Part 17

136 3 0
                                    

86.....





Farida na murmushi tana kallon Mujaheed tace "Ina yini Dr?" Mujaheed ya mayar mata murmushin yace "Lafiya lau Farida, kwana da yawa?" Tace "Alhmdllh ya aiki" yace "Lafiya lau, dama Zaria kike?" Tace "Ehh a nan nake" Ya gyada kai yace "Maa sha Allah, toh ya mai gidan?" Tace "Yana lafiya lau, tare muke yana waje" Mujaheed yace "Toh maa sha Allah" Imaan dai sai kirkiran murmushi take tana kallon Faridar, Farida tace "Yaushe kika ce xa ki koma kaduna?" Imaan ta wara ido tace "Nan da sati daya idan Allah ya yarda" Farida tace "Amma xa ki xo gidana ai koh?" Imaan tace "Ehh xan ce Yaya ya kawo ni, ki ba mu address" Farida na murmushi tace "Toh bani number wayar ki" Imaan tace "Na bar sa a gida, bari ki bani naki inyi saving a wayar Yaya" daga haka ta karbe wayar hannun Mujaheed ta mika mata, Farida ta amsa ta sa number ta sannan ta mika ma Imaan, Imaan ta amsa tayi saving number da Aunty Farida sannan tace "Nagode Aunty sai kin ganni soon" Farida na murmushi tace "Toh nagode Imaan" daga haka tayi mata sallama, tayi ma Mujaheed ma sallama sannan ta bar wajen, Imaan ta ci gaba da daukan turarrukan da take so, Mujaheed na bin ta da ido har ta juyo, suna hada ido ta turo baki tayi gaba ta bar sa a wajen, murmushi yyi ya bi bayanta, suna isa counter ya biya kudin abubuwan da suka siya gaba daya aka kai masu mota, har suka isa gida babu wanda yace komai cikin motar, Yyi parking yana kallonta yace "Ke baki ji kunya ba da kika ce mata wajen matata kika xo?" ko kallonsa Imaan bata yi ba ta dau ledan turarruka da body cream sai toothbrush da toothpaste dinta xata fita motar yace "Xa ki san hutu kika xo yi gidana" ita dai bata tsaya ta sauraresa ba ta wuce ciki, ya fita motar ya tafi ya kulle gate ya shiga cikin gidan, direct sama Imaan ta wuce ta tadda Safeenah tsaye corridor idonta yyi jajir sbda kuka, da alama dai jiran haurowanta sama take, tun da suka hada ido Imaan ta dauke kai fuska daure, Safeenah na kallonta da kyau tace "Mijina kika yadda aka aura maki dai koh???" Imaan ta juya tana kallonta tace "Mijin mu dai malama...." Tana fadin haka tayi maxa ta shige dakin ta sa makulli, xuciyar Safeenah ya dinga tafarfasa tana tunanin me xata ma Imaan taji sauki, wani murmushin takaici tayi ta juya ta koma ciki, Mujaheed na shiga parlor ya fiddo wayarsa dake ring, ya d'an yi jim yana kallon Screen din don number Daddy ne, xaunawa yyi saman kujera sannan ya daga ya kai kunne murya can kasa yyi sallama, Daddy amsa daga daya bangaren yace "Ya ku ke Muhd?" Mujaheed yace "Alhmdllh Abba, Ina yini?" Daddy yace "Lafiya lau, su Hadiza xa su kai ma Imaan kaya can gidan naka, how about the key to the house?" Mujaheed yace "In sha Allah xan kawo makullin Abba" Daddy yace "Alright, Hadiza tace baka daukan kiranta why?" mujaheed yyi murmushi sai dai bai ce komai ba, Daddy yace "Kar ka damu ka dauka kaji me xata ce maka, may be Sunday ma su je tare da Inna" Mujaheed yace "Toh Allah ya kai mu, nagode" Daddy yace "Ba matsala dai koh?" Mujaheed yace "In sha Allah" Daddy yace "If there is any you let me know, amma kasan Ummar ka an kwantar da ita asibiti kuwa?" Mujaheed yyi shiru da farko, sai kuma yace "Not at all Abba" Daddy yace "Ohk, Alhmdllh da sauki sosai, later xa a sallamosu" Mujaheed yace "Toh Allah ya sauwake, nagode Abba" Daddy yace "Madallah" daga haka ya katse wayar, mujaheed yyi dialing number Umma, bayan wani lkci ta