Part 20

183 1 0
                                    

101.....







Cikin rauni Safeenah tace "Haba Mujaheed, why don't you want to listen to me? Why ain't you picking my call bayan kuma kace xaka kira baka kira ba, you don't know why I am....." Imaan dake sauraronta ta katse tace "Ke dakata... What business do you have with my husband again?" Shiru Safeenah tayi jin muryarta, a mugun fusace tace "Uban me yasa xa ki daga wayata, ke na kira da xa ki daga min wayar mijina?" Imaan tayi wani dariya tace "Ehh lallai yanxu na sake confirming cewar ke babbar mahaukaciya ce, kuma kinyi mugun nisa a hauka, shi Mujaheed din ne mijin ki??" Dariya Imaan ta kara yi sannan tace "Toh bari ki ji in gaya maki, ko a mafarki da kyar ki ga Mujaheed a matsayin mijin ki, Mujaheed yyi maki nisa sosai, sai dai ki ajiye a tarihi kin ta6a auren Mujaheed, and let me drop u this last warning, keep from my husband Safeenah kike ko wa?? Wllh ki fita hanyar mijina, even by mistake kada ki sake kiransa don bashi da wani alaka da gantalalla mai tunanin dabbobi irin ki, tun ban nuna maki wacece ni ba maza maza ki goge number mijina daga shegen wayar, wahalalliya kawai mara xuciya, dama can mijin aro kika aura sai a ci gaba da zawarci kuma...." Safeenah bata yadda hawayen da ke sakko mata ya hanata fashewa da dariya ba tace "Ai kuwa ni ke da alaka da mujaheed fiye da kowa... don kuwa a yanxu haka ina dauke da cikin d'an sa ko yar sa, kin gane abinda nake nufi or you need more elaboration?" Imaan da taji wani diff ta bude ido sosai jin abinda tace, shock da taji bai hanata cewa "Ki nemo uban cikinbki amma ba mijina ba, karya kike wllh banxa kawai jahila, ke da Mujaheed bari in sake gaya maki wllh sai dai hange, shi ma daga nesa nesa, Allah ubangiji ya raba sa hada xuri'a da watsatsun tambadaddun family irin naku, duk sharrin ku da kulle kullen ku kuma a kan ku xai kare, xan ga kuma ta inda xa ki sake kiran mijina jaka kawai mahaukaciya" daga haka Imaan ta katse kiran ta danna mata block ta kunna data ta hau WhatsApp can ma ta danna mata block sannan ta goge lambarta gaba daya a wayar tana huci, xata ajiye wayar ta ji muryar Mujaheed a bayanta yace "Toh sannu! give me my phone" ta bude ido sosai sai dai bata juyo ba, yace "I said give me my phone Imaan" lkci daya ta juyo fuska a murtuke tana kallonsa tace "Baxan bayar ba, or do you have any business with the useless lady da xata dinga kiran ka a waya kana biye mata, har ta cancanci ka sake daga kiranta bayan abinda tayi ma mahaifiyar ka?? Ko har ka mance ne? Or is it because you didn't watch the scene? To ba ruwana wllh baxan yadda ba, kuma xan gaya ka da Abba...." karasawa yyi xai dau wayarsa ta dauke a fusace ta fice daga dakin kamar xata tashi sama ya bi ta da kallo, Imaan na komawa dakinta ta ji wani takaicin da bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, ta rufe fuskarta da pillow, Lkci daya tayi tsit ta daure fuska jin budewar kofa, muryarsa taji yace "But did you know u just shouted at me Imaan?" Banxa tayi masa bata dago ba, ya karasa kan gadon yace "Imaan" tashi tayi a fusace xata bar wajen ya fixgota, ta fara buge hannunsa tace "Ni ka kyaleni, leave me alone" ya matse ta jikinsa yace "Listen to me now, bana son kina min magana haka, you don't know why I answered her call and I don't think you have the right to call her, sure Safeenah raised her hands on my mum amma na tabbatar wannan kuskure ne kin kuma san irin xuciya ta Imaan, i don't keep anybody in mind..." Katse sa imaan tayi tace "Ehh nasan kalan xuciyar ka amma ban san kalan yanda ka ba ma addinin ka muhimmanci ba, ban san irin fahimtar da ka ma addinin ka ba, ban san ko kasan illar tarayyar ka da mahaukaciyar ba tunda dama ita nasan jahila ce ba sani tayi ba" yyi gripping dinta da karfi yace "Ke xaki koyar da ni addini na? Do you have to? Are you thinking kin fini sanin addini ne? Safeenah is carrying my child so I have to listen to her no matter what, it's my