Part 8

86 1 0
                                    

41.....



Sadeeq yayi murmushi a hankali yace "But you didn't tell me you where coming here da muka yi waya daxu" Ta dau hijab dinta ta saka still bata juyo ba tace "Ae ba wajen ka na xo ba" murmushi kawai yake yana kallonta, Mariya ta iso bakin kofar rike da tray din abinci tace "Ya Sadeeq Aunty na neman ka fa" ya kalleta yace "Har kin ji sauki kenan" dariya tayi tace "Ehh mana bayan alluran da ka sa aka min, Kuma ga kawata ta xo, Hope yau dai ka tuna ta" Ya langwabar da kai yace "Bayan ta ki juyowa ma in ga fuskarta balle in san wacece" Mariya ta wara ido ta kalli Imaan da ta ki juyowa da gaske, ta yi dariya ta karasa cikin dakin ta ajiye abincin hannunta ta isa kusa da Imaan ta juyota suna facing Sadeeq tace "Toh ka gane ta yanxu?" Shafa kai yayi yana cute smile dinsa yace "Anya.. wani anguwar take? Na taba ganinta ma kuwa?" Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba ta sunkuyar da kanta, Mariya ta bata fuska tana kallonsa don da gaske bata ji dadi ba, Sadeeq ya wara manyan idonsa yace "Toh Sannu da xuwa kawar Mariya, duk da dai ni ban gane ki ba" daga haka ya juya ya rufe masu kofar, duk yanda Mariya tayi forcing din Imaan ta ci abincin da ta kawo mata kin ci tayi wai ta koshi, ruwa kawai ta sha shi ma sip daya, Mariya da gaba daya bata ji dadin kin cin abincin da Imaan tayi ba tace "Dama ki dau drinks dinki ki koma da su bana so da gaske" dariya kawai Imaan tayi ta mike tace "Sai ki ba su Hafsat idan sun dawo, ni dai tashi ki rakani" Mariya tace "Bayan kin walakanta ni xa ki ce in raka ki" Imaan na murmushi ta nufi kofa tace "Toh ni fa na ci abinci a gida nace maki Mariya" Mariya ta mike ta bi bayanta suka fita dakin tace "Toh mu je ki yi ma Aunty sallama ya na iya da ke, nima dai ko ruwa kika ban idan naje gidan ku baxan sha ba" Imaan ta kalleta ta gefen ido tana murmushi suka shiga parlon mum dinta, Sadeeq na parlon tare da mum din nata a xaune, Imaan ta durkusa kusa da kujera tace "Aunty xan tafi" Mum din Mariya tace "Da wuri haka Imaan, toh Ina xuwa" tashi tayi ta tafi dakinta, Imaan ta sata kallon inda Sadeeq yake taga kallonta yake, ta dauke kai da sauri, Mariya tace "Ya Sadeeq yanxu fa su ya Annur xa su iya dawowa basu kawo min komai ba ko?" Yace "Toh ki kirasu mana" Tace "Toh don Allah kira min su ta wayarka, I can't imagine me not eating shawarma today" yace "Wayana na can gida" tashi tayi ta bi mum dinta daki don daukan wayarta ta kira step brother din nata, Sadeeq na kallon Imaan yace "Me yasa baku xo tare da kaka ba?" Ta dai yi murmushi bata ce komai ba, Aunty ta fito rike da leda ta ajiye kusa da Imaan tace "Ki gaida min mum din ki kinji Imaan" a hankali Sadeeq yace "Aunty ita ce fa warce nake yawan baki labari a kai...." Aunty ta kalli Imaan sannan ta kallesa da mamaki tace "Imaan din kuma?" Yana murmushi yace "Sure..." Sake baki tayi tana kallonsa, ya shafa kansa yace "Dama nace maki ba ma sai na kawo maki ita ba da kanta xata xo wataran ki ganta" Imaan taji kamar kasa ya bude ta shige don kunya, ta kasa dago kanta ta kalli Aunty, Aunty tace "Ikon Allah, wai da gaske kake don Allah Sadeeq" Yace "Gata ki tambayeta, but aunt this is our secret ko Mariya kar ki