21_22

636 7 0
                                    

*♡AMNOOR...!*
_A romantic story_

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. W. A★

H-P Place Group.

Free page 21-22

A nutse ta matsa gefe inda babu hayaniya tare da manna wayar da kunnenta tana sake faɗin "Ki jira ni yanzun za mu dawo sai muyi maganar."  Juyowan da za ta yi ne ta ga mutum tsaye yana ƙare mata kallo tunanin inda ta san shi take, zuwa can dai ganin taƙi yin magana ne ya sa shi faɗin Ashe dai ke ce, yau dai ba zan yi ƙuncin baki ba, ki faɗa min sunanki tare da na gidanku domin na ɗau tsawon watanni ina neman ki" Ɗagowa ta yi tare da watsa mishi  narkakkun shanyayyun idanunta wanda yake ɗauke da zara-zaran gashi, cikin ƙwayar idon nata har wani maiƙo da sheƙi me fisgan hankali yake, shi bai taɓa lura da tsananin kyan nata ba sai yau da sauri ya ɗauke idonshi daga kallonta yana sakin ƙayataccen murmushin da ya ƙarawa kamilalliyar doguwar fuskarsa kyau da haiba. Waigowa yai yana sauraron zazzaƙan daddaɗan muryan da ke ratsa masarrafan da ke kai masa saƙo kai tsaye zuwa ga kunnensa.
"Sunana kuma? Me za ka yi da shi? Me sanin gidanmu zai amfane ka da shi?" Ta ƙarasa maganar muryanta na rawa saboda tsoro tare da kallon Zaliha da ke ƙoƙarin ƙarasowa wurin su.  "Ki nutsu! Ba wani abu zan miki na cutarwa ba, da alkairi na zo auren ki zan yi..." Wani irin duka ƙirjinta yai wadda ya sa har tana ƙoƙarin yin ƙwarewa sai dai shaƙuwa ne ya riƙe ta, da sauri Zaliha ta ƙaraso tare da riƙe ta suka bar wurin bin su kawai yai da ido yana mamakin yadda take a tsora ce, juyawa yai tare da shiga motar shi ya nufi gidan Hon. Sa’id domin yana son ganawa da Amrah.
        A rikice suka ƙarasa gida domin yanayin da take ciki abun ya ta'azzara zaunar da ita Mamansu ta yi tana yi mata fifita tare da shafa mata kanta hankali a tashe domin yanayin yadda ciwon yake zuwa ma Nuriyya ba ƙaramin kiɗimasu yake yi ba. Kallon tuhuma ta yi musu rai a ɓace take faɗin "Me kuka mata? Shi ya sa wallahi ban so fitar nan naku ba, babu yadda zan yi ne kawai dan abu kaɗan yake birkitata.." Fiddoh ta ce "Ki yi haƙuri Mamanmu!"
  Zaliha da ke zaune da hannu bibbiyu tai tagumi ta ce "Mamanmu to akai Aunty Nuriyya asibiti mana sai aji me ke jawo mata wannan yanayin ko Fiddoh?" Ta ƙarasa maganar tare da kallon Fiddoh "Bari dai Amrah ta dawo don yanzu ta fita wai Daddy na kiran ta" Suna zaune shuru har Babansu ya shigo yana baza ƙamshi zama yai gefen ta gaban goshin sa Fiddoh yana washe baki domin dama zero yake ya san zai samu wani abu wurinta "Fidausi ya aka yi naga duk kunyi kalan 'yan zaman makoki sai ka ce wadda aka ce na mutu"
Wani banzar kallo tai masa tana faɗin "Da a ce kai ne ka mutu yaushe za mu yi wannan zaman? Ai wallahi DJ zan ɗauko na yi ta tiƙar rawa ina dariya dan an rage mugun iri ne, Uban da be san ci 'ya'yansa ba balle akai ga karatu, tun da Mamarmu ta yi mana ƙoƙarin muka kammala sakandiri fa muke zaune, tun buɗewar idanuna ita ce ɗawainiyarmu ta yi ayyuka ƙarfi, wahala, ga azaban baƙaƙen magana daga bakin mutane, ga zafin rana, duk don saboda mu. Ta shiwar yayarmu ta ɗaura niyar taimaka maka sai dai kash! Wasu 'yan iska suka datse mana farinciki ba su duba rayuwa da yanayin da  muke ciki ba, suka take min 'yar'uwa wallahi ko ba jima ko ba daɗe akwai ranar ƙin dillancin duk ranar da na yi arangama da wa'yannan 'ya'yan Allah wadai ɗin hmm! Allah kaɗai ya san tanadin azaba da raɗaɗin da na yi musu.."
Dakatar da ita yai ta hanyar miƙa mata hannu bayan ya miƙe yana kallon jakarta, "Bani wani abu zan wuce ne"
Cike da shaƙiyanci ta ce "Mu je sai na ba ka.."
"Kinga bana son iya shege bani kawai na yi wucewa ta"
Ya faɗa tare da haɗe fuska. Tsaki Mamansu ta ja tare da miƙawa Nuriyya ruwa tana faɗin "Sallame shi dan Allah ya tafi tun da shi Allah ya yi shi mara lura bare ya fuskanci ya muke ciki.." Dubu ukun da take miƙa masa ya karɓa tare da tattara babbar rigarsa yai gaba.

