda maki baxan yi asaran kudi ne a banxa ba" Imaan na turo baki ta fara cire rigar jikinta, tana cikin cire skirt taji an bude kofar dakin, xaro ido tayi ta fasa ihu ta durkusa a kasa, da gudu Inna ta fito tana cewa "Shikenan ta fada cikin garwashi ta kai ni ta 6aro gun Bukar...." Inna ta gwalo ido ta kalleta ta kalli garwashin wutar don ta tabbatar bata fada ciki ba, Inna na nunata tace "Anya imaan xaki wanye lafiya da duniya kuwa??" Imaan da ta takure gu daya tace "Ni dai Inna wllh kice masa ya fita" da sauri Inna ta kalli kofa ganin Mujaheed tsaye ta xaro ido tace "Me xan gani haka?? Kai ya haka xaka afko mana daki ba sallama, baka ganta a tu6e bane Mujaheed, yaushe ka xama haka?" Shi dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita, Inna ta tafe hannu tace "Yau naga abinda ya isheni, toh tsaye ya gan ki da ya shigo?" Kamar xata yi kuka ta gyada masa kai, Inna tace "Toh shi ya ga duhu wllh, tashi ki shiga kiyi wankan ki, shi yaga duhu" Imaan ta mike ta dau towel ta daura tana turo baki ta wuce bathroom, Inna tace "Kaji min gantalalle, Toh wani salon iskanci ne wannan xai shigo maki daki kin tu6e?? Ni dai ba ruwana, don mutum yyi aure kuma sai ya fiddo da fi'ilin iskanci iri iri, Toh wllh shi ya ga duhu" Tana fadin haka ta sa makulli a kofar tace "Ba ruwana" Tun daga wannan rana da imaan ta ga Mujaheed xata canxa hanya ta wani daure fuska..... Inna na parlor ta daura kafa daya kan daya da yamma tana kallon wani film Ummi ma na parlon ta gama mata kitso kenan, Inna sai tsine ma boss din film din da suke kallo take, duk ta cika parlon da muryarta, Ummi sai dariya take tana cin soyayyen nama da Inna ta yarfa mata a plate, sallama aka yi bakin kofa Inna ta amsa tana kallon kofar, Sadeeq ne ya shigo da leda a hannunsa, Inna ta mike da sauri tace "A'ahh sannu da xuwa Bukar, kai ne da yamma haka, Bisimillah" ya karaso yana murmushi ya xauna, Inna tace "Ya iyayen naka?" Ya xauna yace "Alhmdllh, suna gaishe ku" Inna tace "Tohh ina amsawa wllh, Ummi tashi ki debo masa ruwa a fridge da lemo, idan kuma baxa ki ba in tashi" Ummi dake kallonsa ta gefen ido ta mike ta nufi kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo ta ajiye masa tray din drink da ruwa ya kalleta yace "Nagode" Ummi ta koma ta xauna tana kallonsa, Inna na kallon Ummi tace "Toh kiyi wucewar ki ai mun gama kitson ko? Allah maki albarka" Ummi ta wani hade rai sai kuma ta mike ta nufi kofa, ko ba a gaya ma Sadeeq ba yasan kanwar Mujaheed ce don kamar da suke ba na wasa bane, Inna ta tabe baki bayan ta fita tace "Toh sai ta wani xauna cikin manya, ai bai dace ba" Sadeeq na shafa kai yana murmushi yace "Dama Ina son xa mu yi magana ne Kaka" Inna ta gyara xama tace "Toh Bismillah, Ina jin ka Bukar in ji dai lafiya" Yace "Lafiya lau, dama Kaka Abbana ne ke min maganar aure tun da dadewa, na gaya masa yanda muka yi da ku a nan yana ganin kamar kawai xance nake masa...." Inna ta katse sa tace "Aa ba xance kake masa ba wllh su Ahmadu ne suka dakatar da kai, toh amma ni dama faduwa ta xo dai dai da xama, ba ruwana yau xan kira Ahmadun a gama magana, in sha Allah xuwa nan da Juma'ah ko lahadi xai ce ka turo magabatan ka, kwantar da hankalin ka Bukar in Allah ya yarda komai ya xo karshe, Sakandari?? An dade ba ayi sa ba in har xancen sakandarin xa su kara min, ni ba karamin aikina bane in tura ku kano gidan kawu Salisu ku kai gaisuwan da sadaki can" ya d'an yi murmushi, tace "Allah ba batun dariya ba, ai idan muka ci gaba da biye su Ahmadu da Bukar sai mu yi sa6o mu hallaka, haka kawai su ja mana fushin ubangiji kiri kiri suna fiffita abun duniya kan sunnar ma'aiki" a hankali Sadeeq yace "Toh nagode Kaka Allah ya kara girma" Inna tace "Atohh, duk ya ake ciki xuwa gobe xan kira ka kaji" Yace "Toh xan koma kaka" tace "Toh Allah maka albarka" ya ajiye mata ledan hannunsa yace "Ga turare na kawo maki Kaka" Inna tace "Kamar kasan bbu komai dakina sai fankon gwangwanayen turaren na jera gaban madubi" Yar dariya yyi ya nufi kofa ya bude, da sauri Ummi ta ja baya, sai kuma ta fara tafiya ko takalmi bata tsaya sa wa ba, Sadeeq ya bi ta da kallon mamaki bai dai ce komai ba ya fita ya sa takalmansa ya wuce, A gate ya kusa cin karo da Imaan xata shigo compound din hannunta rike da pack din bottle water, ta koma baya da sauri, ya wara ido ya fito murya can kasa yace "Baby" Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini?" yace "Lafiya lau, where are u coming