1

203 3 0
                                    

Bismillahir rahamanir rahim wa sallallahu allan nabiyyil karim wa ahlihi wa sahbihi wa sallam.

Dukkan godiya ta tabbata gun Allah sarki guda daya mai kowa mai komai wanda ya bani ikon rubuta wannan littafin mai suna HAWA DA GANGARA Ban rubuta wannan labari don cin zarafi ko batanci ga kowa ba idan ma kaga wani waje yayi ma da wani abu da ya shafeka clash aka samu.

Ban yarda wani ya juya wannan labari ta kowacce siga ba tare da Izinina ba.

*Daga Kundin✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
*wattpad@KhamisSulaiman*

*Page 1*
Yasir da Yasira da Mas'ud suna tafiya a mota cikin farin ciki da annushuwa, Yasir da Mas'ud suna gaba, yasira tana baya tana karanta littafin notebook na makaranta.
Yasir ya Kalli Mas'ud, yace "Mas'ud wai yaku kayi da budurwarka Rahman ne? banji kace min komai ba"
Mas'ud yayi tsaki sannan yace "Babanta yace bai amince ba, ni kuma nace in dai haka ne nima na hakura da ita!"
Yasir yace "To ko dama bata sonka yaudararka zatayi"
Mas'ud yace "Kamar ka shiga zuciya ka gani abinda nake tunani kenan naji ma fa ance wai an musu baiko da wani dan kawunta, sunyi min haka ne dama don nace haka abin ya lalace"
Yasir yace "Tunda har ka ji haka ai daka sani cewa kayi ka amince don kaga yadda zasuyi"
Mas'ud yace "Ta yaya zan bari a dinga bata min lokaci bayan na gane gaskiya"
Yasir yace "Da dai kayi hakan"
Mas'ud ya kalli Yasir, yace "Wai kai Yasir ma me yasa baka Kula kowacce mace da niyyar soyayya, ko ba zakayi aure bane? "
Yasir yayi murmushi yace "Hmn Mas'ud kenan, ta yaya ina dan aure kuma sannan naki aure? kawai dai abinda yasa nake a haka, ba wai aure bane bana so, a'a akwai Dalibin!"
Mas'ud yace "To Yasir me zai hana ka sanar dani wannan dalili a matsayina na amininka"
Yasir yace "A'a Mas'ud ka bari wani lokacin zan sanar da kai amma ba yanzu ba"
Mas'ud yace "To shikenan Yasir Allah ya nuna mana lokacin lafiya, gashi nan har Yasira tana koyi da kai ita ma ban taba ganinta da saurayi ba ko tayi zancen wani a matsayin wanda take so"
Yasir yayi murmushi yace "Kan ai dama daga na gaba ake gane zurfin ruwa"
Yasira tayi shiru kamar bata jin abinda suke tattaunawa. Kawai sai wayar Yasir ta fara ringing sai ya dauka ya daga yana cewa "Hello Dr. Karim lafiya kuwa"
Dr. Karim ta cikin waya yace "Dr. Ra'is ne yace yana son ganinka yanzu yanzu."
Yasir cikin tashin hankali yace "Lafiya kuwa Dr. Karim? Ya mai jikin nan?"
Dr. Karim ta cikin waya yace "Eh lafiya dai da sauki, kuma kiran naka ma da yake yi akan ita patient din ne"
Yasir cikin sauri yace "To shikenan gani nan zuwa, dama zan kai kanwata makaranta ne son kashe wata wuta data tashi, amma bari mu fara zuwa nan idan muka gama da wannan matsalar sai mu wuce."
Dr. Karim ta cikin waya yace "To shikenan sai ka karaso" sai ya kashe wayar.
Mas'ud ya kalli Yasir, yace "Lafiya kuwa?"
Yasir yace "Kafin muje makarantar bari mu fara zuwa dubiya asibiti"
Mas'ud yace "To shikenan"
Yasir ya kalli Yasira, yace "My only sister kiyi hakuri zamu dan shiga lokacinki kadai."
Yasira tayi murmushi take "Haba yaya ai ko cewa wai barawo a hannun mata."
Yasir shima yana murmushi yace "Bare ma ba zan taba cewa ba" suyi dariya gaba daya.

Yasir kyakkyawan saurayi ne jar fata mai doguwar fuska, yana da siririn hanci da madaidaicin baki, ga dara daran idanu, matsakaici ne shi ba dogo ba shi ba gajere ba, kakkarfa ne mai madaidaicin jiki shi ba siriri ba shi ba mai kiba ba, kuma shekarunsa talatin da biyar kusan shekarunsu daya dana amininsa Mas'ud. Yasira itace kanwa daya tilo ga Yasir, idan kaga Yasir kaga Yasira don kamarsu daya kamar an tsaga kara, suna matukar kaunar junansu da soyayyar yan'uwantaka mara tamka.

Motarsu kai tsaye cikin Apexwell private Hospital ta shiga, suka je motorbike suka yi parking sannan suka shiga cikin asibitin, suna tafiya sun kusa zuwa office din Dr. Ra'is sai suka hadu da wani babban mutum shi da 'ya'yansa da kuma securities dinsa, kawai sai mutumin ya mikawa Yasir hannu suka yi musabaha.
"Baka ganeni ba ko?"
"Gaskiya ban ganeka ba"
"Ba kai bane Yasir tsohon shugaban kamfanin Abdussattar & Sons constructions & technology Co.?"
" Eh nine "
" Sunana Alhaji Mansur Ilyas Walid shugaban kamfanin Walid Artistic Constructions Development Co."
Yasir yayi murmushi yace "Oho! ban ganeka ba sai yanzu"
Alhaji Mansur yace "Na dade ina nemanka tun bayan barinka kamfaninku, ina son yin wata magana mai muhimmanci da kai amma naga kamar sauri kake"
Yasir yace "Eh wallahi zamu duba wata mara lafiya ne"
Alhaji Mansur yace "To shikenan, nima dama nazo duba wani kawuna ne, amma me zai hana idan ka samu lokacin ka ziyarceni domin mu hadu mu tattauna"
Yasir yace "To shikenan ba matsala"
Alhaji Mansur yace "To sai na ganka"

Suka yi masabaha sannan kowanne ya wuce, su Yasir suje office din Dr. Ra'is su sameshi shi da Dr. Karim, bayan sun gaisa sai Dr. Ra'is ya jasu su tafi cikin I.C.U. su tsaya a bakin kofa suna leka wata mara lafiya ta glass wacce ke kwance tamkar matacciya.
Yasir ya kalli Dr. Ra'is da Dr. Karim, yace "Wai har yanzu babu wani sauyi?"
Dr. Karim yace "Bama wannan ne matsalar ba muna jiye mata shiga comma water doguwar suma!"
Dr. Ra'is yace "Ina son sanin dalilin shigarta wannan hali, shine makasudin kiranka, ta haka ne zamu shawo kan matsalar cikin ikon Allah"
Yasira da Mas'ud su hada baki wajen cewa "Wai ita wannan din wacece ita?"
Yasir yace "sunanta Yusrah itama kuma kanwata ce kamar yadda kike" ya fada yana nuna Yasira.
Yasira da Mas'ud suyi saurin kallonsa cike da mamaki da al'ajabi.
Dr. Ra'is yace "Mu koma office muyi magana a can."

*Alkhamis KSA*

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now