19_20

656 4 0
                                    

*_♡AMNOOR...!_*
_A Romantic Story_

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. W. A★

Free page 19_20

*H-P Place Group*

Riƙo shi Hon. Yai tare da faɗin "Haba da Allah! So kake ka illata kan ka ne ko yaya? Saura kaɗan fa ka buge da ƙofar nan.." Leƙowa Umma ta yi tana faɗin "Me nake ji haka? Aminun ne yake ƙoƙarin kassara kan shi don na ce ya je su gana da matarshi?" Runtsa ido yai da ƙarfi domin kalmar *MATA* tamkar saukar mashi haka yake jin abin a zuciyarshi. Haka suka fito haraban gidan motarshi yake ƙoƙarin shiga cikin ƙarfin hali domin gabaɗaya gwiwowinsa sun sace tamkar tayar mota "Dan Allah ka yi min jagora zuwa inda take wallahi zuciyata na mararin son ganin t..." Dakatar da shi Umma ta yi ta hanyar faɗin "A kul! Karka kuskura bare har ka fara wannan gangancin domin wlh muddin na ji ka je inda yarinyar take wallahi zan saɓa maka.." Dafe kan shi da ke tsananin sarawa yai tuni ya riƙe saitin zuciyarshi da ɗayar hannun "Dan Allah Umma ki yi haƙuri wannan hukuncin yai tsanani da yawa a yi mana uzuri kin san lokacin ɗaya ba zai karɓi wannan lamarin ba, a yanzu yana da damar da zai kawo na shi zaɓin dan Allah Umma ki sassauta masa.."
"Duk wannan daɗin bakin naka Sa’idu ba ɗauka zan yi ba, ka sake jaddada mishi aure ne dai an riga da an ɗaura kuma wallahi na ji wani abu bayan wadda na ce zuciyoyi zai ɓaci"
Buɗe idanunsa da suka fara sauyawa saboda tashin hankali yai a hankali kamar me koyon magana ya ce "An ya ba sauya min Umma aka yi ba? Mahaifiyata ba haka take ba, Umma bata taɓa yanke min hukunci me tsauri har haka ba ya zan yi da raina? Ya zan yi da tarin soyayyarta da ke nuƙurƙusan zuciyata wallahi akullu yaumi da ita nake kwana nake tashi ta yaya zan iya rabuwa da mace mafi daraja kuma mafi soyuwa a gareni farat ɗaya haka?" Ya ƙarasa maganar da ƙyar yana me ƙurawa Aminin nasa idanu.
"Aminu ka yi biyayya ga umurnin Umma Please ka sassauta wannan soyayyar duk fa wannan hidimar da kake ita fa yarinyar bata san kana yi ba, tana can tana rayuwarta cikin farinciki kai kuma kana ƙoƙarin jayya da Umma"
"To ya zan yi?" Hon. Sa’id Ya ce "Haƙuri domin ita ce komai muddin kuma aka ambaci wannan kalmar to tabbas an cuci wadda ake so ya yi ta" Lumshe ido yai tare da faɗin "Shi ke nan!" Duk yadda Hon. Sa’id Yaso fahimtar da shi amma ina karshe ma share shi yai, motar shi a gidan Umma suka bar shi domin yanayin da yake ciki ba zai iya tuƙawa ba.

Kallon shi Maman Nafisa ta yi ganin yadda yake washe haƙora yana ƙirga 'yan farare "Baban.." Be barta ta faɗi abin da take son faɗa ya katse ta "Alhamdulillah yau de buri na ya cika na aurar da wannan guzumar" Ya ƙarasa maganar tare da yin nuni da Nuriyya wacce take ta ƙoƙarin gyara kayan turaren da Maman su ta haɗa, wani irin ajiyan zuciya kawai ta sauke tare da zubewa a ƙasa da sauri Zaliha da ke shigowa tare da Manna su suka rufu a kanta "Ai ko mutuwa kike kina dawowa aure de ya ɗauru kuma gidan nera inda zan dinga samu ina da-na-sha Allah sarkin daɗi!"
"Haba Baba! Me ya sa kake irin haka? Ka san de ba lafiya ne da ita ba har yanzu bata gama dawowa hayyacinta da har za a aza mata wani damuwa ba.." Tsawa ya daka mata tare za zare mata ido yana faɗin "Ke ma irin haka zan yi miki.." Turo baki Zaliha ta yi tana faɗin "Wallahi ba de ni ba, ai ko sama da ƙasa za su haɗe ba wanda ya isa yai min aure ba tare da wadda nake so ba"
"Ke Zaliha! Mahaifin naki kike faɗawa magana? Ban hane ku da irin wannan ɗabi'ar ba? Wallahi na sake jin irin haka zan fasa bakin nan"
"Banga laifinta ba, kinga de irin abin da nake gudu na haihuwar 'ya'ya mata ko? Yau wannan 'yar tayin ce take faɗa min magana? Ai ga irinta nan, kin je kin haifi yara basu san irin kalamin da za su dinga faɗawa manyansu su ba, se na karya ki wallahi in sake jin kin tsoma baki cikin magana ta" Turo baki tai gaba tana ƙunƙuni, tsaki ya ja sannan ya fita a ɗakin yana me faɗin "Aure de an ɗaura, kodayake sun ce ba yanzu za a yi tariya ba" Buɗe ido ta yi tare da fashewa da wani hargitsattsen kuka "Mama dan Allah me na yi wa Baba da ba ya ƙaunar ganin farincikina? Ni kenan daga wannan sai wannan, wallahi na gaji da rayuwar Allah ka ɗauki..." Rufe mata baki Maman Nafisa ta yi tana faɗin "Ki ce Alhamdulillah!" Da ƙyar ta iya furta kalman sannan ta koma jikinta ta lafe tana mayar da numfashi kiran Amrah ne ya shigo wayarta a hankali ta ja jiki daga na Mahaifiyarta sannan ta ɗauki wayar.

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now