gaya ma plss Aunty, you know Mariya talks a lot...." Dariya kawai Aunty tayi ta xauna tace "Ikon Allah, Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi, yayi xabi na gari..." Yace "Ameen" Mikewa yayi yana kallon Imaan yace "Let me drop you" da sauri ta girgixa kai sai dai bata ce komai ba, Aunty tayi dariya tace "Aa ki je dai ya ajiye ki gida Imaan, ki gaida mutanen gidan kin ji, Allah maki albarka..." Sadeeq na murmushi ya nufi kofa ya fita, Aunty na kallon Imaan tace "Imaan idan ma kina da doubt a kan Abubakar a da, tohh stop that now kinji daughter, Sadeeq na son ki fiye da yanda kike tunani, I was so surprise da naji yace min ya sami yarinyar da yake so da aure yar Nigeria, coz ni nasan waye Sadeeq, I know him fiye da uwar da ta haifesa ma, kuma wllh duk jinsa nake ba wai na yarda ba, har gajiya nake da jin labarin ki a bakinsa, But plss kiyi kokarin kame kanki ki kare martabar ki na 'ya mace, am not saying this bcos Sadeeq is bad or anything of such, A'a Ina gaya maki haka ne a matsayina na uwa, ko Mariya iyakar shawarar da xan bata kenan...." Imaan dai ta kasa dago kanta, fitowar Mariya yasa Aunty tayi shiru, Aunty na kallonta tace "Ki rakata compound Sadeeq xai ajiyeta gida yanxu, he is waiting for her" Imaan ta mike tayi ma Aunty godiya cikin sanyin murya ta fita, Mariya ta dau ledan da Aunty ta ajiye mata tace "Mun gode Aunty" daga haka ta bi bayan Imaan da sauri, Mariya ta bata fuska ganin bata ga Sadeeq a bangarensu ba, tace "Kai ya Sadeeq maimakon ya dau motar dake nan yanxu sai mun bi sa har can" ita dai Imaan bata ce komai ba, haka suka dinga tafiya a lafcecen compound din xuwa bangarensu Sadeeq, Building din ya kusa biyun nasu Mariya, Kai kana gani kasan an rasa yanda xa ayi da Naira kuma, Motocin dake parking spaces din wajen sun yi goma ko wanne kuma ya wuce a kirasa mota sai dai Ride, ni kam nace don ma Inna bata xo taga gidan ba... Ai da gobe gobe xata sa Bukar da Ahmadu gaba ta tada bala'i a daura auren Imaan da Bulasawa... Lol, Sadeeq na xaune cikin daya daga motocin parking space din idonsa a kan Imaan dake tahowa tare da Mariya, irin kallon da yake mata yasa Mariya ta kalli Imaan sai dai bata ce komai ba, ana haka aka bude gate din gidan wani ride ya shigo compound din, Mariya tayi ma motar kallo daya ta dauke kai, Drivern yyi parking aka bude back seat, wata da baxata wuce shekaru hamsin ba ta sakko motar cikin shiga ta alfarma, tun daga kunnenta, wuyarta, finger, da wrist duk gold ne, tun da Imaan ta kalleta sau daya ta gane Mahaifiyar Sadeeq ce, Mariya tace "Sannu da dawowa Mami..." Sama sama matar ta amsa, Imaan ma ta gaisheta, ba tare da ta kalli Imaan ba ta amsa, tana kallon Sadeeq tace "Fita xaka yi yanxu Abba..." Ya fito daga motar yace "Welcome back Mami" tace "Yauwa..." Yana shafa kansa yace "Aunty tace in ajiye bakuwarta a gida..." Daga sama har kasa ta kallesa bata dai ce komai ba ta nufi entrance din babban gidan, ya bi ta da kallo, can yace "Mami xa a maki wani abun ne?" ba tare da ta juyo ba tace "Noo ka tafi inda aka aike ka, ka sameni parlona dai idan ka dawo, is Annur back?" yace "I don't think so" Front seat ya xaga ya bude ma Imaan yana kallonta, Mariya ta ajiye ledan hannunta a bayan motar ta