27&28

501 8 0
                                    

*♡AMNOOR...!*
_A romantic story_
Wattpad: ayshajb
Arewabooks:ayshajb
®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. W. A★

Free page 27_28

Kuje YouTube ku yi Subscriber Channel ɗi na FARIN JINI HAUSA TV. Domin samun ƙayatattun littafanmu.

H-P Place Group.

Daga inda yake kwance ya ƙura mata ido yana jin yadda sautin kukanta ke ratsa kunnuwansa miƙewa yai zaune yana kallon yadda ta haɗa kai da gwiwa sai ka ce wadda yai mata mai gabaɗaya, a haka har barci yai awon gaba da ita sai da ya bari barcin nata yai nisa sannan ya ɗaukota tare da kwantar da ita kan gado ya shafa fuskarta yana murmushi “Drama gril, abu ba abu ba kuka, komai na kuka ne a wurinki” Toilte ya koma yai alwala yana fitowa ya shimfiɗa sallaya ya fara jero filfilu. Sai ƙarfe biyu sannan ya haye gadon tare da shigewa cikin jikinta, motsawa tai tare da buɗe ido tana kallon yadda hannayenshi ke saman cikinta shuru ta yi ba tare da ta ce komai ba jin bai yi yunƙurin yi mata wani abu ba ne ya sa ta sauke ɓoyayyen ajiyan zuciya. Washegari da gangan ya wanke mata hijjabinta ya fita yana murmushi, lokacin da ta farga da abin da yai mata kamar zata fasa ihu ga shi kayan da ke jikinta ba za ta so ya ganta a haka ba domin rashin ɗa'a ne duguwan riga me hannu shimi ne a jikinta wanda bai sauka gwiwarta ba, ga shi ya ɗame jikinta sosai ya fitar da shep ɗinta, kwanciya ta yi a gadon tare da rufe jikinta. Turo ƙofar yai tare da sallama murya can ciki ta amsa mishi tare ɓata fuska ɗauke kanshi yai ganin yadda take cika tana batsewa wayarshi ya kara a kunne bayan ya zauna kan kujera, satan kallonta yai tare da faɗin. “Ki zo ga Mamanmu...” Ai da sauri ta wuntsilo har da ɗan guduta, ta manta da yanayin da take ciki jin ya ambaci sunan Maman su. Wani irin haɗiye miyau ya yi yana gyara zaman shi ganin yadda kayan yai bala’in amsar jikinta, gefen shi take shirin zama ya jawota ta faɗo jikinshi, ajiye wayar yai a gefe tare da ƙura wa ƙirjinta ido yana sake haɗiyan miyau cikin marerecewa ta fara magana da ’yar siririyar muryanta “Kuma ka ajiye wayar? Dan Allah ba ni mu yi magana da ita...” Tsit maganar nata ya tsaya jin yana shafa fuskarta zuwa leɓen bakinta.
“Uhm ashe ba ki da wayo farat ɗaya kin taso kina juya min wannan ƙananun abun..”
“Wayyo Allah! Ni ka barni dan Allah ba na so!” Numfashi ya sauke sannan ya ɗagata tare da miƙa mata wayar ya nufi bayi. Hira sosai muka yi da Zaliha domin Mamamu bata kusa wai sun je bikin 'yar maƙofciyarsu ina gama magana da ita na fara binciken Number Amrah bugu ɗaya ta ɗauka “Mara kirki” Cikin ihu ta ce “Matar Daddyna afuwan! Ya abubuwa ya amarci? Ina fatan ana kula min da Daddy?” Juyowa na yi ina satar kallon shi ganin ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa ɗauke kaina na yi ina faɗi cikin raina _(Shi dai ba ya gajiya da wanka sai ka ce agwagwa bini-bini yai wanka)_ “Alhamdulillah Ya Mama da Abba ki gaishesu” Karɓan wayar yai tare da kashewa sannan ya min nuni da nawa ɓata fuska nai ina kallon wayar domin har yau ban iya amfani da shi ba. “Ayya Daddy ban iya amfani da wayar ba ne ai” Ido ya zuba mata yana so ta sake magana da shegen muryan nan nata mai tsayawa a zuciyar mai sauraro “Kika ce?” Ya faɗa tare da ɗaukar wayar ya zauna kusa da ita zubur ta miƙe domin kunyar ganinsa a haka take yi. Suna sallar Isha ya ɗauketa suka sake fita yau ma sun yi yawo dare sosai suka dawo gida yau kan ko wanka ba ta yi ba haka ta faɗa gadon saboda barcin da ya cika idanunta. Shi kam ba zai iya kwanciya haka ba, sai da ya watsa ruwa washegari suka kamo hanya direct ya nufo gida da ita inda ta ga an sauya komai na gidan harda fenti aka yi musu daga cikin motar take kallon gidan tana mamakin wadda yai wannan aiki domin ta san mai gidan de ba yi zai yi ba, dan gyaran bayin gidan ma da ƙyar ya yi sa. Ajiyan zuciya ta sauke jin ya kamo hannunta yana faɗin “Sai na zo kenan? Ko kuma mu wuce can gidan?” Da sauri ta kalleshi tare da kai hannu za ta buɗe motar “Ba zan samu wani abun ba?”
