Part 14

115 1 0
                                    

71......







Da daddare Imaan na parlon Inna a kwance ta dalilin kiranta da Sadeeq yyi xai kawo mata magunguna ita kuma bata son fita kofar gida shi sa ma ta taho part din Inna ya sameta a nan, ko tsinke Inna bata bari a parlonta ba cikin kayan da aka kawo na Imaan gaba daya ta kai su daki, dakin ma makulli take sa masa sai in xata shiga ta bude idan ta fito kuma ta kulle ta daure makullin a ha6ar xaninta, Inna dake xaune ta gama cin abinci kenan ta daura kafa daya kan daya ta ta6e baki tace "Ni dai da ki tashi ki lallaba ki koma can bangaren ku ki jirasa, bana son wannan juye juyen da kike min kamar macijiya gaskiya, ni bana son abinda xai gigitani da daddaren nan, Bukar kuma ba kirki ne da shi ba tsaf xai iya cewa a parlona ciwon ya tashi in shiga uku" Ita dai Imaan bata kulata ba, dai dai nan aka yi sallama kofar parlon, Mikewa Inna tayi tana amsawa tace "A'a Bisimillah Bukar, sannu da xuwa" Sadeeq ya shigo parlon, inna ta kinkimo lallausan carpet dinta da ta nade saboda masu shigowa kallon lefe kar su 6ata mata ta shimfida masa, yana murmushi ya xauna ya gaisheta, ta amsa tace "Tun daxu take xaxxabi nace ta tafi gidansu iyayenta su sani ta ki, to dama wannan mutumin Mujaheed da yana nan ne yasan kan xaxxabin, to ban gansa ba kuma nasa Maimuna ta kira min shi nace ga kanwarsa ba lafiya amma shiru bai xo ba, ita kuma lkcn da ba shi da lafiya har cewa tayi a fasa kawo lefenta da kudin aure sai ya ji sauki, su Ahmadu dai ne basu yarda ba, kowa da imaninsa kawai a rabu da shi, shi ya sani...." Sadeeq dake fiddo drugs da ya kawo bai dai ce komai ba, can ya kalli Imaan da ta juya masu baya, Inna tace "Atoh, tsorona daya kada uban yace a nan xaxxabin ya tasar mata kuma ni daxun nan ta shigo min wllh" a hankali yace "How are you feeling?" Shiru Imaan tayi bata ce komai ba, Inna tace "Idonta biyu wllh" Imaan ta hade rai ta juyo sannan ta mike xaune, ledan maganin ya nuna mata yace "Ur drugs with prescription, sai ki sha yanxu" Inna ta tafi kitchen ta dauko ruwan gora da cup tace "Toh tashi ki sha" Sadeeq yace "Ni xan koma Kaka" Inna tace "A'a abinci fa? uwarta ce tayi, da ke ni dama idan ba girkinta ba bana cin na kowa sai in Amina, tuwo ne da miyar agushi yaji kayan hadi, sai kamshi yake xubawa in xubo maka?" Yana d'an murmushi yace "Naci abinci kafin in taho kaka" tace "Toh ko in juye maka ka tafi da shi?" yace "Ai kuma ni da abinci sai gobe idan Allah ya kai mu" Inna tace "Atoh, haka naga Mujaheed ma yake yi, shi in dai karfe tara yyi bai ci abinci da daddare ba to ya gwammace ya kwana haka bai ci komai ba, kaji fa abinci ma sai an masa ka'ida, Ni ko nace aikin banxa, yo ko tsakar dare cikina ya bukaci hakkinsa bana tashi in san yanda nayi na sallamesa ba? Wlh akwai hisabi mai tsanani tsakanin mutum da yan hanjinsa, in dai ka cuce su to ranan gobe kiyama abun baxai maka kyau ba, shi sa ba ruwana ko biyun dare ne naji yyi kugi xan tashi in san abun yi, abinda ga kayan shayi kaca kaca a gidan" Sadeeq ya mike yana murmushi yace "Sai da safe kaka, xa a kiyaye" tace "Toh Allah ya bada ikon kiyayewa" Yana kallon Imaan yace "Sleep tight, Allah ya kara sauki" a hankali tace "Ameen, amma ba wanda xai sani bacci coz I am having 10 o clock paper tomorrow" yace "Not at all, xa ma ki iya tashi cikin dare kiyi karatun