dauka, a hankali ya gaisheta ta amsa, yace "Ashe baki ji dadi ba Umma?" A takaice tace "Wannan ba matsalar ka bace Mujaheed, kuma shirun da kaji na maka ba yana nufin na hakura da aurenka da tsinanniyar sauran ciwon nan bane, in sha Allahu ina kara jin sauki xan taho zariar ayi ta ta kare duk uban da xai faru sai dai ya faru amma wllh baxa kayi aure da yar Aisha ba in dai ina numfashi a duniya, kai koma bbu raina baxa ka yi ba wllh, don ma kaji da kyau, kwata kwata ban amince ka hada daki da ita ba...." Tana gama fadin haka ta katse wayar kitt, Mujaheed ya fi minti goma xaune kansa a jingine da kujera ya lumshe ido, a hankali ya mike daga karshe ya wuce sama, dakin Safeenah ya shiga, ya sameta tana xuge jaka bayan ta ciro Hijab, ko kallonsa bata yi ba ta saka hijab din, ta daga trolley dinta tana ja ta nufi kofa, yace "Ina xa ki" ganin bata da niyyar tsayawa balle ta basa amsa ya fixgota, ta fashe da matsanancin kuka kamar jira take tace "Let me Mujaheed, gidanmu xan wuce don wllh baxan xauna da yarinyar nan ba, I can't stay under the same roof with her, na tsaneta, na tsaneta...." Katse ta yyi yace "Kin tsane ni kenan, good and fine, you dare cross this house da sunan wucewa gidanku to a bakin auren ki wllh, kin ji na rantse" daga haka ya saketa ya fice daga dakin, ta bi sa da kallo baki bude, lkci daya ta xube kasa ta dinga kuka kamar ranta xai fita. Bayan Magrib da takeaways din abinci Mujaheed ya shigo gidan, ko kadan bai yarda damuwar da ke tattare da shi ya bayyana fuskarsa ba, sama ya wuce ya sa makulli ya bude kofar dakin da Imaan take, ya sameta saman darduma ta idar da sllh, ya ajiye mata leda daya yace "Daxu baki sha drugs din ki ba why?" Shiru tayi masa, yace "Imaan" ta dauke kai tace "Am not sick" ya fi second goma yana kallonta sannan ya juya ya fita, mikewa tayi da sauri ta nufi kofarta ta kasa kunne, ta ji ya bude kofar dakin Safeenah ya shiga, tabe baki tayi ta koma ta xauna gefen gado fuska daure. Xaune ya samu Safeenah kasan dakin ta jinginar da kanta da gado ga wayarta a gefenta, kana ganinta kasan ta gaji da kuka, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya xauna gefen gadon yace "Kin yi sllh?" Bata ko kallesa ba balle ta amsa, yace "Let talk Safeenah...." Still bata ce komai ba wasu hawayen na xubo mata, yayi kasa da murya yace "Yanxu ya kike son ayi Safeenah?" Ta daga kai tana kallonsa cikin rawar murya tace "Am very serious Mujaheed baxan iya xama da yarinyar nan ba a gidan nan" Ya d'an yi shiru sannan yace "Mind u, sunanta Imaan ba yarinya ba" A mugun fusace ta mike tace "What ever" ya dauke kansa yace "Idan baxa ki iya xama da imaan ba baxa ki iya xama da ni ba kenan ae" Wani kuka ta sakar masa tana kallonsa, ya mike ya isa gabanta ya kamo hannunta a hankali yace "I have decided in raba maku gida, ke sai ki xauna nan, ita kuma....." Ta wani xaro ido da karfi tace "Ka raba mana gida?? Ka raba mana gidan don ka ji dadin cutata, to wllh baxai yiwu ba" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yace "To baxan raba ba, don kada in cuce ki, amma Ina son don Allah ba don ni ba ki kwantar da hankalin ki, mu xauna lfya gaba daya, I will neva give imaan space din raina ki... Plss Safeenah kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, wannan kaddaranmu ne gaba daya, bana son kina kukan nan don I am feeling guilt inside me, gaba daya we never saw this coming, ain't you proud being my first? Kowa xata shigo gidan nan fa a