"Ta yi aure fa kika ce Amratu? Wa ta aura? kuma a ina gidansu yarinyar yake? Ya sunan ta?" Kallon sa ta yi ganin yadda ya birkice tare da jero mata tambayoyi.  Alama mahaifinta yai mata a kan ta tafi miƙewa ta yi ita ma tana kallon yadda Daddyn Hisham ya birkice duk sai ta ji tausayin sa, domin ta lura ƙwarai yana son Noor ɗinta, musamman ma da Abbanta ya ba ta labarin yadda  suka haɗu, ta san da shi ya aureta za ta sha gata da soyayya sai dai momy larai fa za ta iya kashe musu 'yar mutane domin baƙin kishi ne da ita, sai kuma ga shi Allah ya yi mata gyaɗar dogo.
"Wai me ya sa kake katse ni a duk lokacin da nake gaf da cimma muradina ne kam?" Ya faɗa cikin yanayin damuwa tare da kallon Aminin nasa. "Gani nai kana ƙoƙarin ƙetare dokar Allah, ita fa yarinyar matar wanin ka ce, way not kai ma ka nutsu ka bi zaɓin mahaifiyarka, wata biyar fa ana abu ɗaya,  ka bar 'yar mutane da nauyin aure na farko ba sauke mata haƙƙinta ka yi ba, ta ya za a takura yarinya bayan kuma tana da miji.." A harzuƙe ya kai mishi naushi, kaucewa Baban Amrah yai yana dariyar shaƙiyanci tare da faɗin "Haba mutumina cool down ka je ku daidaita da wannan amariyar anjima fa ba a haɗu ba,  Larai ta nutsu tana harkan kasuwnacinta kai kuma ta barka da rumgumar filo tare da juyi cikin dare.." Miƙewa yai yana faɗin "Idan ka gama iskancin naka ni zan wuce gidan Umma" Dariya yai sannan shi ma ya miƙe yana faɗin "Ai tare za mu, domin ta ce mu je na san duk ba zai wuce maganar wannan auren ba"
Gaba yai yana jan tsaki domin har cikin ran shi ya tsani wannan maganar, matar ma baya buƙatar ganin ta.
Yana zaune tare da sauraron kukan da Suhaima take rero masa tana ba shi haƙuri a kan ya mayar da ita wurin momynta dan Umma aikin girki take saka ta ita kuma ba so take ba, ɗauke kanshi yai daga gare ta domin ba ya jin zai mayar da ita "Dan Allah Abba ka sa baki wallahi ba zan ƙara neman rigima ba" Murmushi Abban Amrah yai tare da kallon Aminin nasa. "Tun da ta yi nadama a ƙyale min ɗiya ta koma wurin gyatumarta.." Wani mugun kallon da Alh Aminu ya auna mata ne ya sa ta barin wurin cikin gaggawa tare da fashewa da kuka. Ga shi ko ta kira wayar momynta ba ya shiga kuma an hanata fita tana son zuwa duba jikin Lil amma Umma ta yi mata iyaka da ƙofar falo balle akai ga bakin get.
Gyaran murna Hajiya Umma ta yi ta shiga musu faɗa ta inda take hawa ba ta nan take sauka ba, ganin yadda Alh. Aminu ya watsar da maganar auren an shafe watanni a gefe guda kuma gantalin da Laraba take na yawon garuruwa da sunan kasuwanci ba ƙaramin ƙona zuciyarta yake ba, domin dai ta tabbata har yanzu bata ɗauki Aminu da wani muhimmanci ba,
