Part 10

104 2 0
                                    

51....



Kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa don ba karamin tsorata tayi ba, cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba sai na baki dirty slap?? Who sent you, waye ya aike ki??" Hawaye ya cika idonta ta sunkuyar da kanta bata dai ce komai ba, saketa yyi ya jingina da bango xuciyarsa na bugawa, ta tsallake abincin da ya xube ta wuce da sauri tana goge idonta ya bi ta da kallo har sannan kirjinsa bai daina bugawa ba, hade kai yyi da bango yana Kiran Allah a ransa, ya fi minti biyu a haka sannan ya juya da kyar ya nufi bangarensu yana jin idanuwansa na juya masa. Imaan na kwance daki da yamma idonta a lumshe duk da ba bacci take ba, wayarta dake kusa da ita ya fara vibrate, bude ido tayi tana kallon wayar, tun abinda Mujaheed yyi mata daxu take daki taki fitowa duk nacin da Maryam tayi da ita ta fito, gaba daya she is moody, a hankali ta dau wayar tayi picking ganin Sadeeq ne ke kiranta, sallama yayi mata daga daya barin, murya can kasa ta amsa, yace "Are you okay dear?" Shiru ta d'an yi sai kuma tace "Bana jin dadi" yace "Subhanallah baki jin dadi kuma, kin yi stressing kan ki da yawa kenan, what's wrong? I mean me kike ji ke damun ki?" Cikin sanyin bemurya tace "Ache all  over" yace "Subhanallah, kin sha drugs din ki?" Ta gyada kai kamar yana ganinta yace "Ohk toh xan kawo maki wani yanxu sai ki sha shi da daddare, you will feel much better" tace "Toh" yace "Xan kira ki idan na iso" daga haka yyi mata sallama ta katse wayar ta ajiye ta rufe idonta. Biyar saura ya sake kiranta yana waje, Hijab ta saka har kasa, xata fito ta tuna birthday gift dinsa ta koma ta dauko flower din da cards ta saka cikin hijab ta fito, Few visitors ne a parlon nasu, ta tafi dakin Ammi ganin bata ciki ta fito, a balcony ta tadda Ammi da Mama Hansai, Ammi na kallonta tace "Ina xa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Ammi ba dadewa xan yi ba ana kirana a waje ne" Ammi na kallon hannunta dake cikin Hijab tace "Meye wannan kike boyewa a hijab?" Murmushi tayi kanta a kasa tace "Ammi ba komai bane, sako ne fa" Mama Hansai na dariya tace "Yi wucewar ki kinji" wucewa imaan tayi tana murmushi, Yana tsaye jikin motarsa idonsa sanye da glass ya sa kananun kaya, sunkuyar da kai tayi ta isa kusa da shi, da damuwa yace "Ya jikin" tana d'an murmushi tace "Da sauki" ya dauko wani leda a gaban motar ya mika mata yace "ki sha tablets daya each each kafin ki kwanta" Bata amsa ba ta fiddo hannunta dake cikin hijab ta mika masa flower din hannunta cikin sanyin murya tace "Happy birthday dear" still yyi yana kallon flower din ko kiftawa babu" lkci daya ya karba yana wara ido so happy yace "Waowww Thanks soo much baby I love it...." Ita dai murmushi kawai tayi, a hankali tace "i am happy u love it...." Ko bai fada ba she can see how happy he is, yana wara manyan idanuwansa yace "But baby how did you know I love flowers plss?" Ta langwabar da kai tace "I only guess" lumshe ido yyi murya can kasa yace "I feel like hugging you sweetheart" d'an murmushi kawai tayi ta dauke kai tace "Ni xan koma ciki, and I am sorry I won't be able to attend ur party saboda bana jin dadi" a sanyaye ta kare maganar, cike da damuwa yace "Ai na maki uxuri dear, Allah baki lafiya thanks a lot, I will give you a call later" a hankali tace "Ameen ngd" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da kallo still smiling. Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Ta Rasulu, cikin rashin jin dadi Mama Hadiza tace "Yanxu fisabilillahi kin kyauta min Inna, duk yanda na takarkare a kan an ci maki mutunci sai ki watsa min kasa a ido??" Inna tayi kasa da murya tace "Toh Hadiza shikenan ana ta bani hakuri ana hada ni da Allah sai in botsare kamar shaidaniya? Babba fa dama da hakuri aka san sa, baki ga yanda aka cika min parlon nan ba daxu ana bani hakuri har da su Audu d'an tsut, daga karshe sai kuma ga Bulasawa da kansa shi ma ya tako har parlon nan ya ce inyi hakuri, to idan dai ni ba tsohuwar banxa bace mai kunnen kashi mara jin magana Hadiza ai ya ci ace na yayyafa ma raina ruwan sanyi in hakura, kuma ni dai gaskiya Rukayya bata ta6a min irin haka ba, hau ne ya fada mata...." Ta Rasulu na nuna Inna ta kankance ido tace "Ke dai Asabe ki dinga jin tsoron Allah, nan kika maida mu mahaukata muna bambami daga karshe kika watsa mana kasa a ido wai kin hakura, Toh ai ina gida xa ki sa a kirani ki kawo min karar Rukayya, ba kuma ruwana wllh don baxan saurare ki ba, ke kuma Hadiza me xai dame ki?? Ai kadan da aikin Asabe kenan baki biyu, ni ban yi mamaki ba, ni ba dai ruwana ban ce komai ba in yi magana ta kullace ni, amma banda haka me aka yi aka yi wani shegen Bulasawa da har xai bata hakuri ta hakura? Bayan abinda tsinanniyar matar nan Rukayya ta mana, Kai Asabe Allah ya baki lafiya, ya kuma shirye ki, ni dai kin ga tafiyata nan...." Inna ta tsuke fuska tace "Toh ai ni ba gantalalliya bace da xa ayi ta ba ma hakuri in ki hakura kamar kafurar Bayan tsauni, ehe... Bulasawa kuma ni ya fi min kowaaa, yaro mai hankali da natsuwa mai magana irin ta manya, duk sai da ya fada min maganganu masu dadi da kwantar da xuciya wanda su Amadu suka kasa, toh ni ko me xance ma yaron Banda Allah ya masa albarka, ai in dai bai auri Imaan ba to sai dai in ni Asabe bana numfashi, Imaan ta sa ce in sha Allah, Bai fi min wasu 'yan uwan nawa ba ma ni Allah na tuba, Rukayya kuma ai tuni tana akurkin gidan da ta gina ma iyayenta sai kace ba ni ta ma rashin mutunci ba da xa a bar ta ta kwana gidan nan...." Ta Rasulu ta mike tace "Ni dai tunda kika kunya ta ni, kika kunyata Hadiza Allah sai ya saka mana ya bi mana hakkin mu, Rukayya kuma mu dai je xuwa muna nan dake xata dawo gidan nan...." Inna tace "Ke ni fa ban hakura da abinda Rukayya ta min balle ta dawo, ai Rukayya yar iska ce, aure ne dai nace aje a daura kada 'ya yana su ji kunya" Ta Rasulu tace "Oho dai ni kin ga tafiyata sai ki saka Bukar gaba ya bada kudin nan na laluran Imaan a san abun yi...." Daga haka ta fice daga parlon, Inna tace "Toh Allah bar xumunci ta Rasulu, Allah ji kan mai salati da jikan shehu, Allah ya saka da alkhairi ai ni kin gama min komai a duniya wllh kin fi min kowa ma, Allah ya bar mu tare sai kuma kin dawo bikin Imaan da Maimoon in sha Allah, Kai ae xan taho har gida maki ban gajiya, Bari dai 'yan kauyen nan su koma kauyukansu xa ki gan ni" Mikewa Mama Hadiza tayi ta fice daga parlon rai ba dadi, Inna ta bi ta da kallon gefen ido tace "Toh meye kuma axumi uku da xa ki yi, sai kace warce bata axumin Ramadan, Ni dai ba ruwana dama ban aike ki kiyi ta rantse rantse ba...." A ranan Mama Hadiza bata kwana gidan ba ta tafi gidan wata yayar Mai gidanta dake nan garin kadunan. Imaan na parlon Inna bayan isha tare da Maryam suna cin abinci aka bude kofa, kallon kofar suka yi Mujaheed ya shigo da sallama murya can kasa, wani daddadan kamshi ya gauraye parlon, yayi wani kyau na daban cikin milk shaddar jikinsa dake ta talli, Maryam na murmushi tace "Groom dama har yanxu baka tafi ba?" shi dai bai ce mata komai ba ya xauna, Imaan dai bata kalli inda yake ba tun bayan da suka hada ido shigowarsa, ta dinga cin abincinta a hankali, daga cikin dakin Inna tace "Mujaheed ne?" Maryam tace "Ehh" da sauri Inna ta fito ta marairaice tace "Tun daxu nake cigiyar ka Mujaheed, nace to ko har ka tafi wajen amaryar ne ba sallama ni patuu...." Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yanxu xan tafi" Xaunawa Inna tayi ta fashe da kuka a hankali tace "Shikenan yanxu Mujaheed sai dai ka xo ka gaishe mu ka tafi?? Shikenan ba kai ba kwana cikin gidan nan yanxu balle ka xo da sassafe ka gaisheni, wa xai dinga shigo min nan muna hira? Shikenan tafiya xaka yi ka bar ni yanxu, dama ba kowa gare ni ba sai Allah sai kai, kaine me debe min kewo gashi yanxu kayi aure xaka tafi gidanka ka barni ni kadai raina..." Mujaheed bai san lkcn da yyi murmushi ba sai dai bai ce komai ba yana danna wayarsa, Inna na share hawayenta cikin rawar murya tace "Rayuwa kenan, lallai sabo turken wawa, Allah ubangiji ya ba ku xaman lafiya da matar, in sha Allah xuwa nan da kwana biyu imaan xata rakoni don baxan gane gidan ba in xo ganin daki in sa albarka kuma in maku nasiha da amaryar, Allah ya sanya alkhairi... Ni dai baka taba min komai ba Allah maka albarka" Mujaheed na murmushi a hankali yace "Ameen" Mikewa yayi yace "Toh sai da safe" Inna ta kara rushewa da kuka har da rike kai, Maryam ta kasa ci gaba da danne dariyar da ke cinta, Imaan kam kin dago kanta tayi tana juya shinkafar gabanta, Cikin kuka sosai Inna tace "Shikenan kuma, wayyo rayuwa kenan...." Maryam na murmushi tace "Allah ya bada xaman lafiya Ya M.A, sai mun xo ganin dakin Aunty amarya" Mujaheed ya d'an yi murmushin karfin hali ya gyada mata kai ya juya ya nufi kofa, Inna na kallon Imaan da ta sunkuyar da kai tace "Toh ke baxa ki ma yayan naki fatan xaman lafiya da matarsa ba Imaan" Shi dai Mujaheed bai tsaya ba har ya fita, bin sa da kallo imaan tayi sai kuma ta mike ta bi bayansa da sauri, Maryam ta xaro ido tana kallon Inna tace "Wai kuka fa take yi..." Inna ta kara rushewa da kuka tace "Ka ji ki da wata magana, baxa ta yi kuka ba?? ke kinsan wahalan da Mujaheed yyi da ita tun tana tsumma, ke kinsan irin fadi tashin da yayi a kanta tana karama, to ko ubanta bai yi wahalar da Mujaheed yyi a kanta ba, kullum a makale da shi xa ki ganta duk ta takura bawan Allahn duk inda xa shi tana hannunsa, tayi ta basa wahala, har goyata ya sha yi, ta xo ta fara ciwace ciwacen da ba a san kansa ba nan ma babu irin wahalan da bai yi da ita na ganin ya nema mata lafiya ba, ai shakuwar dake tsakaninsu ko d'a da uwa sai haka, kuma kice baxata yi kuka ba yau xa su rabu na har abada" tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta xamo daga kan kujera tayi xaman dirshan a kasa, Maryam dai sai dariya take kasa kasa. Imaan na fita parlon Inna taga har yayi nisa, ta bi bayansa da sauri tace "Yaya" tsayawa yayi ya juya yana kallonta, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta nufesa da gudu ta rungume sa cikin rawar murya tace "Xan yi missing din ka Yaya" kasa cewa komai yayi, lkci daya idonsa ya canxa launi, rungume ta yyi shi ma yyi ya lumshe ido, kuka ta dinga yi a kirjinsa, cike da karfin hali yace "Ae xa ki dinga xuwa gidana in sha Allah..." Ta gyada masa kai kawai hawaye na sauka idonta, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri da abinda nayi daxu, ban san it's wrong ba I wouldn't have done that, kayi hakuri plss...." A hankali yace "Na hakura" gently ya janyeta jikinsa ganin hawaye take har sannan yace "Toh ya isa haka mu je ki rakani gun mota" Bata iya ta ce komai ba ya kama hannunta suka nufi gate. Tafiya kawai suke kamar ba su son tafiyar har suka fita gate din gidan, suna isa motarsa ya juya yana kallonta