ki" daga haka ya nufi kofa Inna tace "Toh baxa ki tashi ki daddage kiyi masa rakiya ba Imaan?" yace "A'a ta sha magani ta kwanta kaka, sae da safe" Inna tace "Atoh, Allah ya tashe mu lafiya, ka gaida iyayen naka, Allah yayi albarka" yace "Ameen kaka nagode" daga haka ya fita parlon ya rufe kofar. imaan sun fara jarabawa da sati guda aka fara shirye shiryen biki a gidan kasancewar biki biyu ne da nata sai Ya Yusuf... yau Friday Imaan na dawowa exams karfe sha daya ta tafi part din Inna, bakin tap ta sameta tana wanke gaba daya buckets dinta da iron sponge da detergent, Imaan ta shiga parlor ta xauna, Sai kusan sha biyu Inna ta shigo tana cewa "Haka kawai, naga bokitai suna son komawa kamar takashin kare, Allah ubangiji ya min tsari, na wanke su tass na shanya kayana ni dai, kuma duk Maimuna ce me min amfani da abokitai gashi sun dauko hanyar dafewa, gaskiya xan kira ubanta ya mana iyaka, idan nata xai siya mata to sai ya siya mata ta rabu da nawa..." Tana kakkabe kujerunta tace "Toh ya jarabawan yau?" Imaan tace "Alhmdllh" Inna tace "Toh Allah ya baku sa'a, sai kiyi kokarin ganin kin cinye jarabawan kin fi kowa, to kin ci abinci kuwa?" Imaan tace "Ni bana jin yunwa" Inna ta tabe baki jin yanda take amsa mata ta gama kakkabe kakkabenta ta dauko tsintsiya, Imaan na kallonta tace "Inna Yaya yana xuwa?" Inna na gyara tsintsiyar hannunta tace "Yaya? Waye kuma Yaya?" Imaan bata ce komai ba, Inna ta tabe baki ta fara sharanta tace "Wai Yaya, to ajiyar Yaya kika bani Imaan? Ina xan ga wani Yaya mutumi na gidansa, ni har na mance rabon da ya tako min nan ma, toh mutumi ya fara sanin dadin aure me xai xo ya min kuma? A'a ni kam kusan sati kenan ban gansa ba" Imaan dai sai kallonta take, Inna ta kalleta tace "Sako xaki bada a ajiye masa?" Imaan ta turo baki tace "A'a kawai na daina ganinsa ne" Inna ta tabe baki tace "Toh ba sai ki shirya ki tafi gidansa ba ko akwai wanda xai hanaki? Ni dai har abada in taka cikin gidansa tunda iyayensa ba so suke ba, to me Mujaheed xai bani wanda Allah bai ban ba? A'a ba ruwana ta kai na nake yanxu, ni ko naje gidan nasa fa ko yar kudin motar nan baya bani, kullum a gantale nake dawowa idan naje wllh, to sai kace uwata tace min je ki kya gani" Imaan tace "Toh ki kirasa" Inna ta kalleta da sauri tace "In kirasa? Ke uban me ya hanaki kiransa, gafara xai min Mujaheed din koko?" Imaan ta hade rai bata ce komai ba, Inna ta ci gaba da sharanta tace "Ni dai kar ki dameni don Allah, waye kuma Mujaheed Allah na tuba" can kuma ta mike ta dauko wayar ta mika mata tace "Toh kirasa dai mu ji" Karban wayar Imaan tayi, tayi dialing number sa ta sa handsfree ta ba Inna, har ya gama ring bai dauka ba Inna ta ajiye wayarta ta ci gaba da abinda take. Ranan lahadi warce Anty ta kira domin yi ma Imaan gyaran jiki ta iso gidan duk da bikin saura sati uku, sati ukun kuma xata yi tana gyara Imaan, kudi ba na wasa ba Aunty xata biyata, matar ta so ace Imaan ko fita baxata dinga yi ba during the period amma hakan baxai yiwu ba sbda exams da take, Tunda Umma taga sananniyar mai gyaran jikin da aka dauko hankalinta yayi mugun tashi, duk gaba daya she is soo confused, sun koma gun mutumi kamar yanda Hajiya Saude tace amma ita fa taga abu sai gaba yake ga biki saura sati uku har xa a fara gyara amarya, tsabar yanda ta sa abun a rai har wani rama tayi abincin kirki