17&18

630 6 1
                                    

*_♡AMNOOR...!_*
_A Romantic Story_

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. W. A★

Free page 17_18

*H-P Place Group*

"Ki yi haƙuri Nuriyya ta ko wanne yanayi Ubangiji ya kan jarabci bawa domin ya gwada ƙarfin imaninsa ta ki ƙaddarar kenan babu ta yadda za ki kauce masa Allah ya ƙara miki lafiya da sannu za ki ga sakayya akan duk wanda ya aikata miki wannan aika-aikar, me ya sa ba ki kira number dana ba ki ba? Yanzu da ban biyo Na'ilah duba ƙawarta ba shi kenan ba zan san abin da ke faruwa da ke ba? Har yanzun kin kasa sakin jikinki da ni bayan da zuciya ɗaya nake ƙaunar ki, Allah ne shaida"
Sunkuyar da kai Nuriyya ta yi tana jinjina irin ƙaunar da Amrah take mata "Na gode sosai Amrah!" Hannunta ta riƙe tana faɗin "In Sha Allah zan tsaya miki a dawo da case ɗin.." Cire hannunta ta yi daga nata tana faɗin "In har da gaske ƙaunar da kike min daga zuciyarki ce dan Allah kar ki ɗaga wannan maganar koma waye na yafe!" Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke hawayen da ke zubo mata "Shi kenan ba zan tada maganar ba tun da ba ki so zamu wuce ki riƙe wannan zamu dinga magana" Kallon waya tare da tulin kuɗin ta yi da sauri Maman su ta ce "Amratu! Wannan kayan arziki haka? Ubangiji ya yi albarka mun gode ƙwarai!" Murmushi Na'ilah ta yi sanan ita ma ta miƙawa Fiddoh kuɗi tare da ajiye mata jakar da ta zo musu da shi wanda yake ɗauke da kayan abinci "Beb! Ki yi ƙoƙari ki miƙe Please ana ta cigiyarki kowa ya yi missing ɗin ki duk casu idan babu ke ba daɗi wallahi gashi kwana biyu ba wani update tun bayan na Alh. Aminu bamu sake fitar da komai ba, after zan dawo tare da Dr ya duba mana ke" Gyaɗa mata kai Fiddoh ta yi tare da faɗin "Thank you Bestie!"
Bayan tafiyarsu Maman su ta kalli kuɗi haɗe da kayan tana jinjina lamarin a zuciyarta ashe har yanzu akwai mutane irin Alh. Aminu a duniyarnan? Zaliha ce ta katse mata tunani ta hanyar faɗin "Wayyo Allah daɗi kashe ni! Allah yai musu albarka yanzun Mamanmu tun da kin iya turare Allah a ware wasu kuɗin ki faɗa min abubuwan da za a sayo sai ki fara yi kawai kuma a duba mana wani ɗaki daban kinga da ma nan ya yi kaɗan wlh tsawon shekaru muna zaune a ɗaki ɗaya yanzu ka a ware mana namu." Maman Nafisa ta ce "Kin yi gaskiya, amma ina tsoron kar Babanku ya zo ya ɗauke kuɗaɗen dan wallahi muddin ya shigo na san sai ya ga wannan kuɗin.."
"Aikuwa bai isa ya je inda kuɗin nan suke ba, wallahi muddin ya taɓa zan yi mishi rashin M.." Fiddoh ta faɗa tana gyara kwanciyarta.
Da yamma kuwa sai ga Na'ilah ta dawo tare da likita nan ya shiga duba jikinta sannan ya bata magungunan haɗe da allurai bata ƙyale likitan ya ta fi ba sai da ta sa shi ya duba jikin Nuriyya.
Kwana biyu tsakani Fiddoh ta miƙe ta fito ras da ita nan ta tsaya ta ƙarewa matan gidan kowacce sai da ta zageta sannan ta fita ta nufi gurin Emanuel da ma a takure take daga nan ne fa lamarin ya canza salo nan suka faɗa duniyar masha'arsu Fiddoh kamar mayya haka ta kanannaɗeshi suna abu ɗaya sai da ta fanshe kwanakin da basu tare sannan ta ƙyale shi tana kwance saman jikinshi tana murza nipples ɗinsa cikin yanayin da ke nuna har yanzu bata samu gamsuwar da take buƙata ba, hannunta ya riƙe yana magana cin Hausar da be gama ƙwarewa. "Mene kuma Fiddoh? Na yi sosai ki bari na huta haka.." Wani irin numfashi ya ja sakamakon kamo bananarshi da ta yi tana matse saman "Hmmm!" Ya sauke wani gwauron numfashi yana jin yadda take tsotsar abin sai da ta sa suka koma tana ride ɗin shi kamar ba za ta ƙyale shi ba. Sai da ya ga abin nata na neman fin ƙarfin shi kafin ya ƙwace daga jikinta yana mayar da numfashi duk da shi ya fara buɗe mata ido amma ya lura jarabarta ya fi ƙarfin sa. Kallon sa ta yi tana yamutsa fuska sannan ta shirya ta fita.
Bayan ta karɓi dubu biyar gurinshi domin yanzu rashin mutunci take ji.