responsibility or ain't you aware of that religious lady?" kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa ko kiftawa babu, ya saketa yana kallon wani direction din, can ya juyo ya jawota xata kwace kanta ya kankameta giving her a romantic kiss all over her neck, wasu hawaye suka dinga sakko mata tana son kwacewa amma ba rikon wasa yyi mata ba, murya can kasa yace "I have to listen to her for the Kamar daxu hot romance ya shiga mata amma wannan karan she didn't even respond, bata kuma sake jiki ba, har lkcn kuma hawaye take har da shessheka, hakan yasa ya kyaleta yyi kwanciyarsa ya juya mata baya, tun bayan aurenta da Mujaheed yau shine karo na biyu da Sadeeq ya fado mata, tasan Sadeeq baxai ta6a mata haka ba, he will never, dama kuma Mujaheed ai bai ce yana sonta ba kawai aura masa ita aka yi, dole ya nuna mata muhimmanci Safeenah gareta, tunanin hakan yasa ta fashe da kuka sosai shi dai bai ce mata komai ba. Daren ranan gaba daya Imaan ta kasa bacci, karfe biyu saura ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta fara sllh, sai uku saura taji bacci ya fara damunta tayi kwanciyarta nan saman darduman, haka yasa Mujaheed ya mike ya kashe Ac dake aiki a dakin ya koma yyi kwanciyarsa, daga nan kuma bacci ya dauketa. Da asuba bude kofar dakin da yyi ya farkar da ita, tana ji ya koma dakinsa bayan wani lkci ya fito ya wuce masallaci. ko da ya dawo sllh ya tadda ta tana yi, ya xauna gefen gado har ta idar, ta mike ta dauka qur'ani ta koma kan darduman ta xauna, duk yana bin ta da kallo ta gefen ido, ta fara karatun ta, bayan wani lkci ya mike ya fice daga dakin. Sai da gari ya fara washewa Imaan ta mike ta ajiye qur'ani ta dauke darduma ta fita dakin a hankali, bude kofar parlonsa tayi making sure bata yi making sound ba ta karasa kofar dakinsa da bai rufe ba gaba daya ta tsaya, waya ta ji yana yi calmly, sosai gabanta ya fadi tana sauraren abinda yake cewa, "What did you mean Safeenah, sure i will take care of you, I will take care of my child u are carrying, after that ba wani abu kuma..." Abinda Imaan taji ya fada kenan, da mamaki ta ji yace "Auren kisan wuta kuma?? Did you even know what you are saying?" Imaan taji gabanta yyi mugun faduwa taji ta ma kasa tsayuwa bakin kofar, mikewa mujaheed yyi yana kallon kofar jin motsi da sauri ta matsa ta jingina da bango, ya karaso bakin kofar ya bude suka yi ido hudu ta wani daure fuska, yace "We will talk later" daga haka ya katse wayar yana kallonta yace "Why do you derive joy intruding in my affairs imaan? gari ya waye common ki bude baki ki gaida mijin ki baki iya ba amma kin iya kishi da saka masa ido, do you have any problem? Meye amfanin kishin naki?" Kallonsa kawai Imaan take bbu ko kiftawa, yace "Bana son kina saka min ido a abinda nake yi, and I don't think it's necessary ki dinga shigo min nan da safe ba gaisheni kika xo yi ba..." juyawa imaan tayi ta nufi kofa ta fice daga parlon ta wuce dakinta, ita kanta tayi mugun mamakin yanda ta dake xuciyarta, ta cire kayan jikinta ta tafi bathroom kawai ta wanke baki ta hada ruwan wanka tayi ta daura towel ta wanke bandakin ta fito, sai bayan da ta gama shiryawa ta feshe jikinta da turare sannan ta gyara dakinta ta kunna turaren wuta. Tana goge goge a parlor Mujaheed ya sakko cikin shiri sai xuba kamshi yake, yana kallonta yace "What will you take for breakfast Imaan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "I will sort that out" kofa ya nufa ta bi sa da kallon gefen ido har ya fita gidan ta ji fitar motarsa gaba daya. Sai a sannan wasu hawaye suka dinga sakko mata ta dinga jin wani xafi a ranta, tayi kukanta mai isarta ta gama goge gogen da take ta wuce sama ta kwanta, har sha daya bata fito daki ba balle ta nemi abinda xata ci gaba daya taji yunwar ma bata ji. Da rana tana kitchen ta na dafa indomie ta ji shigowar motarsa gidan, tana ji ya shigo parlor sannan ya karaso kitchen jin kamshin dahuwar da take yi, yana tsaye bakin kofar yana kallonta daga