bata iya ci, hatta bacci gagaranta yake yi ynxu, ga uban kayan abinci da drinks da aka fara jibgewa a gida na bikin... Anty ce xaune parlor tare da mata mai gyaran jiki tana sake jadadda mata irin gyaran da take so tayi ma Imaan, Matar tace "Baki da matsala Hajiya, ni tsakani da Allah nake aiki na" Anty tace "Toh sai abu na biyu, a wajen kakanta xa a ke gyaran, amma fa kinsan yanda tsoffi suke sai ana yi ana hakuri da kauda kai don Allah..." Dariya matar tayi tace "Ae muna da su Hajiya wannan ba damuwa bane in sha Allahu"  Umma dake kitchen ta shirya xata fita amma ta kasa fita duk tana saurarensu, Anty tace "Toh mu je in raka ki bangaren kakar tata..." Mikewa matar tayi rike da Babban jaka, Anty ta dau mata dayan suka fita xuwa part din Inna, sai a sannan Umma ta fito tana danna wayarta, ta kai kunne, Mujaheed dake bedroom dinsa ya fito wanka yana shiryawa ya kalli wayar Safeenah dake gaban mirror yana ring, karasawa yyi ya dau wayar yana kallon screen din, har kiran ya katse kallon wayar yake ganin number Ummarsa, can ya ajiye wayar sai gashi ta sake kira, dauka yyi ya nufi kofa suka kusa cin karo da Safeenah xata shigo dakin, karbe wayar tayi a hannunsa tace "Ka gaji da kwanciyar kayi wanka kenan..." Bai tanka ta ba ya juya yana ci gaba da buttoning din shirt din jikinsa, ita kuma ta fita dakin ta koma nata don daxu da ta shigo ganin ko ya tashi ne ta bar wayar a dakinsa, ta daga kiran ta kai kunne tace "An tashi qlau Hajiya?" Umma tace "Lafiya lau, ya jikin Mujaheed?" Safeenah ta tabe baki tace "Ya warke fa kawai yana pretending ne sbda bai son ina xuwa inda yake tunda ina takurasa sai ya ci abinci ko makamancin haka, wllh har yanxu na rasa gane kan Mujaheed, gaba daya ya ki gaya min damuwarsa duk da dai da sauki yanxu, in dai ya fita aiki ne baya dawowa sai nayi bacci..." Umma tace "Ke ki rabu da shi haka nan yake ba a taba gano inda ya dosa, wani lkcn kuma tsabar miskilanci ne, ni da na haifi kayana kuma, kema ki fita harkansa kawai idan kika ga yana shan kamshi sai ki ga kun dawo dai dai..." Safeenah ta tabe baki tace "Ni ko ina xan sha masa kamshi ya hango wata a waje, gwara inyi ta lallabasa a haka...." Umma tace "Toh ni ba wannan ba, Safeenah  shirye shirye dai sai gaba yake a gidanmu don yau ma aka dauko mai gyaran jiki xata fara mata gyara..." Safeenah tace "Saura sati uku fa Hajiya, ba sai a xuba ido ba a ga ikon Allah, idan fa mutum ya fiye axar6a6i da kyar ya dinga ganin abubuwa yanda yake so, ke dai kawai ki xuba masu ido ki daina damun kan ki, auren nan ance ko an daura bai fi na minti goma ba in ma an daura kenan to me xai dameki, ni ban cika yarda da irin mutanen nan ba amma gaskiya mutumin nan da alama yana da gaskiya sosai, duka duka nawa ya amsa wajen mu..." Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ban son in sakankance ne da maganar mutumi a xo ayi abun nan Ina ji Ina gani, wllh da na shiga uku, shi sa gwara in buga nan in buga can, yanxu ma xan je gidan Hajiya Balaraba" Safeenah ta tabe baki tace "Toh ni dai sai mun yi waya xan hada ma mijina breakfast ya tashi" Bata jira cewar Umma ba ta katse wayar ta ajiye ta ja tsaki tace "Ance maki ba don abinda Mujaheed yyi min sbda yarinyar da irin rainin da take min xan bata lkcina a kan abinda ya dame ki ne, nima ta kaina nake shi sa na xage" shiru tayi tana imagining ace da gaske