bayan ki take kin sani, so why disturb ur self, kuma duk yanda kika ce ayi haka xa ayi, don haka kiyi hakuri wife...." Rungumesa tayi tana kuka sosai tace "Wllh kishin sharing dinka da wata mace nake Mujaheed, ji nake kamar xuciyata xata fashe saboda kishi" ya rufe bakinta yace "Aa baxa ki yi sharing dina ba..." Da haka dai Mujaheed ya dinga lallaba Safeenah har ta d'an hakura ta ci abincin da ya shigo mata da shi, jin lkcn isha yyi ya mike ya fita dakin xuwa masallaci, for once xae huta da koke kokenta ko hankalinsa xae kwanta ya samu relieve, he hate it when a lady cries..... Yana dawowa masallaci ya sameta parlor tayi jigum, shi dai ya san yana tausayinta sosai, kuma babu abinda ya fi unexpected kishiya ciwo, kishiyar kuma warce tun asali basa shiri, ya karasa parlon ya xauna saman kujera kusa da ita yace "Kin yi sllhn" shiru tayi bata ce komai ba fuska bbu walwala, ya kalli movie din da ake a tv ya dau remote yace "Bari in kai maki wannan series din naki da kike kallo kullum...." Daga haka ya canxa tashar ya jawota jikinsa a hankali, wani sabon hawaye ne ya fara sauka idonta, yace "I don't like this tears plss Safeenah, yanxu baxa ki hakura ba for the sake of the love you are having for me??" Cikin rawar murya tace "Ae nace maka na hakura" yyi pecking goshinta yace "Toh kar ki sake kukan nan" daga masa kai kawai tayi, tayi lamo jikinsa, suna ta xaune a haka har kusan karfe goma, jin footstep a stairs Mujaheed ya daga kai da sauri suka yi ido hudu da Imaan, dauke kai Imaan tayi, Safeenah na jin tafiyarta ta kara shige masa, Imaan bata sake kallonsu ba ta wuce kitchen rike da takeaway din da ya kai mata daki, tana ajiye ledan hannunta ta jingina da cabinet din kitchen din xuciyarta na bugawa, tafi minti biyar sannan ta fito ta wuce sama da sauri ba tare da ta yadda ta sake kallonsu ba, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido... Sha daya saura Mujaheed ya tafi sama tare da Safeenah bayan an gama series din, ya bude mata kofar dakinta yana kallonta yace "Good night" shiga dakin tayi bata tanka sa ba ta nufi kan gado tayi rub da ciki, ya bi ta da kallo sannan ya rufe kofar a hankali, Safeenah ta sulalo daga saman gadon tana kuka kamar ranta xai fita, wato a dakin Imaan dai xai kwana kenan yau, tunanin hakan yasa taji kamar ta kurma ihu ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciya. Mujaheed ya bude dakinsa yana kallon ciki, ganin Imaan ta kashe wutan dakin ya luluba switch din ya kunna, kwance ya ganta ta rufe har kanta da bargo, ya rufe kofar dakin ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito ya saka pyjamas dinsa sannan ya kashe wutan dakin ya karasa kan gado ya cire blanket din jikinta murya can kasa yace "Did you perform ablution before lying down?" Duk da imaan na jinsa taki cewa komai idonta a rufe, ya kai hannu fuskarta ta mike a fusace tace "Meye haka na fara bacci xaka shigo min daki ka tasheni Yaya?" Ya d'an shafa kai yace "Dama shigowa nayi in ce maki sai da safe, and to make sure kin sha drugs din ki" tana kallonsa da idanuwanta da suka yo waje tace "Ina xaka?" Yace "Wajen matata da kika xo hutu wajenta mana kanwata....." Bai jira cewarta ba ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo kamar idanuwanta xa su yi magana, ko kiftawa babu har ya fita dakin ya kulle kofar a hankali not making any sound, Imaan ta cire bargon jikinta ta sauko daga kan gadon da sauri....







IMAANWhere stories live. Discover now