har idanuwanta sun yi jajir, sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Sai da safe, I am wishing you a happy married life...." Yayi murmushin karfin hali yace "Thanks imaan" Juyawa tayi ta fara tafiya yace "Imaan" ta tsaya sannan ta juyo jin bai ce komai ba ta dawo inda yake tana kallonsa, yace "Shiga mu je xan siyo ma Inna abu ki kawo mata ynxu" a hankali tace "Toh" sannan ta xaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga driver seat ya tada motar, the journey was silent har suka iso gun masu gashin kaji, yayi parking ya kashe motar, ya sauka, ba a dau lkci sosai ba ya dawo rike da leda uku na kaji da fresh milk, ya bude back seat ya ajiye leda guda sannan ya bude side dinta ya mika mata leda biyu ta amsa ya xaga ya shiga driver seat, gida ya koma bayan yyi parking ya juya yana kallonta yace "Sai da safe" ta sauke idonta kasa tace "Allah ya kai mu..." Yace "Ameen, ki dau daya sai ki kai ma Inna daya" D'an murmushi tayi ta bude motar ta fita, ta nufi gate ya bi ta da kallo har ta shiga sannan yayi reverse ya bar layin. Washegari asabar tun da wayewar gari Ammi da Aunty, Mama Hansai da matan kawu Bala suka dinga aiki a gidan trying to make sure everywhere was neat, masu kujeru dama su ma sun xo sun dau kayansu, su Maimoon, Ummi da Maryam kadai ke taya su aikin, Imaan kuwa na kwance dakinta wai kai na ciwo, Rahma dama tare da ita Umma ta bar gidan da yammacin jiya.... Bayan azahar Imaan na part din Inna tare da Maryam, Inna na kan darduma tana bada labarin nan dai na irin yanda aka haifi Mujaheed tana tsaye bakin kofar asibiti tun safe har dare, wahalan da tayi da shi tun yana tsumma, yanda ya girma a wajenta da fadan da yasa ta dinga yi da jama'ah a anguwa, har lkcn da ya tafi kasar waje karatu.... Imaan dai na kwance sai game take a wayarta tana tabe baki don ita dai har ta haddace labarin nan layi layi, Maryam sai dariya take ita da ba a ta6a ba ma labarin ba, Inna na matsar kwalla tace "Har xuwa jiya da aka daura masa aure, Allah sarki Mujaheed dina" Dariya kawai Maryam take har da kwanciya, Inna dai sai matsar kwalla take tace "Duk cikin 'ya yan Ahmadu babu ya shi, gashi duk ya fi su kyau wllh, ga tsafta ga mutunta na gaba da shi, sam Mujaheed bai san wani abu wai rashin kunya ba, bai taba mayar min da magana ba, wllh jiya ban yi baccin kirki ba da tunaninsa na kwana..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai, sai a sannan Imaan tayi murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Inna tace "Da dakunan bangaren nan nawa sun kai uku sai in ce su dawo nan da matar kawai ni dai in dinga ganin sa kullum" Maryam dai sai dariya take, Imaan ta mike ta wuce daki ta dalilin kiranta da ake a waya, Daga kiran tayi ta xauna gefen gado ta kai kunne hade da yin sallama, ya amsa yace "How are you dear?" Tace "Alhmdllh" yace "Hope kin ji sauki sosai" tana murmushi tace "Sure, sosai" yace "Ohk to ki dan fito ki amshi sako" ta xaro ido tace "Na me?" A hankali yace "C'mon dear" tana murmushi tace "Toh bari in fito" daga haka ta katse wayar ta fito parlor tana kallon Maryam tace "Mu je ki rakani" Inna na goge hawayen idonta tace "Ina??" Imaan ta turo baki tace "Ae yanxu xa mu dawo" Inna ta marairaice tace "Tou ni dai kar ku dade, mai tayani xaman gashi yayi aure ya tafi..." Dariya imaan tayi ta fita Maryam ta bi bayanta, har suka isa gate Maryam tambayarta inda xa su take yi amma ta ki gaya mata, suna fita gate din Maryam tayi shiru ganin Sadeeq tsaye kusa da motarsa, murmushi yayi ganinsu, Maryam tace "Hi...." Yace "Hello Maryam" tana murmushi tace "Happy Belated birthday Sadeeq" yace "Thanks much... Hope an gama biki lafiya?" Tace "alhmdllh" yace "Maa Sha Allah, Allah ya basu xaman lafiya" Maryam tace "Ameen" kallon Imaan da ta jingina da motar ta rungume hannu yayi a hankali yace "Hello princess..." Ta d'an yi murmushi tace "Ya gida" yace "Alhmdllh, ya Kaka?" Imaan ta langwabar da kai tace "tana ciki tana ta missing ya Mujaheed" Yace "Allah sarki, ta kwantar da hankalinta after a month sai ta koma gidan gaba daya koh" Yar dariya kawai imaan tayi tace "Gaskiya ne" yyi murmushi ya bude back seat ya fiddo da wani kwali dake a rufe amma ko bai fadi meye a ciki ba kowa ya sani, yana kallonta yace "Here..." Ta xaro ido tace "Haba wannan ai yayi yawa" yace "Ni ma sun min yawa, take plss baby" Imaan tayi murmushi ta d'an risina ta amsa tace "Toh Allah saka da alkhairi" hararanta yyi tayi dariya bata ce komai ba, wani box mai kyau ya fiddo ya mika mata ta make kafada tace "Bana so" hade rai yayi ya kalli Maryam dake murmushi yace "Kin ganta koh?" Maryam tayi dariya ta mika masa hannunta tace "Bani in rike mata" Mika ma Maryam box din yyi, Maryam tace "Allah ya saka da alkhairi" Yana murmushi yace "And ban mance promise da na maki ba, kin bar min xabi or you want anything?" Yar dariya Maryam tayi tace "Ehh na bar maka" yace "Toh shikenan, thank you" Kallon imaan yayi yace "Dear, we will talk later ki gaida kaka" Imaan tace "Toh xata ji nagode" Sallama yayi ma Maryam ma suka nufi gate, ya bude maxaunin driver ya shiga ya tada motar, suna shiga gida Maryam ta kashe ma imaan ido tace "Yau xa mu ci cake mu yi dam, amma me xa ki ce ma Ammi?" Imaan ta xaro ido tace "Part din Inna xan kai ai" Maryam tace "That will save u long explanation" Washegari Sunday tun da sassafe Inna ta gama shiryawa wai xa su gidan Mujaheed da Imaan, Daddy dake parlor xaune yana kallon news yace "Toh ai kila ma basu tashi ba da sassafe xa ki je masu Inna" Inna ta xaro ido tace "Sai kace rubabbu Bukar kace min basu tashi ba, Toh ni dai gaskiya na shirya kuma yanxu xan tafi ina imaan din?" Daddy yace "Bata tashi ba" Inna ta xauna saman kujera tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni.... baccin safe ko baccin asara ni Asabe, karfe takwas ace mutum mai rai bai tashi yyi wanka ya kintsa ya karya ya gyara gidansa ba? Kuma tun jiya nace mata ta shirya da safe xa mu tafi tare tunda wannan yarinya Maryam dangin ubanta sun xo sun tafi da ita jiya da magariba... Kai ku dai baku da tsari gaskiya... Meye kuma baccin safe??" Shi dai Daddy bai ce komai ba, Ammi ta fito daga kitchen ta gaida Inna sannan ta tafi dakin Imaan ta tasheta...  Inna na ta xaune parlor ta tsuke fuska har imaan ta fito bayan kusan minti talatin cikin atamfa riga da skirt na biki da aka masu bata sa ba, sosai kayan suka amsheta, Inna tace "Ki dauko mayafi mu tafi idan munje can kya karya gaskiya...." Ammi da Daddy suka kalleta, can Ammi tace "A'a inna da dai ta karya ai bata da 6ata lkci wajen cin abinci, ta je gidan mutane da sassafe...." A fusace Inna tace "Ke dai Aisha ki daina haka, ki dinga jin tsoron Allah, Gidan Mujaheed din ne gidan mutane idan ba walakanci ba, gidan Mujaheed ne fa, ni dai ku dinga tsoron Allah sai kace wanda xata gidan 6are? Ke dauko hijabinki mu tafi, shi gidan yayan nata xaki ce ma gidan mutane saboda baki da mutunci..." Tana fadin haka ta nufi kofa a fusace, Daddy ya tabe baki bai dai ce komai ba, Imaan ta sa hijab ta dauko takalminta da wayarta tana kallon parent din nata a hankali tace "Sai mun dawo" Daddy kadai ne yace "Allah ya kiyaye" Ammi kam bata ce komai ba sai aikin gabanta take.



IMAANWhere stories live. Discover now