sama har kasa don skirt ne karami jikinta sai riga yace "Kin yi breakfast din?" Tace "Nayi" yace "Ohk ga lunch na kawo maki and you are cooking, amarya bata girki ai" Bata ce komai ba ya juya ya fita, har ta fito daga kitchen yana xaune parlor, ta wuce sama rike da plate din abincinta, kasa cin indomie din ta yi ta sha five alive da ta debo kadan ta tura abincin gefe tana jin wani xafi da xuciyarta ke yi mata, bayan wani lkci ta mike ta fitar da plate din har lkcn yana parlor xaune ya bi ta da kallo ta shiga kitchen ta fito ta koma sama, bata kuma sake fitowa ba har Magrib. Bayan Isha tana tsaye gaban press sanye da hijab har kasa xata fito da kayan bacci da xata sa Mujaheed ya shigo dakin, ko kallon direction dinsa bata yi ba ta ci gaba da ciro sleeping dress dinta, ya kulle kofa ya karaso ya ajiye ledan hannunsa yace "Ga abinci" shiru bata ce masa komai ba ya isa bayanta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Ni kike sharewa ko??" Bai jira cewarta ba ya fara daga hijab dinta to gain access to her body, a fusace tace "Stop it Yaya" juyo da ita yyi ya fara kissing dinta gently yana daga hijab din, ta fara turasa amma ya ki sakinta, sun dau lkci sosai a haka amma gaba daya ta ki sakar masa jiki sai kukan take masa tana son kwace kanta, ya saketa daga karshe ya mike ya xauna gefen gado da idanuwansa da suka sauya kala, sauka take son yi daga saman gadon ya fixgota yace "You are only good at show casing unnecessary kishi, to warce kike kishi a kanta 6ata ta6a hana ni hakkina ba, ko da kuwa sau goma ne a rana.. I know what I am saying" Imaan tace "Sai kaje ta baka yanxu ai" daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin, sannan ya gyada kai. Washegari gaba daya Mujaheed bai shigo dakinta ba yanda ya saba da safe, ita dai ta gama duk abinda take, ta fita xuwa kitchen ta hada shayi ta dawo parlor ta xauna, sakkowa yyi downstairs kasancewar ranan Friday ne sanye yake cikin milk shadda da yyi masa kyau sosai, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya shigo parlon ya dau makullin motarsa yana kallonta don har snn kayan bacci ne jikinta yace "Sai yanxu kika tashi kenan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ehh" yace "Ohk, xan je gida sai na dawo after Juma'at prayer" tace "Nima xan je gida" yace "A'a ki jira next week xan kai ki" ta wani hade rai ta kallesa, yyi murmushi yana shafa kansa ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallon fresh legs dinta don kayan iyakar sa kneels yace "In sha Allah next week xa ki je ae" Bata ce komai ba ya amshi shayin hannunta ya jawota jikinsa ta fixge ta matsa daga wajen ta dau cup din shayin ta, mikewa yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, yace "What will you be taking for lunch?" Ba tare da ta kallesa ba yace "I will sort that out" dawowa parlon yyi ya ajiye makullin hannunsa da waya ya koma sama, ta bi sa da kallo gefen ido, sai da taji budewar kofar parlonsa sannan ta mike da sauri ta dau wayarsa ta ga ya sa lock, kallon wayar ta dinga yi da mamaki kafin ta kashe ta ajiye ta koma da sauri ta xauna, ya sauko downstairs rike da Atm card dinsa ya dau waya da makulli ya nufi kofa yace "Sai na dawo" Bata ce komai ba har ya fita, ta ajiye shayin hannunta don gaba daya ji tayi ya fita ranta, imagining ta dinga yi wai gun Safeenah xai je, lkci daya taji hawaye ya kawo idonta ta jinginar da kanta da kujera tana jin xafi a xuciyarta. Sai kusan la'asar Mujaheed ya dawo gidan, sai bayan kusan minti talatin ya shiga dakinta ya ganta kwance idonta rufe ya karasa kusa da ita ya xauna yana shafa fuskarta a hankali yace "Lil sis" kin bude ido tayi yyi murmushi don yasan ba bacci take ba, ya kai lips dinsa nata ta bude ido da sauri ta dauke kai, shafa cikinta yyi yace "Ga abinci Inna ta bada a a kawo maki downstairs" ta mike xaune ta koma can karshen gado on a serious note tace "Bana son kana ta6a ni Yaya, I don't like it" shiru yyi yana kallonta, can yace "Kar na ta6a ki