chapter 29

245 37 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

        RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

29🍎

Qaran da yaji ne yasa shi farkawa a firgice, cikin tsawa yace
"Who the hell is this?"

Sharan ta take hankali kwance, ta kashe vacuum cleanern ta juyo tana kallon shi har yanzu idanun shi a rufe yake.
"Shara fa nake yi k....."

"You are fired, ki fita na Kore ki a aiki"

Tabe bakin ta tayi ta kunna cleanern taci gaba da aikin ta.

"Baki ji abin da nace bane? Ya fada hade da bude idanuwan shi ya zuba su akan ta.

Kwata_kwata ya manta da akwai halittar ta cikin gidan, dafe kanshi yayi Yana Jin Yanda yake Masa ciwo saboda tashin shi a barchi da tayi.

Tana gamawa ta qaraso gaban king sized bed da yake zaune akai tace
"Ka tashi na gyara gadon kaji?"

"Feenah why are you disturbing my peace? Me yasa ko yaushe idan kina tare Dani bani da kwanciyar hankali ne? Yanzu a cikin gida na ma ba Zaki barni na kwanta na huta ba?"

Turo Baki tayi tace
" Gari fa ya waye yanzu kusan qarfe 8:00 barcin mene Kuma zakayi?"

Rafka uban tagumi yayi cike da takaici yace
"I hate you Feenah"

Saida tayi wani murmushin Jin Dadi kafin tace
"I hate you too Mr arrogant"

Tashi yayi a zabure ya yaye duvet dinda yake lullube a ciki ya sauqo ya fara tunkaro ta Yana fadin
"Me Kika ce?"

"Kaifa ka fara cemin you hate me shine Nima na fada maka abin da ke chikin zuciya ta" ta fada tana tafiya da baya.

Yaci gaba da nufo ta still tana ja da baya
" No me Kika fada after that?"

Kamar zatayi kuka Dan ta tsorata da yanayin shi tace
" Nifa kawai cewa nayi I hate you Mr arroga....." Tayi saurin rufe bakin ta da tafin hannun ta Dan sai yanzu qwaqwalwar ta ya hasko Mata barnan da tayi.

Girgiza Kai take yi tana neman afuwan sa, yana tunkaro Ta tana tafiya da baya sai jinta tayi tayi tuntube da wani qaramin table, tayi baya zata Fadi da azama ya riqo ta.

Runtse idanuwan ta tayi tana jiran ta jita timm a qasa amma shiru, Ahmad kuwa zuba mata idanuwa yayi Yana qarewa fuskar ta kallo,'she is damn beautiful' ya fada cikin zuciyan shi.

Feenah da taji ta a hannun mutum ta bude idon ta sukayi Ido hudu da Mr arrogant ya zuba Mata na mujiya.

Murguda Baki tayi tace "da'alla sake ni"

Ya tabe baki hade da fadin "ok "
Ba tare da ya dago ta ba ya sake ta ta sake yin qasa data Fadi ya riqo ta, a garin haka shima tsantsi ya debe shi dukan su biyu suka yi qasa.

Ta saki ihu Ta Fadi a Akan hannun shi da ya riqo ta shi Kuma ya Fadi a kanta.

Dane Mata Baki yayi da yatsan shi yace
"Yi shiru kada ki fasa min dodon kunne"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now