chapter 34

285 37 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

34🍎

5:10am

Ya farka hade da sauqe idanun shi a Kan fiskar ta, murmushi ya sake ganin Yanda take shaqar baccin ta hankali kwance, ya tashi ya bude bedside drawer ya dauko shopping bag din da ya shigo da shi jiya ya saka hannun sa a ciki ya fito da wani qaton macijin roba idan ka kalle shi ba zaka taba cewa ba na gaske bane, ya tsaya daga gefen ta kadan sannan ya fara Kiran sunan ta a hankali.

"Feenah! Feenah!!"
Bude idon ta take yi tana rufewa don barci ba Gama sake ta ba, Yana ganin haka da sauri ya sake Mata macijin a Kan fiskar ta.

Ihu Mai tsananin qara ta kurma ta  tashi tsaye a Kan gadon tana kaiwa macijin duka da throw pillows dake Kan gadon, gaba Daya ta rikice tana qoqarin sauqa daga Kan gadon Amman ta kasa, da qyar ta samu ta sauka a guje ta fita daga dakin tana arta a guje.

Ganin da gaske ta Kai maqura wurin tsorata gashi ta fita da rigan barci a jikin ta, yasan ana fitowa daga sallan asuba maids din gidan dasu shigo su fara ayyukan su, da sauri shima yabi bayan ta Yana Kiran sunan ta Amman inaa Feenah gudu kawai take zabgawa tana kuka.

Duk girman gidan cikin abinda baifi 5 minutes ba ta zagaye shi sannan tayi hanyar kofar main parlor, jijjiga handle din take da iya qarfin ta ta kasa budewa, a lokacin ta tuna da tasan pin din budewa ta fara rubutawa Amman wrong pin yake gwada Mata, tanayin five attempt duka ba dai_dai ba gaba Daya security systems na gidan suka fara alarming danger.

Gudu Ahmad ya qara ya nufo ta don yasan babu babu Bata lokaci securities dasu shigo su duba abin da ya faru, ya riqo hannun ta Yana kallon cikin Idon ta yace
"Calm down Feenah babu abin da zai same ki, come back to your senses please"

Wani razanannen ihu ta sake da ta kalli fuskan shi, ganin Bata Gama guduwa daga maciji ba ta hadu da aljani saboda har yanzu wuri da duhu Dan ko fitowa daga sallar asuba ba'ayi ba gashi babu wani haske sai Jan wutan danger alert a take ta sume Masa a wurin.

Tsaki ya ja cike da takaicin ta, shi bai ga wani abin tsoro ba a Nan da har zata suma, ya ciccibota da hanzari yayi ciki da ita Dan yaji ana bude qofar.

Yana shiga ya kwantar da ita Akan bed dinshi kafin ya sauya kayan jikin shi zuwa baqar jallabiya, ya fita ya sanar ma securityn da suka shigo komai lafiya kafin suka dunguma masallaci.

A Yanda ya fita ya barta haka ya dawo ya same ta, ya debo ruwa ya yayyafa Mata, a take ta sauqe wani gauron numfashi.

Zare idanuwan ta tayi ganin ta sake dawowa dakin da macijin yake, da sauri ta yaye duvet din da ya rufe ta dashi ta sake dirqa daga gadon ta falla da uban gudu wannan karon kafin tayi Nisa ya riqo ta ya maido ta jikin shi.

"Feenah relax it's not a snake it's a toy, macijin roba ne"

Cak ta tsaya daga qoqarin kwace jikin ta daga riqon sa da take yi ta kalleshi a nitse tace
"Ya Ahmad roba fa kace? That means Kai ka sakamin?"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now