xaga gun imaan tace "Plss kice ma Ammi ina gaisheta kin ji" Imaan ta shiga motar tana murmushi tace "Toh xan gaya mata" Sadeeq ya tada motar suka fita compound din Mariya na daga masu hannu, Sai da suka hau saman titi murya can kasa yace "Nayi missing din beautiful face din ki two days Imaan" Murmushi kawai tayi, yace "ke ko naga ma baki damu da rashin xuwa na ba koh? You won't even understand what I am going through now" Ta kallesa a hankali tace "I thought you are busy this days ne shi yasa" girgixa kai kawai yayi, bayan kusan minti biyar yace "My birthday is coming soon...." Ta kallesa tace "When" yace "7 days from today in sha Allah" shiru tayi don ranan daurin auren Mujaheed kenan, can tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" yace "Anything for me?" Murmushi tayi tace "Me kake so?" Murya can kasa yace "Ke nake so Imaan" ta wara ido tace "Ni kuma" ya gyada kai yace "I don't know... i just have this urge of wanting to be with you, sai yanxu nake ganin nisan kwanakin da suka rage... I want you by my side as my wife" kasa kallonsa tayi ta kuma kasa cewa komai, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru" kwace hannunta tayi a hankali still ta ki cewa komai, parking taga yayi ta juya tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "I am thinking of meeting grandmum, ko xata kara yi ma su Abba magana" Imaan ta kallesa da sauri tace "Maganan me?" Yana kallonta yace "Su yi hakuri su bani ke any time from now, wllh har professor xan iya barinki ki xama a gidana" Imaan ta girgixa kai kamar xata yi kuka tace "A'a ni dai, bayan ga abinda daddy na yace" Shiru yyi yana kallonta, cikin sanyin murya yace "Toh shikenan i will continue waiting and having patient in sha Allah" Driving ya ci gaba da yi, sai da suka kusa layinsu yace "My frnds are throwing a birthday party for me, kuma ke ce babban guess a wajen ranan" ta wani xaro ido tana kallonsa yace "Yea, don't turn down my offer baxan ji dadi ba....." Kasa cewa komai tayi yana shigowa layinsu gabanta yyi mugun faduwa, what if Mujaheed na waje yanxu haka, kafin ya isa kusa da gate dinsu da sauri tace "Kawai ma ka ajiye ni a nan ba sai ka karasa can ba" ya kalleta yace "Why?" Ta hadiye abu da kyar tace "Nothing" Bai ce komai ba ya kai ta har bakin gate din ta fara kalle kalle kamar munafuka ta bude motar ta fita yace "Wait Imaan" tsayawa tayi ya juya ya dauko ledan da Mariya ta ajiye mata, Mika mata yayi ta amsa tace "Nagode sai anjima" daga haka ta shige cikin gidan da sauri har hakan ya basa mamaki ya bi ta da kallo, tana shiga kuwa ta kulle gate din, sai da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin Mujaheed da Yusuf a compound din, Yusuf na xaune kan farin kujera Mujaheed kuma da alama gate xai fita amma sai kallonta yake, bata tsaya wani tunani ba ta fasa wani ihu ta sake ledan hannunta ta durkushe wajen tana yarfe hannu tana kiran Ammi, Mujaheed ya karasa inda take da sauri yana kallon kafarta yace "Me ya faru??" Ta kamo hannunsa tace "Wayyo Yaya kafana ban me ya same shi ba..." durkusawa yyi ya daga dogon hijab din jikinta yana kallon kafar, ta gefen ido ta dinga satan kallon kasan gate taga ko Sadeeq ya gama reverse.



IMAANWhere stories live. Discover now