"Wallahi wannan zaman da za mu yi ya zama na ƙarshe ka tafi gidan su yarinyar nan ku daidaita kanku dan a satin nan zata tare ba wani magana ɓata lokaci tunda abu na tafiya shekara" Ɗagowa yai tare da gyaɗa mata kai yana faɗin "In Sha Allahu za a yi yadda kika ce" Da mamakin kalamansa ta sake kallon shi ganin yanda ya sauko babu jayayya kamar lokacin baya, "Yawwa Madalla Ubangiji yai maka albarka Aminu na" Murmushin yaƙe yai mata sannan ya fara laluben makullin motarshi tare da ficewa a falon ya barta suna tattaunawa da Abban Amrah nan ta sanar da shi inda gidan su Nuriyya yake da kuma yadda take so a yi komai ba tare da Labara ta sani ba sun tattauna sosai inda ya tsayar da maganar da cewar zai gyara part ɗin Amrah domin yarinyar ta zauna a can na ɗan lokaci. Yana fitowa ya shiga mota tare da kallon Aminin nasa ya ce "Na ji daɗin yadda ka amince mata ba tare da jayayya ba, yanzun muje gidan su yarinyar" Shuru kawai yai masa har suka ƙarasa anguwar tsayar da motar yai yana ƙarewa gidan da suke fuskanta kallo. Dama tun fitar su Umma ta kira Baban su ta sheda mishi za su zo, yana ganin tsayuwar motar ya ƙaraso kallon up and down Baban Amrah yai masa ganin yadda yake taku ɗaɗɗaya yana maza gare.
"Barka da zuwa Alh" Ya faɗa tare da miƙa masa hannu nan shima ya miƙa masa suka yi musabaha sannan ya gabatar musu da kanshi tare da musu iso zuwa ɗakin shi da ke wajen gidan. Ɗakin fess yake kasancewar shi mutum ne me tsafta ɗan ƙwalisa domin ya ƙawata ɗakin da kayan ƙyale-ƙyale na zamani cike da shaƙiyanci yake magana tare da gabatar musu da kayan motsa baki kana ya ce "Har yanzu ban gane wane ne angon ba" Kallon Alh Aminu da ke ta murmushi yaƙe Baban Amrah yai kana yai masa nuni da cewar "Ga shi nan" Sunkuyar da kai Alh Aminu yai ganin yadda Baban su yake ƙare mishi kallo yana gyaɗa kai. "Madalla bari na turo muku ita" Yana fita Baban Amrah ya ce "Amma da ganin wannan sirikin naka ɗan duniya ne" Shi dai bai ce masa komai ba. Lokacin da Babban su Nuriyya ya shigo ya yi daidai da zura ƙatuwar hijjabinta tana ƙoƙarin yin Sallar la'asar da ya wuce ta domin yau da zazzaɓi ya wuni, "Nuratu ki shirya kina da baƙi a ɗaki na, ki yi sauri domin ba jimawa za su yi ba"
"Ai ka bari ta yi Sallah ko kuwa?" Maman Nafisa ta faɗa tana hararar shi. Jiki a sanyaye ta yi Sallar tana sallamewa ya azal-zala musu wuta ta yi ta fito Fiddoh da fitowarta kenan daga banɗaki ta kalle shi tare da faɗin "Ai ta amsa za ta zo, ka je mana, ka tsaya kana surfawa mutane ruwan bala'i haka za ta je ba tare da ta shirya ba?" Fita yai yana masifa.  "Dalla ke ma ki shirya kin yi tsaye se rawar jiki kike ba dole a cika mutane da surutu ba" Fashewa kawai Nuriyya tai da kuka domin ta rasa ya ma za ta yi. Ɗauke kai Maman Nafisa tai domin wannan ba maganar da za ta saka musu baki ba ne. "To ni me zan yi? Dan Allah shirya mu je tare.." Zaro mata ido Fiddoh ta yi tana faɗin "Wa? Taɓɗi! Ai ki shirya kawai ki je wurin mijinki ba inda za ni"