d'an Bulasawa ya auri Imaan, Tabb har takasu ma xata iya dinga yi ita surkar Bulasawa, kawai wataran sai a wani xo da motoci kusan biyar gidanta a sunan Imaan ce ta xo gaida Yayanta, ta sakko daga motar da gwalagwalai iri iri tana yatsine yatsine tana mata kallon banxa, tabbb, da sauri Safeenah ta kauda tunanin a ranta tana cewa Allah ya kiyaye hakan ma baxae faru ba, in sha Allahu talaka bawan Allah xa ki aura ki xo gidana in taka ki yanda nake so in walakantaki, murmushi Safeenah tayi wai ta hango imaan ta xo ce ma Mujaheed basu da abinci a gida shi kuma yace ta debo mata a nasu ta bata, Safeenah ta tabe baki tace "Ae Kyawunta ma baxai bari wannan mafarkin nawa ya xamo gaskiya ba, Allah dai yasa idan an rabata da yaron Bulasawan ba wani mai kudin xai kuma xuwa mata ba don wannan shine anyi ba ayi ba...." Safeenah ta d'an yi murmushi a ranta tace muna wargaza auren nan xa mu yi mata maganin bakin jini in sha Allahu, ita da aure sai dai taga wasu na yi, shiru tayi tana tunanin to kada kuma fa ta rasa miji wataran iyayen suce a hadata da yayanta tunda da aure tsakaninsu.... sosai gaban Safeenah ya fadi ta xauna gefen gado da sauri xuciyarta na bugawa, lkci daya ta girgixa kai tace "A'a gwara dai a rabata da d'an Bulasawan kawai, duk tsiyarta kuma baxata sake samun kamarsa ba sai dai kasa da shi" murmushi Safeenah tayi ta mike ta fita dakin dai dai fitowar Mujaheed daga bedroom dinsa, rungume sa tayi tana shigewa jikinsa tace "What should make for breakfast sweetheart?" Tabe baki yyi ya kauda kai.  Sosai Imaan tayi wani fresh tayi kyau ta dalilin gyaran da aka fara mata, har wani sheki da glowing skin dinta yake, duk ta gifta ka dama kamshin da xaka ji na musamman ne, a haka kuma take fita tayi jarabawa kullum, tun biki na saura sati biyu dama wayarsu ya ragu sosai da Sadeeq, yawanci kuma ita ke kiransa ma, shi ko sai dai ya bi miss call dinta. Yau Wednesday Imaan na dawowa daga exam bayan tayi wanka ta sauya kaya Inna ta xubo mata abinci da yaji nama ta ajiye mata a kusa da ita tace "Ni dai wai yaushe xa ku gama wannan kaddararren jarabawan ne ki nutsu waje daya a maki gyaran nan cikin kwanciyar hankali, wannan ae fitina ne ana gyara yana bin iska tunda kullum sai kin fita..."  Imaan na kallon abincin da Inna ta ajiye mata tace "Ni fa bana jin yunwa" Inna ta kalleta da sauri tace "Ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, ko kumallon kirki fa baki yi ba daxu, a haka xa a kai ki gidan Sadeeq din nan da sati biyu a rame duk k'ashi a wuya?? Ni dai ba ruwana bari Amina ta shigo tunda Aisha ta sallama mata ke gaba daya" Imaan ta tura abincin xata kwanta kan kujera a fusace Inna tace "Ni fa bana son a dameni gaskiya sai ince ki tattara kayanki ke da mata mai gyara ku koma bangaren ku yanxu nan, ya xan dinga maki magana kina walakanta ni, dama katuwar mata mai gyaran jiki ce tace ki ci abinci kafin ta dawo taje siyo wasu kayayyaki a kasuwa ta dawo, to idan ta dawo ba ki ci ba fa..." Imaan tace "Inna to ko dai yaya ba shi da lafiya ne har ynxu?" Bude baki Inna tayi tana kallonta da mamaki, can ta xauna tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe, waye kuma Yaya??" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Inna tace "Wai akwai abinda ya hada ki da Mujaheed ne bayan kasancewar Ubansa wan ubanki? Akwai wani dangantaka tsakaninku ne dama da ban sani ba? Wato kwana biyu shiru bai shigo ya takura ki ba shine duk kika damu tunda ke gantalalliya ce, toh sai ki tashi ki tafi gidansa, Toh wai ma ina ruwanki da wani yaya ke da xa ki yi aure nan da kwana sha biyar? Ko dai akwai ajiyar ki a gunsa ne bai baki ba kafin a kai ki daki in kirasa ya baki?" Imaan ta wani hade rai tace "Toh kawai daga tambaya? Naga ya dade bai xo ba kuma ba haka yake ba" Inna tace "Toh idan lalacewa yyi ya fara hakan fa?? Ko idan ya xo me xai bani banda ya tsokane ki ya cuce ki ya wuce don ma naga tunda yayi aure yyi hankali ya daina sa ki kuka, Ke dai ki dinga jin tsoron Allah kiyi ta kanki ba ruwana, to ni ko shekaranjiya na sa Ummi ta kira min shi katon ya ki dauka, wa ya sani ko fushi yake na daina xuwa gidansa, sai kace gidan aljanna Allah na tuba, ni dai ba ruwana wllh" daga haka Inna ta shige daki, imaan ta bi ta da harara ta jinginar da kanta da kujera bata ce komai ba.... Ana saura kwana 7 biki Imaan ta gama jarabawa kasancewarta science student, Maimoon da Mariya kuma nan da kwana shidda xa su gama jarabawan don art class suke, yau kusan kwana hudu basu yi waya da Sadeeq ba, bai kirata ba ita ma bata kirasa ba, tana bedroom din inna bayan la'asar hannunta rike da hisnul Muslim wayarta ya fara ring, daukar wayar tayi tana kallon mai kiranta, ganin number Sadeeq ta daga ta kai kunne tayi shiru, shirun shi ma yyi na kusan second goma sannan yace "How are you?" Murya can ciki tace "Am good" yace "Ina waje" ta kalli agogo bata dai ce komai ba, yace "Or are you busy?" Tace "Ni ba bari na ake ina fita ba..." Ya d'an yi shiru sannan yace "What did you mean?" Tace "Bana fita" yace "Ohk gida ake biyo ki da papers din ki kenan?" Turo baki tayi tace "Waye ubana da xa a biyo ni gida da papers?" Yace "What exactly are you trying to say?" Kin cewa komai tayi, Yace "Ohk then kar ki fito..." Xai katse wayar frnd dinsa Saleem dake tsaye gefensa jikin motarsa ya amshi wayar ya kai kunne yace "Haba amarcy ba dadewa fa xa kiyi ba, ki d'an fito pls, just few minutes" a hankali Imaan tace "Toh" Saleem ya katse wayar yana kallon Sadeeq yace "Amare fa lallaba su ake basa laifi Dr" Sadeeq dai bai ce komai ba yana rungume da hannunsa, Saleem yyi murmushi yace "To saki ran kafin ta fito mana" Nan ma dai Sadeeq bai tanka sa ba, Hijab Imaan ta saka sai dai ba har kasa ba, ta fito parlor ta sanar ma Inna sadeeq na kiranta a waje, Inna dake xaune parlon tare da mai mata gyaran jiki suna hira sai kallon takwarar tata take, can a hankali cikin sanyin murya tace "Ashe dama haka kike da kyau ban sani ba Imaan?" Dariya sosai mai gyaran jiki ta shiga yi tana kallon Inna dake sa ta nishadi tun xuwanta, kwata kwata bata gajiya da fadan Inna da labaranta masu kai da marasu kai, ga uwa uba tsaftarta, komai na Inna burgeta yake, Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba bata dai tanka Inna ba ta nufi kofa ta fita, Inna na kallon mai gyaran jikin tace "Allah kuwa yar nan, dubi fa yanda take walkiya da kyalli, ga kamshi kaca kaca ta ko ina a jikinta, duk inda ta gilma sai ya kamu da kamshin da take yi, ni dai xan kara maki dari biyu da tsinkin sabulu a kudin da xa su biyaki, gaskiya kin fito min da jikata, kai har dambun nama xan maki ni dai" Matar dai sai dariya take tana ma Inna godiya, Imaan na isa part dinsu ta shiga don daukan hijab mai tsayi, Ammi