chapter 55

248 32 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

55🍎

Tana Gama fadan haka ta fita hade da rufo musu qofar.

A zuciye Ahmad yabi bayanta da sauri Feenah Tasha gabanshi tana girgiza Kai hawaye na zuba a idanunta tace
"Aa Hayaty please ka rabu da ita kada kasa kanka a cikin masifa, nasan Sarai Amrah zata iya aikata abinda ta fada, kada kabiye Mata please idan Rai ya baci ai hankali bayi gushewa, insha Allah, Allah zai karemu daga sharrin ta"

Komawa yayi ya zauna Yana haki, da qyar Feenah ta samu ta rarrashe shi ya kwantar da hankalin shi.

Washe gari tun safiya Imran da Eesher suka zo duba jikin Feenah, sun sameta tana ta hidimomin ta don jikin da sauqi sosai, tsaki Amrah taja da tahango su daga sama tayi qoqarin Kora Ahmad daga gidan saboda kada ya zamo Mata cikas a plan dinta gashi ta samu qarin wasu ciwon Kan.

Tana ganin Imran ya shiga study room din Ahmad ta sauqo da sauri ta tare ma Eesher hanya, cikin nuna Isa tace
"Ke Ina zuwa?"

Saida Eesher ta watsa Mata kallon Tara saura kwata sannan tace
"Amman dai Kinga ba gidan ubanki na shigo ba ko?"

" Naji ba gidan ubana Kika shigo ba Amman fita ya zamo Miki Dole domin Nan gidan miji na ne kokuma nace gidana, sai kije ki dauki munafikin mijin ki ku fita masu tada zaune tsaye"

Dariyan qeta Eesher tayi tace
" Allah sarki, su ba saban ba Dole ki nuna Mana halin kanta waye, Kuma na rantse Miki da Allah Kika sake fadan wani mummunan kalma Akan miji na saina zubar Miki da haqwara aljana Mai zubin dawaki kawai" ta angijeta ta Fadi a qasa sannan tawuce bedroom din Feenah kanta tsaye.

Haka Amrah tayi ta jira sai yamma liss kafin su Imran suka fito zasu tafi, Feenah tabada Abdallah a hannun nannyn shi ta fita raka su Eesher, bayan mintuna kadan sai gata ta dawo Amrah Bata lura Ahmad na bayan ta ba tayi ma wani ma'aikacin gidan alama sannan ta wuce dakin ta babu Bata lokaci ya sake igiyan chandelier a daidai saitin kanta.

Da gudu Ahmad ya jawota gefe da qarfi dukan su suka Fadi a qasa, Feenah ta runtse idanun ta tanajin qaran fashewar chandelier, ga glass din jiki sun fettu a qafan Ahmad sunji Masa ciwo saboda shine a saman Feenah.

Bayan komai ya lafa Feenah ta bude idanuwan ta tana kallon Ahmad tare da sake Masa qayatatten Murmushi tayi Masa peck a cheeks tace
" You are my saviour, nasan babu abinda zai taba cutar Dani matuqar Ina tare dakai, ka tuna lokacin da mota ya kusan bigeni a Chicago?" Murmushi ya sakar Mata ba tare da yace komai ba taci gaba da cewa
"A ranar ka sadaukar da rayuwar ka domin tawa rayuwar, yauma ka ceci rayuwata na gode sosai Abban Abdallah I love you"

Peck yakai mata a lips yace
" I love you too ummin Abdallah yanzu dai muje a duba waye yayi Miki wannan danyen aikin, ko wanene shi yau sai yayi nadamar aihuwan shi cikin duniyar nan"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now