Juyowa ta yi tana kallon Mamansu da ke zuba turare a kwalba, "Ayya Mamanmu dan Allah ki ce mata muje tare" Ba tare da ta ɗago kanta daga abinda take yi ba ta ce "Ku je tare da Zaliha" Zaliha da ke taya ta zuba turaren ta zunɓuro baki tana mita ita tana aiki za a ɗaga ta. "Ai ko na je wallahi ba zama zan yi wurin mata da miji ba" Ta faɗa tana share hannunta a jikin hijjabin da za ta saka, kallon yadda Nuriyya ke shirin fita ba tare da ta shafa mai ko turare ba "Eyye! Dama haka ake zuwa wurin miji bagajan-bagajan ba shafa mai bare hoda ko turare? Kuma da wannan uban hijjabin za ki tafi sai ka ce matar malam?" Dakatawa Nuriyya ta yi tare da juyowa tana kallon yanda take hijjabin da take Sallah ne, ba shi da wani ainu. Bata aune ba ta ji Fiddoh ta buɗe turare tana zuba mata. Cikin faɗa Maman su ta ce "Wai Firdausi lafiyar ki ? Turaren nan fa an riga da an biya na gama musu haɗin kayan amare ne fa.."
"To ai ita ma amariyar ce" Fiddoh ta faɗa tana dariya tare da kallon yanda Mamansu ta haɗe fuska "Yi haƙuri Mamanmu ni zan biya sai a musu wani shi ke nan? Ku kuma tsayuwar me kuke? Ko se Baba ya dawo ne za ku tafi?" Hannun Zaliha ta riƙe suka fita Zalihar ce ta yi Sallama sai da aka amsa musu sannan suka shiga.
Zama suka yi kan ledar da ke malale ƙasan ɗakin cike da ladabi Zaliha ta gaishe su da murmushi suka amsa domin yabawa da nutsuwa tare da tarbiyyanta abin ya burgesu ƙwarai. Nuriyya kam har yanzun kanta na ƙasa da murmushi Baban Amrah ya kalli Nuriyya tare da taɓa Aminin nasa nan shima ya ɗago yana duban inda take, mutuwar zaune yai yana sake kallonta "Ita ce fa!" Ya faɗa yana kallon Baban Amrah wanda ya miƙe tare da yafito Zaliha suka fto tare da nufar wurin mota yana tambayarta sunan ta.
"Suna na Zaliha Hamisu Saleh"
"Ni ce name amma kina mace na ji ki da turaren maza kuma haɗi na musamman" Turo baki ta yi tana faɗin "To ba aiki ɗurawa nake yi ba, shi ne Mamanmu ta ce se na rako Aunty Nuriyya"
Dariya domin yanayin da yarinyar take magana ya burge shi sosai haka suka ci gaba da hira tana zuba mishi surutu da shirme shi kuwa yana biye mata can dai ya tambaye ta game da karatu shuru ta yi masa ba tare da ta ba shi amsar ba.
"Turaren na siyarwa kuke yi?"
"Eh kuma harda haɗin amare Mamanmu ta iya da na maza ma duka ana yi"
  "Je ki kawo min su na gani" Da gudu ta shiga gida ta ɗauko mishi kwandon da take zuwa talla da shi.
"Lallai Mamanmu ta iya turare masu kyau zan so mu yi magana da ita domin haɗin ya yi min kyau, kodayake zan turo Amrah sai su yi magana.."
"Amrah? Aunty Amrah dai da na sani ƙawar Auntyna?"
Murmushi yai mata gwalo ido ta yi tana faɗin "Taɓ! Abun da mamaki wallahi to shi wancan mijin Aunty na ya alaƙarku yake da shi?"
"Alh Aminu shi ɗin Amini na ne tun yarinta komai namu tare muke yin sa" Daga haka hira ya ɓarke tsakaninsu Zaliha nata zuba mishi shirme yana murmushi.

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now