36.

317 5 0
                                    

*♡AMNOOR...!*
Romance Story.

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
      ★F. J.W. A★

Page 36.

*Domin ki ƙanwaty, Maryam Usman Turare much luv dear. Wannan page naki ne.*

Subscriber My YouTube channel Muna ɗora littafanmu a can.   https://youtube.com/@farinjinihausatv.5609?si=4jZwznZJHugMg4VU

Saboda tsananin takaicin abin da Suhaima ta yi kasa tuƙa motar ya yi. Abban Amrah shi ya amsa yana tausar shi a kan ya yi haƙuri, “Ka san ɗan yau, ka haifeshi ne ba ka haifi halinsa ba, dan Allah ka danne wannan fushin naka...” Dakatar da shi Alhaji Aminu yai zuciyar shi na wani irin ƙuna “Kamar ni da girmana, da mutuncina, a ce kullum ina hanyar karɓo Suhaima a police station? Wannan yarinyar ta isheni! Karatu taƙi ta mayar da hankali ta yi shi, ba damuwa ba dai aure take so ba? Zan yi mata tun kafin ta ɗauko min abin kunya, tun kafin ta watsar min da mutuncina a idon jama'a zan aurar da ita” Hon Sa’id dai shuru yai mishi domin idan Aminin nasa ya ɗau zafi ba ya jin lallashi. Haka suka isa station ɗin. Cikin girmamawa 'yan sandan suka shiga kawo gaisuwa tare da musu jagora wurin mai gidan nasu. Suna fitowa Abban Amrah ya ce a sake su duka. Haka aka buɗe su suka fito, kallo Dalil ya yi rai a haɗe ya ce “Ka zo gida ka same ni” Sunkuyar da kai Dalil ya yi zuciyar shi na bugawa da jin furincin Alhaji Aminu. Fiddoh kuwa ba abin da take sai kallon Alhajin tana zabga uban murmushi. Ko zafin bakinta da ke a fashe ba ta ji domin ganin Alhaji Aminu da jin muryan na shi ya tafi mata da raɗaɗin komai farinciki take ji a ranta tare da wani irin shauƙi. Kallon Suhaima ta yi tare da  lashe baki harda lumshe ido ta yi kana ta ce “Sexy guy...” Naushi Suhaima ta kaiwa bakinta sai dai kafin hnanun nata ya isa Fiddoh ta riƙe tana mata wani irin banzan kallo, “Ki shiga nutsuwarki domin na kusan zama Maminki, zan auri mahaifinki dan shi ne murdin raina, shi ne mafarki na, kuma farincikin rayuwata” Cikin ihu da jin zafin furucinta Suhaima ta ce “Shashasha ki ma daina wannan tunanin domin fasiƙa ƙazama mara asali  irin ka ba ta da gurbi a gidanmu, Uban ki ma ɓarawo ne  an gaya miki ban da labarin ki ne? wallahi tallahi kika sake irin wannan maganar saina illata ki!” Riƙe haɓa Hon. Sa’id ya yi yana kallon ikon Allah, Alhj Aminu kuwa wani ƙazamin kallo ya watsawa Fiddoh tare da jan dogon tsaki ya fisgi hannun Suhaima suka fita. Da sauri ta biyo bayansu tana faɗin “Koma dai mene ne saina mallake...” Ba ta ƙara sa maganarta ta ba Abban Amrah ya tari numfashinta da faɗin “Hauka kike yi domin ba abin da zai yi da ballagazar karuwa irin ki, matar shi ta farko naushi ɗaya za ta miki ta ɓalla ƙasussuwan jikinki, ita kuwa Amariyarsa ba ta bar ƙofar da wata mace za ta burge mijinta ba, idan za ki je ki nema ɗan' iska irin ki gwara tun wuri ki kama hanya domin kuwa a nan kin makaro, ba ki da gurbi, kariya kawai. Kuma wallahi idan na sake samun labarin kina bibiyar shi ba za ki ji da daɗi ba” Sai da Abban Amrah ya yi mata tas sannan ya shiga mota suka baɗe ta da ƙura. Wani irin ihu Fiddoh ta saka tare da zubewa bisa guiwowinta tana sakin wani  azababben kukan da tun da take ba ta taɓa yin sa a rayuwarta ba, domin ba'a taɓa yi mata ƙazamin zagi da cin fuska irin wanda Abokin Alhaji Aminu ya yi mata ba. Ta yi kukan da tun da take a duniya ba ta taɓa yin irinsa ba, sannan ta kama hanyar gida tana shiga gidan ta faɗa jikin Maman su da ke zaune tana aiki “Subahanallahi Firdausi! Me ya samu fuskar ki? Wa ya taɓa min ke? Wa ya saka ki kuka?” Lokaci ɗaya Maman su ta jero mata wannan tambayoyin, cikin wani irin sheshsheƙan kuka me shiga jiki ta ce “Maman mu faɗa muka yi da yarinyar Alhaji na, Maman mu yau an ci mutuncina an yi mini zagin da tun da kika haifeni ba'a taɓa yi mini irinsa ba, Maman mu a gaban Alhaji na, amininsa ya zage ni, ya kirani da karuwa, ballagaza, ɗiyar sa ta yi min gorin dangi Maman mu wai ba mu da asali... Da sauri Maman Nafisa ta rufe bakin Firdausi hawaye na zubo mata. Cire hannun Maman tasu ta yi tare da faɗin “Akwai wanda ya isa ya kaucewa ƙaddarar sa ne Maman mu? Ba yin kaina ba ne! Zuciyata ce take son shi,  ko laifin ne dan na so shi? Wallahi Maman mu ina son Alhaji sosai ban taɓa jin zafi da ƙunci irin na yau ba, kuma wallahi ko dan na baƙanta zuciyar Suhaima saina auri mahaifinta, ni suka kira da karuwa! Wallahi saina addabi rayuwarsu hatta uwar ta ba zan sararawa ba” Runtsa ido Maman Nafisa ta yi tana jin zafin abin a zuciyarta musamman ma kalmar *Karuwa*. “Ki yi haƙuri Firdausi, ki fita rayuwar... Miƙewa Fiddoh ta yi zaune tare da harɗe ƙafafunta tana faɗin “Wallahi tallahi ba zan barsu ba, muddin da rai a jikina saina addabi rayuwar Alhaji kuma saina aure shi” Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata. Matsowa Zaliha ta yi jikin Maman Nafisa tana sauke ajiyan zuciya domin ita ma abin da aka yi wa 'yar'uwatata ya taɓa zuciyarta tagumi ta yi tare da faɗin “Ina danginmu suke? Mu 'yan asalin ina ne? Domin ni ma an sha goranta min kuma har gobe ana yi mini gorin dangi dan Allah Maman mu ki faɗa mana” Juyar da kai Maman Nafisa ta yi tare da faɗin. “Na so a ce Nuriyya  na daga cikin waɗanda za su saurari wannan labarin”.
****
Mutanen Bangaran ( Makiyayan shanu ) ko Larabawan Chadi rukuni ne na ƙabilun Afirka a yankin Larabawa  da ke zaune a yankin Sahel na Afirka musamman tsakanin tafkin Chadi da kudancin Kordofan, wanda suke da mutane sama da miliyan shida. Ana kiran su Bangare a Sudan, Abbala, da Har ila yau, an san shi a gabashin Chadi da iyal DJINED  da kuma Shuwa Arab a Kamaru, Najeriya da yammacin Chadi. Kalmar Shuwa ance ta samo asalin ne daga yaren Kanuri. 

AMNOOR 💋Where stories live. Discover now