Tana fitowa suka yi karo da Baban su dakatawa ta yi tana ƙare mishi kallo ganin yadda ya sha shadda me ruwan goro sai maiƙo yake ga dukkan alamu sabo ne kallon takalmin ƙafarshi ta yi nan ma dai sabo ne hatta agogon hannunsa. "Allah ya sa dai ba kayan wasu aka ƙwamuso ba, dan na ji ana sanar da cewa an yi sata.." Hannunsa da ya miƙo mata ne ya sa ta katse maganar tata alamu yai mata akan ta ba shi na shi kason "Wallahi ba zan ba da ba! Domin gumi na ne, yadda kake buga jiki kake ɗauke-ɗauke haka ni ma nake sake jiki na yi abin da za a ba ni kuɗi.."
"Au haka ne abun?" Cike da baƙin cikin halinsa ta ce " Ya fi haka, lokacin da nake kwance me ka tsinana min? Mamanmu ke ɗawainiya da mu ita ce take fita tana yawo a rana domin samo mana abin da za mu ci.."
"Ba za ki ba ni ba kenan?" Tsaki ta ja sannan ta ce. "Muje na gwada idan ya mun sai na ba ka." Tana gama faɗar haka tai shigewarta ba tare da ta ba shi ko sisi ba.
Komawa yai gun Ema yana tambayar shi yau bata shawu ba ne? "Ta sha amma ba sosai ba" Gyaɗa kai ya yi tare da miƙa ma sa hannu "Mene ne kuma?" Emanuel ya tambaye shi tare da ɓata fuska. "Money! Ai na faɗa maka duk lokacin da kuka yi wata mu'amula ina da nawa kason ɗiyata ce, ni na ba ka go and hed ɗin da kake kome da ita" 2k ya zaro ya ba shi. Lokacin da ta shiga gidan direct ta nufi ba yi bayan ta ɗauki ƙaton butar da Maman Nafisa take alwala da shi kallon Zaliha da ke girki ta yi sannan ta ce "Ki kawo min ruwan zafi" Taɓe baki Zaliha ta yi sannan ta ɗibi ruwan tabi bayan ta da shi.
Washegari bayan fitar ta sai gata ita da su Na'ilah da leda niƙi-niƙi cike da kaya ta direwa Maman Nafisa tana faɗin "Kayan haɗin turaren na kawo miki tare da haɗin gwiwar 'yan group ɗin mu" Cike da mamaki Maman Nafisa ta ce "Wani group kenan?" Dariya suka yi sannan suka fita Fiddoh tana faɗin "Group ɗin 'yan sirri masu tona asirin abin da ba'a sani ba" Wani iri take jin abun, daɗi ne ba daɗi ba, rayuwar da Fiddoh take yi sam bata so babu yadda za ta yi, ka haifi ɗa ne ba ka haifi halinsa ba, mutane da yawa suna mata kallon uwar da 'yarta ta gagare ta bayan kuma ba haka ba ne, da ana buɗe zuciya da ta buɗe kowa ya ga irin baƙin cikin da ke ciki wanda ya danganci halin da Firdausi take yi, duk iya ƙoƙarin da Uwa take Allah ya gani ta yi shi amma abun sai dai a barwa Ubangiji...
"Ki yi haƙuri Mama addu'a za ki ci gaba da yi mata. Komai yana da ƙarshen sa haka watarana zai zamto tamkar ma ba a yi sa ba". Cewar Zaliha, ɗauke hawayen da ke zubo mata ta yi tare da faɗin. "Haka ne Zaliha Ubangiji ya daɗe shirya mana zuri'a." Amsawa ta yi sanna ta kwashe kayan ta je ta adana su. "Mama!" Juyowa ta yi tana kallon Zaliha. "Na'am Zaliha ina sauraron ki."
"Da ma na ce yaushe za ki fara yin turaren? Dan na faɗawa Malaman islamiyyan mu zan kawo musu su saya kuma ma na ce da ƙawaye na su faɗa a gida.." Shuru ta yi ganin Maman Nafisa tana murmushi "Tun ba a fara ba har kin soma tallar?"
"Ai da zafi-zafi akan bugi ƙarfe in ji masu salon zance" Miƙewa Maman Nafisa ta yi tana faɗin. "Ai da ma sai masu salon zance dan Hausar ma jinsa muka yi, zan yi ƙoƙari na fara amma fa gaskiya bana son maganar tallar nan domin na riga na yanke shawarar na fita da shi..." Cikin shagwaɓa ta katse mata maganar "Haba Mamanmu! Bafa tallar ba ne, iya makaranta ne fa dan Allah kin ji Allah daga makaranta shi kenan" Da ƙyar dai ta lallaɓa Maman su ta yarda akan in ta yi zata bata ta je da shi. Duk wannan budurin da ake Nuriyya tana daga kwance tana sauraron su ba tare da ta ce komai ba.
Domin har yanzun jikin nata ya kan motsa mata, cikin kayan da Na'ilah ta kawo musu suka yi dafa dukan taliya suka ci su uku domin Fiddoh bata dawo ba, suna cikin cin abincin Baban su ya shigo shi ma suka zuba mishi sai da ya gama ci sannan ya tambaye ta inda ta samu kayan turare shuru ta yi masa ba tare da ta yi bayani ba. Nuriyya ya dakawa tsawa yana tambayar ta. A firgicewa ta yi nan jikinta ya fara rawa kamar wacce aka jonawa lantarki, tsaki yai tare da barin ɗakin da sauri Maman su ta yi kanta ita da Zaliha suna taɓa ta hankali a tashe Maman su ta kwantar da ita tare da riƙe mata hannuwa dan har idanunta sun firfito tamkar wacce rai yake shirin barin gaggan jikinta domin har wani shiɗewa take tana jan numfashi, da ƙyar dai jikin ya daina rawa. A lura irin na Maman Nafisa Nuriyya ta kamu da cutar ɗimuwa wadda  muddin aka yi mata magana me ƙarfi nan da nan take ficewa daga hayyacinta musamman ma idan namiji ne yai mata ihu abin na fin haka tsanani.

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now