“Kamar me fa?” Cike da mamaki ta yi maganar. Matsowa yai tare da kai hannunta bakinsa “Irin haka..” Da sauri ta fara waige-waige tana jin wani bala’in kunya na rufe ta. Buɗe mata motar ya yi suka fito tare nan ya sa yara suka kwashe kayan zuwa cikin gida da sauri Zaliha ta fito ganin Nuriyya ce ya sa ta daka tsalle tare da rumgumeta “Wayyo Allah Aunty shi ne ba ku faɗa kuna hanya ba? Ina wuni Daddy barka da hanya” Da murmushi ya amsa mata yana kallon yadda Nuriyya take ƙasa-ƙasa da kai ita ala dole kunya take ji. Wannan yanayin nata ba ƙaramin burgeshi yake yi ba. “Hmmm! Alhaji da ma ina jiran wannan ranar ya kamata in faɗa maka gaskiya dangane da wanna yarinyar da aka liƙa maka, yanzu kai ba ka yi bincike ba ka amince da auren wannan 'yar iskar..” Runtsa idonta ta yi da ƙarfi tare da ƙanƙame hannun Zaliha idanunta na kawo ruwa.
“Ya Subhanallah bawan Allah me kake faɗa ne? Ban fahimce ka ba fa?” Ya faɗa yana kallonta yana son gasgasta zancen nasa duba da yanayi da ta shiga. “Eh Alhaji abin da ka ji na faɗa maka yarinyar nan karuwa ce! Maza uku suka gama hawa da sauka kanta, da farko ni zan aureta amma da na fuskanci halayyarta sai na janye dan ba mace-ta-gari ba ce, burin kowane uba ya samar wa 'ya'yansa uwa-ta-gari sai aka yi rashin dace domin da na fahimci ɓoyayyun halayyarta sai na ga ba zan iya auren fanɗararriya..”
“Innalillahi wainna ilaihir rajiun! Wallahi Daddy ƙariya yake min sharri yake min! Ban san...” Dakatar da ita yai ta hanyar faɗin. “Ya isa haka! Ku shiga gida!” Cikin ɗaga sauti yai maganar muryanshi na nuna zallar ɓacin rai. Baban su ne ya shaƙe wuyar mutumin yana faɗin. “Munafuki la'ananne me haddasa fitina tsakanin ma'aurata sai Allah ya la'ance ka..” Dukan shi yake yana faɗa mishi mugayen kalamai motar shi ya shiga da sauri yana jin yadda kanshi ke juyawa yana ji kamar ba a duniyar yake ba. “Taka mota mu tafi!” Da sauri ta buga motar tana kira sunan shi cikin muryan kuka “Dan Allah Daddy ka tsaya ka saurare ni wallahi sharri yake mun ka tsaya na yi maka bayani ba haka ba ne karka kalle zancen sa. Daddy dan Allah ka saurare ni...” Hannunta Amrah da ƙarasowarta kenan ta riƙe  suka nufi cikin gidan tana gunjin kuka “Me ya sa ba ki faɗa ma sa komai ba? Na ɗauka duk ya san abinda ya faru ashe bai san komai ba? Ɗan farincikin da na fara samu aka daƙushe min? Shi kenan ni ba zan ji daɗi ba a rayuwa? Amrah na dawo da niyar karɓan sa a matsayin miji duba da halayyarsa masu kyau da nagarta, Amrah mai ya sa ƙaddara ta zaɓe ni? Sai ni? Komai sai ni ce? Whay Amrah! Me ya sa komai yake zuwa mun a cukurkuɗe? Sai yaushe ne zan yi dariya kamar kowa? Sai yaushe zan samu sukuni na daina fuskantar matsalolin rayuwa? Ni kenan daga wannan sai wannan...”
“Yi haƙuri Noor komai da lokacinsa duk abin da yai farko zai yi ƙarshe wallahi na ɗauka Hajiya Umma ta sanar da shi komai ashe ba haka ba..”
Cikin kuka Nuriyya ta dakatar da ita da faɗin “Ya zan yi? Ban san yadda zan yi mishi bayani ya fahimta ba na san yana can yana saƙa zancen zuci..”