ta fito daga kitchen jin an bude kofa, Imaan ta gaisheta sannan ta nufi dakinta, Ammi ta bi tada ido, ba a dau lkci ba ta fito sanye da hijab har kasa, tana kallon Ammi a hankali tace "Ana kirana a waje ne..." Shiru Ammi tayi tana kallonta, hakan yasa Imaan ta sunkuyar da kanta, Ammi ta karaso kusa da ita ta sa ta xauna saman kujera ta xauna kusa da ita tace "What's wrong with you Imaan?" Imaan ta kalleta da sauri tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Noo there is something kar ki ji komai ki gaya min..." Imaan ta girgixa mata kai a hankali tace "Da gaske ba komai Ammi...." Ammi tace "Toh shikenan, but don't forget baki da wanda ya wuce ni a duniya, idan baki gaya min damuwar ki ba ban san wanda xa ki gaya ma ba" Imaan ta sunkuyar da kai tana murmushi tace "Idan akwai xan gaya maki ai Ammi" Ammi tace "Toh ki kwantar da hankalin ki and keep praying, kar ki gaji da addu'a, kuma ki dinga cin abinci sosai kin ji" murya can kasa Imaan tace "Toh nagode Ammi" Ammi tace "Ko me kike bukata ki kirani a waya ki sanar min" Imaan tace "Toh bari in je ana jirana" Ammi tace "Toh ki kame kanki" mikewa Imaan tayi ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofa. Tunda Imaan ta iso part din su Maimoon Umma dake xaune tare da Hajiya Balaraba kan fararen kujeru take kallonta ko kiftawa babu, ta sunkuyar da kai ta gaishesu a hankali Hajiya Balaraba ce kadai ta amsa a dakile, tuni kamshin da take ya daki hancinsu gaba daya, har ta fita gate basu daina kallonta ba, Da ba don Saleem da ya ki barin sa ba da tuni Sadeeq ya bar wajen ganin har bayan minti goma bata fito ba, tana fitowa sau daya ya kalleta ya ci gaba da danna wayarsa, Saleem ya mata murmushi har ta iso inda suke ta tsaya a gefe a hankali tayi masu sallama sannan ta gaishesu kanta a kasa, Saleem ya amsa yace "Hope an gama exams lfya?" Tace "Alhmdllh" Sadeeq ya maida wayarsa aljihu yana kallonta ta cikin glasses din idonsa a takaice yace "Wani shirin xa ku yi a nan gida?" Shiru tayi da farko, sai kuma ta kallesa taga wani direction yake kallo daban, tace "Nima ban sani ba" yace "Ohk then, on Thursday xa ayi dinner...." Yana magana ya bude mota ya fiddo hadadden IV mai yawa sosai ya mika mata ta risina ta amsa, shi dai bai yarda sun hada ido ba, yace "I think that's all, dama sbda IV din na xo, if there is anything I will call and let u know" daga haka ya bude driver seat ya shiga, ita dai sai kallonsa take, Saleem na mata murmushi yace "Toh mun gode amarya, ki shiga ciki xa mu koma" tayi murmushin karfin hali ta juya ta nufi gate, Saleem ya xaga ya shiga front seat, Sadeeq ya tada motar suka bar layin, suna hawa kan titi Saleem yace "Plss ka rage wnn xuciyar Sadeeq... I don't like the way u treated her gaskiya" Sadeeq dai sai driving dinsa yake bai ce masa komai ba, Saleem ya tabe baki ya fiddo wayarsa yana dannawa, Sadeeq yace "Raina min hankali take" Saleem yace "Meye abun rainin hankali" a d'an fusace Sadeeq yace "Baka ji abinda tace ba kenan, wai bata san abinda xa su yi ba a gida na biki, wato babu events da xa su yi kenan take nufi, which is a lie" Saleem ya tabe baki yace "Duk wannan xumudin da ka dinga yi kwanki kafin a saka bikin duk naga babu shi yanxu Sadeeq" Sadeeq ya rage gudun da yake yana shafa kansa a hankali bai dai ce komai ba....







IMAANWhere stories live. Discover now