sbda me?" A takaice tace "Saboda bana so" yace "Ohk" daga haka ya nufi kofa yace "Farida ta kira daxu tana gaishe ki" daga haka ya fita ta bi sa da harara, sai kuma ta 6ata fuska xata yi kuka. Haka nan suka ci gaba da rayuwa gidan da gaske kuma ya daina ta6a ta iyaka ya siyo mata abinci da drinks ya ajiye mata, wani lkcn ya hada da gasasshen kaza wani lkcn kuma fruits, a ko da yaushe tana daki ita kadai, shi kuma yawanci yana parlonsa, duk dare dai xai shigo to make sure ta sha drugs dinta sannan ya wuce dakinsa yyi kwanciyarsa. A haka har yayi resuming aiki ranan Monday, karfe takwas saura ya shigo daki ya ganta kwance tana bacci sbda dadewa da tayi tana azkar bayan sllhn asuba, ya isa gabanta yana kallon skin dinta dake wani sheki, ya durkusa kusa da ita, ya fi minti biyu yana kallonta kafin a hankali yace "Imaan" Bude ido tayi, sai kuma ta mike xaune ta koma baya, ya mike yace "Xan wuce aiki, akwai kayan shayi downstairs with bread, I don't know ko xa ki ci egg ki soya yanxu kafin in tafi" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" yace "Ohk..." Daya wayarsa ya mika mata yace "If you need anything you call me, but don't call anybody with the phone" tace "Ni dai xan kira Ammi na" juyawa yyi ya fita dakin ya kulle mata kofa. Sai kusan karfe hudu da rabi ya dawo gidan yana haurawa sama ya bude dakinta daga kai tayi ta kallesa daga xaunen da tayi gaban mirror tana tsefe kitson kanta, yace "Kin ci abinci kuwa?" Ta ci gaba da abinda take tace "Na ci" yace "Me kika ci?" Tace "Ni dai na ci" yace "Gobe xa a kawo maki house maid sai ki dinga monitoring dinta tana girki" ta kallesa tace "A'a bana so, xan iya" yace "Ai ba ni na fada ba, daddy ne ya fada" daga haka ya fita dakin nata. Ta gama tsefe gashinta ta dau abubuwan wanke gashi ta shiga bandaki ta wanke gashin nata sannan ta fito ta busar. Kwanciya tayi saman gado maganganun da Ammi tayi mata daxu ya dinga dawo mata, ji tayi kamar ta fashe da kuka tunawa da tayi Ammi fa ce mata tayi bbu ruwanta dole yana da hakkin kula da Safeenah da cikin da tace tana da shi, ita ko kadan bata yadda Safeenah na da ciki ba ta rasa dalili, gashi duk hanyar da xata san ko suna waya ynxu bbu don tun ranan bata sake shiga dakinsa ba. Bayan isha Mujaheed na dawowa masallaci ya shigo bedroom dinta da ledan abinci, kamar ko da yaushe a dai dai wannan lkcn yau ma ta fito wanka ne, da sauri ta koma bathroom, ya ajiye mata ledan abincin ya fita dakin, ta gama shirin kwanciyarta har ta kwanta sai kuma ta mike ta dau ledan ta fita da shi, xaune ta gansa parlor ya bi ta da kallo ganin kitchen xata shiga yace "Kin ci abincin?" Tace "Am not hungry" mikewa yyi ya bi bayanta, ta ajiye ledan xata juyo suka kusa cin karo, komawa baya tayi da sauri ya dau ledan da plate sai cup ya kamo hannunta yace "You must eat, baxa ki kwanta haka ba" da mamaki tace "Ka ta6a ce min I must eat a gidan nan?" Bai tanka ta ba ya xaunar da ita ya debar mata abincin ya ajiye mata sannan ya xuba mata drink din ya ajiye yace "ki cinye yanxun nan Ina kallon ki" da mamaki take kallonsa, can tace "Ni dai nace maka na koshi" yace "I am not joking imaan, ki ci abincin nan ko kuma ki sha drink" shiru tayi tana kallonsa, can ta turo baki ta dau spoon ta fara cin abincin yana kallonta ko kiftawa bbu, da kyar take hadiyewa daga karshe ta ajiye cokalin ta mike tace "Ni dai na koshi" rikota yyi yace "Drink din fa?" ta xaro ido tace "Ni bana shan drink da daddare" ya hade rai yace "Take it now Imaan" dariya ya bata ganin how serious he is tace "Ni ka ta6a ganin na sha drink da daddare haka?" Yace "Ehh ki sha ko kadan ne" kamar xata yi kuka tace "Ni Yaya fa baxan iya Sha ba" ya dauka cup din ya kai five alive din bakinta yace "Bude bakin my friend" karba tayi a hannunsa kamar xata yi kuka ta kai bakinta ta fara sha, ya dinga kallonta har tayi rabi sannan ya saketa ya mike yyi wucewarsa sama ta bi sa da kallo ta ajiye sauran drink din.





IMAANWhere stories live. Discover now