11_12

984 11 1
                                    

*♡AMNOOR...!*
A Romantic story💋

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. W. A★

Free page 11_12

Kalman innalillahi kawai Maman Nafisa take nanatawa cikin zuciyarta ganin yanda Firdausi ta faɗo kanta tana magana cikin yanayi na maye "Mama! Yaushe kika dawo hala?" Daga haka wani irin barci ne ya figeta nan ta kwanta tana sauke ajiyan zuciya hawaye ne ya sauko mata tana tir da irin wannan rayuwar bata ɗauka lalacewar da ake faɗa Fiddoh tayi ya kai har haka ba, Duk wannan halin da ta tsinci kanta ita da ƴaƴanta mijinta ne silar komai yanzun da tana zama tare da yaran suna wuni da haka bata kasance ba amma babu yanda za'ayi ta zauna saboda da aikin ne suke samun ɗan abinci.

Kyakkyawan siririn fuskanta ne ya ci gaba da yi mishi gizo miƙewa ya yi zaune tare da kunna hasken ɗaki kallon agogo ya yi nan ya ga ƙarfe ɗaya saura na dare toilte ya nufa tare da yin alwala ya fito ya shimfiɗa Sallaya nan ya fara jero filfilu sai da ya yi Sallar subayi kafun ya kwanta nan barci me nauyi ya ɗauke shi takwas da ƴan mintuna ya farka sharp sharp ya yi wanka shadda mai ruwan goro wanda ya ji aiki gaba da baya ya saka, Ya na cikin fesa turare aka turo ƙofar bai juyo ya kalleta ba domin a ƙa'ida in har ta shigo masa ɗaki ba tare da sallama ba bai cika kulata ba, Shuru ta tsaya zuciyarta na zafi ganin yanda yai kamar bai ganta ba. "Wannan kwalliyar fa duk na menene?" Ta faɗa tana tsura mishi ido domin ba ƙaramin kyau ya yi ba, kayan ya fitar da kyawunsa sosai sai dai fuskan nan nasa a ɗaure ya ke tamau tare da ya kalleta ba ya ɗauki wayarshi tare da mukullin mota ya fito biyo shi tayi tana faɗin "Aminu magana fa nake maka!"
"Kin shigo min ɗaki batare da kinyi sallama ba, Bayan haka baki gaisheni kinyi min ya jiki ba amma kin iya tu sa ni gaba kina tambayar kwalliyar na menene? To Aure zan ƙara kwanan nan kiji da kyau! Kuma wallahi na kuma ganin kin shiga lamarin nan zanyi mugun saɓa miki"
"Ni kake kallo cikin ido kana faɗa mun Aure zakayi kwanan nan? Okay Allah ya bada sa'a ayi mu gani idan tuna na hura wuta mtsss" Ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsaki ɗan murmushi kawai ya yi sannan ya zauna yana shirin yin breakfast.

Nuriya ce ta miƙe tare da ɗaukan tiren gyaɗarta kallon Maman su tayi kana tace "Maman mu na ta fi" Gyaɗa mata kai kawai tare da faɗin "Allah ya bada sa'a don Allah kar ki daɗe kin ga yamma tayi sosai" Fita tayi tana faɗin "In Sha Allahu" Kallon Emanuel dake tsaye yana shafa tumbin sa tayi kaman zata fashe da kuka domin daga shi sai ɗan guntun gajere wando kuma ya tare hanyar da zata bi ta wuce "Nure ina binka kana ta wani kakkaucewa daɗi fa zamuji kuma wallahi zanyi duk abinda zaka ji farinciki abun nan daɗi ne da shi babu wani wahala idan nayi ma ke da kanki zaki dinga zuwa kina buɗe min legs ina shiga muna jin daɗi" Ya ƙarasa maganar tare da washe baki yana shafa wandon sa domin har ƴar bananan na shi ya fara motsawa "Dan Allah Emanuel ka ƙyaleni na ce maka ni ba ƴar iska ba ce bazan taɓa yin wannan ƙazamin rayuwar ba.." Shuru tayi sakamakon ganin mahaifin ta ya shigowa "Ke dalla can shashasha ki bashi haɗin kai zai fi miki da wannan wahalar tallar da kike, Tnda ke Allah ya yi ki mai baƙin jini baki da mashinshini tunda shi ya ji ya gani ba sai ki bashi ba?" Ware ido ta yi a razane ta ja da baya domin bata taɓa zaton jin wannan furucin daga Baban su ba, Wani shegen dariya Emanuel ya yi ganin yanda lokaci ɗaya ta tsure raɓa su ta yi ta wuce tana jin Mahaifinta na faɗin "Wallahi kwanan nan zanyi sadaka dake kina niman shekara ashirin babu wanda ya yi ko da sallama"
"Ina kuwa wani zai yi sallama da yaran ka, Ko ka manta halinka na sace-sace da caca ne? Ta ya kake tunanin wani zai dube mu da mutunci kai da kanka kake bata damar gurɓata rayuwar mu Allah wadaran Uba irin ka turr da halinka" Fiddoh ta faɗa tana hararan su, Washe baki ya yi yana faɗin "A'a Fidausi yaushe kika zo nan?" Wani kallon banza ta watsa mishi sannan ta shige cikin gidan.

** *** ***

"Yawwa Hisham ka ga wancan ita ce yarinyar wancan mutumin daya ɗauki sarƙa a shagon, Duk cikin yaran na shi ita ce nutsattsiya ƙanwarta kuwa lalacewar nata ya fi haka dan last week na haɗu da ita a bikin birthday ɗin Haiydar in kaga yanda Fiddoh take da maza abun babu ƙyan gani yarinyar ta lalace da yawa kuma Uban ne duk ya ɗora ta wannan harkan dan biyan wani inyamuri ya yi akan ya fasa mishi ita, Daga haka fa yarinyar ta mayar da maza kamar rigan sakawa duk wanda ya yi mata harka take da shi kamar mayunwaciya haka take da Namiji.."
Dakatar da shi Hisham ya yi ta hanyar faɗin "Ni ina ruwana da wani rayuwarsu kawai ku faɗa min abunda zamuyi wanda zai baƙanta mata dan bazan bar 500k ya tafi a banza ba, Dole nayi wani abun" Gyaɗa kai ɗayan abokin na shi ya yi tare da tsurawa Nuriya ido yana ƙarewa halittar ta kallo duk da cikin ƙaton hijjabi take haka bai hanashi ganin yanda manyan mazaunanta suke motsawa ta cikin hijjabin ba "Ka bar komai a hannu na yan faɗa maka yanda za a yi" Duk zuzuta kyawunta da suran jikinta da suke Hisham bai kalli Nuriya ba, Hankalin shi na kan wayar shi, Haka suka gama surutu tare da tsara abunda zasu mata.

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now