Part 6

99 1 0
                                    

26.....



Ammi ta dinga kallonsa kafin a nutse tace "I want to give u this warning Mujaheed, stay away from Imaan" shi dai bai yarda ya kalleta ba, bai kuma ce komai ba, juyawa tayi ta bar bakin kofar, Mujaheed ya fita xuwa kofar fita parlon. Washegari da safe Imaan ba inda bata duba ba a dakin tana neman wayar Mujaheed ganin bata gansa inda ta ajiye ba, kamar xata yi kuka ta fito parlor sanye da uniform din islamiyya, tana kallon Ammi a hankali tace "Ammi kin ga wayar nan na jiya?" Ammi ta mata wani kallo tace "Wanda kika bani ajiya?" Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin ko kallonta Ammi bata sake yi ba ta juya ta wuce dinning don yin breakfast, mamaki ta dinga yi ta ya xata nemi wayar ta rasa a inda ta ajiye, daga karshe tayi concluding kawai Ammi ce ta boye, ta tura soyayyen dankalin gabanta ta mike ta dawo cikin parlor, safarta ta sa ta xura Hijab din makarantarta ta dau jaka tana kallon Ammi dake parlor kamar xata yi kuka tace "Ammi fa kila xai yi amfani da wayarsa don Allah ki bani in kai masa plss" Ammi ta daga kai tana kallonta, da sauri Imaan ta fice daga parlon don ta san sauran, parking space ta tafi ta tsaya tana jiran su Maimoon su fito, Mujaheed ne ya fito tare da Yusuf, Imaan ta dinga kallon hannunsa da mamaki ganin wayarsa, bai ko kalli inda take ba ya nufi gun motarsa ya bude ya shiga, Yusuf dake kallonta yyi murmushi yace "Why are you looking at him that way" kamar xata yi kuka tace "Ya Yusuf jiya ya dauke min wayata shine nima naje dakinsa na dauke nasa toh yanxu ga na sa a hannunsa ban san ya aka yi ya dauke ba, ni kuma nawa har yanxu ya ki bani" Yusuf yace "Toh me yasa ya dauke wayar ta ki?" Tace "Nima ban sani ba kuma har daki na ya shiga ya dauka, ni dai wllh ya bani waya ta xan je in gaya sa da inna" Yusuf ya kalli Mujaheed da har ya tada motarsa amma idonsa na kansu, dauke kai Yusuf yyi yace "Yaushe har ku ka fara shiri da Mujaheed da har ya shiga dakin ki ya dauke waya?" Ta turo baki tace "Ni ba wani shirin da mu ke, kawai ganinsa nayi a dakina bayan Ammi da daddy sun fita" Yusuf ya sake kallon Mujaheed da yaki driving din motarsa, ya dauke kai, Imaan tace "Ya Yusuf ka yi masa magana plss kuma fa ana kirana a wayar" Yusuf yace "Wa ke kiran ki?" Boye fuskarta tayi ta fara dariya, Yusuf ya dinga kallonta, ta xame Hijab din da ta rufe fuskarta a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa yace "Baxa ki gaya min ba" ta wara ido tace "Ya Yusuf wani ne, he is my friend" jin Yusuf bai ce komai ba tace "Ni dai kafin su fito bari in je in gaya ma inna" daga haka ta wuce ya bi ta da ido kamar yanda Mujaheed ma ya bi ta da kallo, waje ta ga inna tana ta faman goge window with seriousness, Imaan tace "Ina kwana inna" Inna ta d'an kalleta kafin ta dauke kai tace "Aa ba wani inna ina kwana, ke din ce xa ki xo gaisheni takanas da safe, ke dai fadi abinda ya kawo ki ina ji" Imaan tace "Toh ko ba yaya bane ya dauke min wayata tun jiya ya ki bani" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, Inna ta ajiye tsumman hannunta a bokiti da mamaki tace "Waye kuma yaya?" Imaan ta rungume hannunta xata yi kuka, inna tace "Lallai ba lafiya, shi Mujaheed din akwai wani alaka ne tsakanin ku wanda ni ban sani ba da har xai dauke maki waya? ko sata ya fara yi ba a sani ba a gidan, ni dai naga abinda ya isheni, gaskiya wannan d'a na Ahmadu yana cutar mu a gidan nan, to meye kuma xai dauke maki waya kamar shi ya siya? ko yana bin ki bashi ne? Toh a gaskiya ya kamata Mujaheed yyi aure ya kama gabansa na gaji da maganarsa kuma haka Allah ya gani nayi kokari, shekara kusan talatin da biyu ana abu daya, wannan ai fitinanne ne mara son xaman lafiya, mu je gun Ahmadu in ji ko shi ke koya masa ya dinga walakanta ni a gidan nan" daga haka inna tayi gaba imaan ta bi bayanta, Inna ta tsaya kamar warce taga mugun abu ta juyo da sauri tana kallon Imaan tace "Toh da ya dauke wayar ta ina