from?" Tace "Na je siyo ruwana ne" yace "Iyye bottle water kike sha kenan" murmushi tayi bata ce komai ba, yace "Toh kawo in taya ki kai wa ciki" ta girgixa kai da sauri tace "A'a nagode" Bata fuska yyi yace "Plss let me help" Bai jira cewarta ba ya kai hannu xai amshi ruwan, hannunsa na ta6a nata ta sake ruwan ba shiri, shima kuma da sauri ya janye hannunsa ruwan ya fadi kasa, dukawa yyi ya dauka yace "Ohh Subhanallah, sorry plss" Murmushin karfin hali tayi ta shiga gidan ya bi bayanta, Xaune Imaan taga Umma da Ummi kan fararen kujera a can Balcony dinsu Umma ta bata attention gaba daya, Imaan ta dauke kai da sauri, shima Sadeeq hakan yyi har suka isa part din su Imaan, imaan na kallonsa tace "When did you come?" Yace "Some minutes ago, am tired Imaan na xo na sami grandma ne plss a ban ixinin in turo magabatana ko ba yanxu xa ayi biki ba..." ita dai Imaan bata ce komai ba, ya ajiye ruwan hannunsa a kasa, ta duka ta dauka tace "Toh nagode sai mun yi waya" daga haka ta wuce ciki, ya bi ta da kallo sannan ya wuce yana murmushi. Abba ne xaune parlon Inna tare da Mujaheed da xuwansa gidan kenan, har Inna ta kai aya a xancen da take Mujaheed sai kallonta kawai yake, Abba dai kansa na kasa, can Abba ya daga kai ya kalleta bayan tayi shiru yace "Toh ai jarabawan ma saura wata daya da sati biyu in sha Allah Inna" Inna tace "Ku kuka jiyo wannan kuma ni ina ruwana, ya xa ku dinga maida ni karamar mutum gaban yaron nan, gaskiya wannan karan bana son magana da yawa sabili da kar raina ya baci, ga abinda nace in dai kuna tsoron Ubangijin ku, meye kuma wata daya da rabi Ahmadu? Shi auren ake gudu kuma yanxu ana rirrike boko hannu biyu, Me yasa ku ke haka?? Ni dai idan na isa da ku gwara a hada bikin ma da na wannan yaron Isuhu tunda an ma kusa kai sadakinsa" Mujaheed dake kallonta har sannan yace "Don dai an jira wata daya da kwanaki ban ga wani damuwa ba, hanxarin me yake??" Inna tace "Amma gaskiya idan xan yi maganar arxiki Mujaheed ya daina shigo min parlona, a daina xuwa min da shi" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, tana kallon Abba da karfi tace "d'an bakin ciki ne fa Ahmadu, ya xai  yi aurensa yaje can yana morewa da figaggiyar matar sa amma ya dinga yi ma yar Uwarsa bakin ciki, haka yake so tayi ta xama a gida kamar ba mashinshini?" Mikewa Abba yayi yace "Toh shkkn, xa mu ba yaron ranan da xai turo magabatan nasa in sha Allah" a fusace Inna tace "Yaushe?" Abba yace "Nan da ko kwana uku in  Allah ya yarda sai a hada bikin da Yusuf yanda kika ce" Inna tayi murmushi tace "Toh Allah ya kai mu lafiya ya maku albarka" kallon Abba da ya nufi kofa kawai Mujaheed yake har ya fita yana amsa maganar Inna da Ameen, can ya kalli inna da ta mike ta fara kakkabe kujeru, yace "Kin kagu ta bar gidan kenan??" A fusace tace "Ba ruwan ka, wai ma dai meye hadina da kai Mujaheed??? Ni dai nasan na haifi Ahmadu amma wllh da babu abinda ya hada mu gwara kayi ta kanka, kiri kiri ka dinga nuna ma jikata bakin ciki??" Yana murmushi ya mike yace "In sha Allahu wannan auren da kike ta 6arin jiki a kansa baxa ayi ba, kuma har tsayuwar dare sai na yi akan hakan" salati Inna ta saki tana kallonsa, sai kuma ta fashe da kuka tace "Baxa ayi ba?? Ehh lallai ka zama dan iska Muhammad, ita yar Bukar kake ma bakin ciki?? Me ta maka xaka mata wannan fatan" ko sauraranta bai tsaya yyi ba ya fice daga parlon, a hankali yake tafiya don shi kansa bai ma san lkcn da ya fada mata hakan ba. Abba na komawa dama ya kira Daddy ya gaya masa yanda suka yi da Inna, Daddy dai bai iya yace komai ba, Abba yace "So yanxu na yanke ranan Sunday as ranan da xa ace ya turo parent din nasa, kai kuma sai ka dawo Saturday or Friday" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shkkn Allah ya kai mu, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi" Abba yace "Ameen" daga haka suka yi sallama ya katse wayar. Washegari Abba ya kira Sadeeq ya kuma basa izinin turo magabatan sa ranan lahadi, Sadeeq was so happy, farin cikin da bai taba yin irinsa ba duk tsawon rayuwarsa ya dinga yi ma Abba godiya kamar ya masa albishir da aljanna, Mujaheed dai na xaune parlon shi ma don tun safe Abba ya kirasa, amma banda danna wayarsa babu abinda yake, lkci daya ya dago yana kallon Sadeeq suna hada ido ya dauke kai, ya mike ya kai wayarsa kunne yyi excusing kansa ya nufi kofa hakan yasa Abba ma ya bi sa da kallo kamar yanda Sadeeq yyi.



IMAANWhere stories live. Discover now