6_10

1.1K 17 2
                                    

*♡AMNOOR...!*
A Romantic story💋

*PAID BOOK!₦500*
*_DOMIN SAMUN CIGABAN LITTAFIN ZA'A TUNTUƁI WANNAN NUMBER TA WHATSAPP_* 09079740079

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. W. A★

🔞❌...

Free page 6_10

“Yes! an fasa wannan Auren in kuma ka shirya mutuwar ƴar ka Bisimillah, Gida na ni ɗaya ce! Aminu bai isa ya sake wata mata ba muddin ina raye ba shi da power ɗin ƙara Aure..!” Tas tas ta ji saukan lafiyayyun mari har guda biyu sake bindigar tayi a ƙasa tare da dafe kuncin ta tana kallon Alhj Aminu “Ka mare ni?” Cikin tsananin ɓacin rai ya ce “Ki na mamaki ne kin ɗauka yanzun  da ne, da zaki ratso tsakiyar maza kiyi mun tijara sannan ki ta fi lafiya? Laraba da yuwuwar na kai ki asibiti domin bincikar lafiyar ki wannan shi ne karo na biyar da kike ɓata min Aure..” Riƙe shi Hon Sa'id ya yi tare da kara waya s kunne yana kiran matar sa, Babu ɓata lokacin Salamatu ta ƙara so tana jan hannun Hj Larai, “Me kenan kika aikata haba Larai har yanzun kina nan da wannan halin naki fisabidillahi bakya kyautawa wannan ai hauka ce, Ya zaki kwashi yara ki ta fi tare da su kuma a gaban idonsu kike aikata komai wannan fa ba tarbiyya ba ce...” Dakatar da ita Hj Larai tayi tana magana rai a ɓace “Sannu uwata! Na ce sannu, kinzo ki ta sa ni gaba kina min faɗa da Sa'idu ne yace zai ƙara Aure ban san irin haukar da zakiyi ba..”
"Wallahi ba abinda zanyi Sunna fa zai aikata in dai Auren zai samar da kwanciyar hankali wallahi ina maraba in har mace ta gari zai ɗauko bani da matsala ai gwara Auren da  biye-biyen matan banza, Magana ta gaskiya kina takura Aminu babu hali ya yi ƙoƙari Aure sai kinyi sare sarin da zaki rusa masa farinciki ban san wata shegiyar ba ce take kawo miki gulman Auren sa, yau da ace kina faranta ran sa nasan ko kusa bazai yi tunanin wani Auren ba, da'ace har yanzun kina haihuwa na rantse miki da Allah Aminu bazai ji sha'awar ƙara Aure ba, Amma ya son yara Hajiyar shi naso taga ya tara zuri'a kasnacewar shi ɗaya ne ɗan ta Namiji duk sauran ƴaƴanta mata ne. Amma ke kin juyar da mahaifar ki kin ce baki buƙatar tara yara yo ba dole.."

"Ya ishe ni haka!" Tsaki Salamatu tayi tare da juya kan motar ta ta nufi gidanta lamarin Larai ya daina bata mamaki ya dawo bata tsoro dan bata dan sheɗanin dake kai mata gulma ba.

Gyaɗa kai Hajiyar shi tayi bayan ta gama jin duk wani jawabi daga bakin Hon Sa'id, "Allah ya kyauta Amma lamarin Labara na buƙatar ganin likita nafi tunanin aljanu gare ta" Aminu dake kwance hannunsa ɗaure da drip domin tun a can ya zube jinin sa ya hau dalilin da yasa suka ranƙayo da shi asibiti tare da kiran Mahaifiyarshi kenan, Murya a dusashe ya ce "Wallahi Umma tsaban iskanci kawai yake damun ta, karki ɗauki alhakin Aljanu ban cin ina duba daraja da girma irin na zumunci wallahi da na daɗe da sakin Laraba saboda fitina ni kenan bani iko da gidana ƴan'uwa na basu da ikon zuwa gidana yara na ban isa in ce musu kaza suyi ba, kowa abinda ran shi ya raya masa shi yake yi wani irin jarabta ce wannan?"

"A kul! Kar na sake jin irin wannan kalaman, Ka sake ta ta je ina? Ai haƙuri zaka ci gaba da yi. Shiya sa tun farko da ka ce Labara zaka Aura na ƙi, Domin na san halin Zuwaira duk da ƙanwata ce Amma yaranta basu da ɗa'a sam, Ganin ka na ce lallai sai ita shiyasa na zama ƴar kallo yanzun wa gari ya waya? Sai kaci gaba da haƙuri da halinsu shawaran da zan baka shine kayi ƙoƙari koma ya ya ne karka bari nan gaba ta wargaza maka Aure duk yanda za'ayi kafun a shiga sabuwar wata kayi Aure ko nayi maka Aure da duk wacce tayi mun!"

"A'a Hajiya Umma a dai yi haƙuri In Sha Allahu zai duba wacce tayi daidai da ra'ayin sa" Cewar Hon Sa'id. Ita dai bata sa ke cewa komai ba har aka sallamoshi.
  Durƙusawa Maman Nafisa tayi har ƙasa tana mishi barka da zuwa "Yawwa sannu da aiki, Ga wannan a siyawa yara wani abun" Hannu biyu ta saka tare da faɗin "An gode Baban Hisham Allah ya ƙara buɗi Ubangiji ya shiga lamarin ka" Cike da  jin daɗin Addu'ar ta ya gyaɗa kai tare da nufan part ɗin shi dake sama, Cikin gaggawa ta kammala ayyukan ta kafun ta nufo gida cike da murna tana ƙirga kuɗin da Alhj Aminu ya bata dubu goma sha biyu ne cas, Har da hawaye saboda tsananin murna ta mance rabon da ta riƙe dubu biyar nata na kan ta , Yau gashi tana riƙe da kuɗi masu yawa.

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now