Bulasawan ke kiran ki?" Imaan tace "Toh ba wayar na wajensa ba, kila ma ana ta kirana ya daga" Inna ta saki salati tace "Ashe yau xa a ga barbadin fitina a gidan nan, mu je gun Ahmadun" Yusuf na nan tsaye inda yake, Mujaheed kuma ya wuce kenan inna ta iso kamar xata tashi sama, Yusuf na kallonta yace "Ina kwana Inna" a fusace ta juya tana kallonsa tace "Da ban kwana ba xaka gan ni, ko a titi kake gaida uwarka Amina, to hirr dinka... Dama duk gantalallen da yace jikata xai sa ma ido ya dinga yi ma bakin ciki to yyi ta kansa inyi nawa a gidan nan, ba ruwana, kada ma ka sake gaisheni bana so, ko kuma in tsine ma gaisuwar...." Kallonta kawai Yusuf yake bai ce komai ba, Inna ta wuce kamar xata tashi sama, imaan da ta ki yarda ta kallesa ta bi bayanta, Anty na goge goge parlon Abba inna ta shiga imaan na biye da ita, Anty tana kallonta tace "Ina kwana Inna?" Inna tace "Ke ba xancen ina kwana, Amina ashe kema jaraban kika haifa ban sani ba sai jiya, ashe Isuhu ma ba mutumin kirki bane na banxa ne ni ban sani ba, ashe halinsa daya da tijararren nan Mujaheed, to Ahmadu ya ga ta kansa kuwa don wannan ba yaran nunawa bane, banda haka ta ya xa su nuna bakin ciki da hassadansu a fili kan jikata, daga Allah ya axurtata da mai kudi saurayi sabon jini sai hassada ya tashi? toh wllh su cire idanuwansu kan imaan, shi Isuhu tsabar shaharan da yayi a fannin bak'in ciki ce min yyi a bar xancen sabon saurayin ma gaba daya, ke ki ji min mugunta, kice min lalacewa bai xo duniya ba?? saboda mamakin abinda yace min sai nake tambayarsa ko idan aka bar batun sabon saurayin su xa su aureta?? Budan bakin katon sai ce min yyi to na sani ko su xa su auretan? Ke ki ji wani sa6o fa, kawai ya ja gida ya rushe da ni a ciki" Inna ta fara matsar kwalla tace "Yanxu Isuhu bai ji kunyar gaya min haka ba, idan ba ta6ewar basira ba dama ina su ina Imaan daga shi har Mujaheed din, wllh ta fi karfinsu, me garesu da har xa su rike min ita salon wataran in xo daukar gawarta ina kuka suna bani hakuri, haka kawai su kai ni su baro, yanxu fisabilillahi Allah ya dubeni ya fiddo mata dai dai ita kuma sai bakin cikin yan uwa ya tashi, to Allah ya so ni dama ba abinda na hada da su, ba dangin iya balle na baba, kawai ni dai nasan na haifi Ahmadu shi kuma ya haifesu, ni sai ince Bukar ya tattara ya bar gidan ma...." Shigowar Abba yasa ta dakata, Abba na kallonta yace "Lafiya inna?" A fusace tace "Ina fa lafiya Ahmadu isuhu da Mujaheed sun fi karfina, kawai yaro ya dage ya kwace ma yarinya waya sai kace Rukayya ce ta siya wayar, to wllh kafata kafar wayar nan yau idan ba haka ba in bar kowa da Allah, kuma gaskiya a daina bata min rai gidan nan don duk ranan da xuciya ta debeni idan ban bi Bukar Abuja ba ace bani bace" Abba dai ya kasa cewa komai, Ajiyar xuciya Anty ta sauke tace "Toh ina Mujaheed din?" Inna tace "Sai ki tambayeni Mujaheed ba tare ku ka kwana gidan nan ba ke kuma" Abba ya dau wayarsa yyi dialing number Mujaheed, Mujaheed na driving ya daga wayar, Abba yace "Where did you drop imaan's phone?" A hankali Mujaheed yace "It's with me" Abba yace "Bring it back now" daga haka Abba ya katse wayar, inna ta xauna kan kujera tana kallon Imaan tace "Xauna mu ga ta inda wayar xai fito" Imaan da ta ki yarda ta kalli Abba ko Aunty ta karasa kusa da inna ta xauna, Inna tace "Ahmadu dai bai yi sa'an 'ya ya ba gaskiya, don Mujaheed da Isuhu sai su iya kashe mutum" Anty ta ci gaba da aikin da take yi, Inna sai girgixa kafa take bayan kusan minti goma sai ga Mujaheed ya shigo parlon, Inna tace "Huuuu an dai ji kunya, fito da wayar da ka dauke" Mujaheed dai bai ko kalleta ba ya mika ma Abba wayar, Abba ya mike ya ba inna, inna ta karbe ta mika ma imaan tace "Tashi mu je, daga yau dama duk inda kika ga Mujaheed ki canza hanya da gudu don ba mutumin kirki bane" Imaan ta mike ta bi bayan inna, inna ta bude kofa tana cewa "Sai kuma ka sace wayar Rukayya idan ta ajiye ba dai na imaan"

IMAANWhere stories live. Discover now