“In Sha Allahu komai zai zo da sauƙi muje ki yi sallah sai mu ƙarasa maganar daga ba ya”
Janta ta yi har ƙuryar ɗaki Nuriyya kam ta yi shuru tana kallon ikon Allah domin an canza fasali da tsarin gidan an ware part ɗin Maman Nafisa da ban haka ma nasu kowane da toilte an gyara tare da zuba kayan alatu “Duk cikin sati biyu aka yi wannan aiki? Waye ya yi?”
    Zaliha da ke ƙoƙarin girka mata taliya ne ta amsa da faɗin “Aikin mijinki ne duk shi ya yi mana wannan abun arzikin” Shuru tayi tare da ajiye handbag ɗinta ta nufi bayi wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala tana fitowa sai ga Fiddoh ta shigo da ihun murna ta rumgumi Nuriyya “Su amare an yi fresh kinga yadda jikinki yake wani glowing kuwa? Kin yi kyau kin cicciko lallai an ji...”
“Ke kam Allah ya shirya mana wannan bakin naki” Dariya ta yi tare da kwanciya saman Bed tana faɗin “Ina zanga Alhaji na? Taɓ! Wallahi na yarta aure ni’imomi gareshi tun da ga shi na gani da idona..” Tsaki Nuriyya ta yi don ta lura magana take son saka ta. Zaliha ce ta faɗa wa Firdausi abin da ya faru.. Tun kafin ta dire zancen nata Fiddoh ta wuntsilo tare da faɗin “Kan babban buran uba! Ai kuwa zai na ci kan uwar..”
Riƙe ta Nuriyya ta yi ganin yadda ta zaburo tana shirin fita ta san kuma muddin ta fita maganar ba zai tsaya iya nan ba sai an kai ga 'yan sanda dan kaɗan ne daga halin Fiddoh abu in dai ya shafe ta ko Maman su ba ta wasa da shi. “Mene ne haka? Dalla malama cika ni saina koya mishi hankali wallahi da sojoji zan haɗa shi su ci uban ɗan shegiya”
“Eh na san haka za ki yi shi ya sa ba na so ki fita Baba ma kaɗai ya ishe shi ba sai an kai ga hukuma ba..”
“Kina nufin kenan na ƙyale shi?” Cike da takaici ta miƙe tana jan tsaki sannan ta sake faɗin “Wannan shegen zuciyar naki ba ya faɗa miki gaskiya” Fita ta yi tana ashar domin dai ba ta cikin hayyacinta shi ya sa ma ta yi saurin dakatar da ita. “Ai da kin ƙyaleta wallahi..” Da sauri Nuriyya ta ce “A'a Amrah ba ki ganin halin da take ciki ne? Ta yaya zan barta ta je ta yi abin da za a dawo ana da-na-sani?”
Amrah ta ce “Kuma haka ne fa Allah ya kyauta, ina wayarki?” Kallon Zaliha da ke ajiye musu abinci ta yi tare da faɗin “Ɗauko min waya yana cikin jakar can” Juya wayar Zaliha ta yi tana faɗin “Wow! iPhone 14 pro max! Aunty Nuriyya wayyo Allah! zan kashe selfi..” Karɓan wayar na yi ina faɗin “Damuwarki ragagge ne”
“Noor ai gaskiya ce koni na yaba lallai an tsuma Daddyna dole kema ya gwangwajoki da wannan wayar da ake ya yi” Ta faɗa tana jujjuya wayar ita ma kana ta kira layin shi sai dai har kiran ya katse ba a ɗaga ba, sake kira ta yi amma still no answer sai da ta jera mishi five miss call bai ɗaga ba kallonta na yi domin tuni zuciyata ta sake karyewa murya na rawa na ce “Kin gani ko? Ya ƙi ɗaukar kiran...” Na ƙarasa maganar hawaye na zubo min “Tura mishi saƙo" Karɓan wayar na yi hannuna na rawa na rasa ma me zan rubuta kallon ta na yi tare da yin shuru “Noor ki nutsu! Mijinki ne a wannan ɗan tafiyar da kuka yi, ya ci a ce kin fahimci wa kike aure sati biyu ba wasa ba..”
“Wallahi Amrah na kasa tuno komai ban san abin da zan rubuta mishi ba, kuma ma ba zama yake ba, bare har na  karanci halayyarsa..” Amrah ta katse ta da faɗin “Ki tuna dai!” Runtsa idona na yi da ƙarfi nan sauran hawayen suka zubo a hankali na fara rubuta mishi kalamai har na gama sannan na tura mishi muna zaune har 10 domin ta ce a nan za ta kwana tun da Mamanmu sun je biki ƙauye ne. Abinci ma sai da ta takura min kafin na ci kaɗan.

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now