4

31 3 0
                                    

               HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                           *page 4*

   Sai ta zuba mana abinci ni da 'ya'yanta maza biyun nan, sannan ta karbi Yasira daga hannuna a take ta fara shayar da ita.

   Tun daga wannan rana na manta da maraici da kadaici na manta da wahala da kuncin rayuwa.

Wannan mutumi shine Alhaji Abdussattar da matarsa Badrah sai 'ya'yanta babban Zayyad da kaninsa Dayyab sai jaririyar kuma Shukrah.

  ZAMANMU A GIDAN ABDUSSATTAR

   Da muka je garinsu muka sauka daga jirgin kasa nan kai tsaye gidan Abdussattar muka wuce, gida ne babba na masu rufin asiri wadanda suka fi karfin dukkan bukatunsu akwai 3 bedrooms kowanne da toilet a cikin sannan ga wadataccen parlor, a gefe kuma ga dining room mai cin mutum takwas da kuma kitchen da wani toilet din duka parlour.

    Washe gari Alhaji Abdussattar ya daukeni ya kaini boutique ya siya min suttura da takalma da huluna da hiramai da dai sauran kayayyakin ado aka zuba min a cikin sabuwar wardrobe dina dake dakinsu Zayyad da aka siyo min tare da wani karamin gado daidai ni, kai duk wani abu da zan bukata na rayuwa sai da aka siyo min.

    Sannan aka sani a makarantarsu Zayyad aka kaini primary 2, a lokacin Zayyad yana nursery 4, shi kuma Dayyab yana nursery 2. Sannan aka sani a makarantar islamiyya wadda 'ya'yan gidan suke zuwa, Allah ya bani basira don ina da kokari sosai a kowacce makarantar da nake yi don haka nayi fice a dukkan Makarantun biyu, wannan yasa malaman suke sona, iyayenmu ma suka kara kauna a cikin zuciyarsu.

     Alhaji Abdussattar Architect ne kuma Engineer yana zanen gidaje kuma yana kirkira a harkar Technology yana aiki da wani babban kamfanin dake babban birnin kasar a matsayin mataimakin shugaba.

     Yasira da Shukrah shekarunsu bibiyu a duniya aka yaye su, tunda nake ban taba ganin yara irinsu ba, babu ruwansu da kuka ko rigimar yara ta yaye koda yaushe a zaune suke ba ruwansu da barna ko kurun kurun irin na yara.

    Ganin haka yasa baban namu Abdussattar yake tunanin wadannan yara ko basu da lafiya ne saboda dukkan yara ba haka suke ba, yayi la'akari da lokacin da Zayyad yana yaro fitinarsa da barna da kiriniya ai ba magana sai da ya addabi kowa kuma duk wasu kaya komai amfaninsu haka yake lalata su. To haka ma lokacin da Dayyab yana yaro shima fitina da barna kuma idan aka hanashi ya dasawa mutane kuka.

    To ganin Yasira da Shukrah su basa irin wannan sai aka kai su asibiti wajen wani babban likita, duk wani bincike anyi amma babu wata matsala, likita yace suna cikin kashin lafiya babu abinda yake damunsu kawai su a haka Allah ya haliccesu, suna da hakuri da juriya.

   Shekararmu uku a gidan babarmu Badrah ta sake haihuwa ta samu da namiji ranar suna aka rada masa suna Zayyan, a lokacin ina primary 4 a makaranta su kuwa Zayyad da Dayyab anyi musu repeating har sau biyu saboda rashin kokari Zayyad a nursery 5 yake shi kuma Dayyab a nursery 3.

    Wata rana muna makaranta a cikin ajinmu ni da abokaina muna karatu da debate a tsakanin mu dama haka muke yi idan babu malami a ajin. Muna zaune kawai sai ga Zayyad da Dayyab sun shigo ajin suna kuka, shi Zayyad an fasa masa hanci shi kuma Dayyab an fasa masa baki dukkansu sai zubar da jini suke, na tashi cikin sauri na tare su ina tambayarsu waye yayi musu haka suka ce min Ammar ne, ina jin haka sai na kama hannunsu na jasu muka tafi wajensa.

    Ammar wani fitinannen yaro ne a makarantar mu azzalumi ne kuma mugu yana cutar da yara sosai shi yasa yara suke tsoronsa, kuma da ganin ake shagwaba shi don kwata kwata bashi da tarbiyya.

    Muna isa wajen Ammar na tambayeshi me suka yi masa da har ya kai shi ga yi musu irin wannan mummunan hukuncin, mai makon ya bani amsa sai yayi min gatsali da gadara, ni kuwa kawai sai na shakoshi na dinga duka da kyar aka kwace shi aka kaimu wajen Displine master ya tambayi me yasa na dakeshi, nayi masa bayanin komai sannan aka kira Zayyad da Dayyab don tabbatarwa, bayan an tabbatar aka tambayi Ammar me suka yi masa nan ma ya kasa bada amsa, Displine master yayi mana sulhu, Ammar da Zayyad da Dayyab aka kaisu Dispensary aka yi musu Treatment sannan ni da Ammar kuma aka yi fada sosai akan daukar hukunci a hannu.

    Bayan mun fito daga office din Displine master sai Ammar yake zagina yana cewa wallahi ba zai yarda ba, ni kuma na hau dokin zuciya na sake lallasa shi aka sake mai damu office din Displine master aka tambayemu.

  Displine Master yace "Baku aka kawo yanzu ba don kun ga ban zaneku ba shine ku ka sake yin fadan ko?"

Nace "Shine yake zagina kuma yace ba zai yarda ba duk da hukuncin da kayi!."

  Displine Master yace "To me yasa baka zo ka gaya min ba? ko ba yanzu nayi muku kashedi akan daukar hukunci a hannu ba?" nan aka rarrankwashe mu aka koramu aji.

   Da aka tashi bayan mu isa gida na sanar da iyayenmu abinda ya faru nan ma aka yi mana fada, musamman ma su Zayyad da Dayyab don Abbanmu yace basa ji ta yiwu ma su suka takale shi, ni kuma nace a'a cin zali halin Ammar ne kowa ya school yasan halinsa, aka dai yi mana fada sosai.

   Da gari ya waye muna tashi sai naga fuskar Zayyad ta kumbura tai suntum idonsa yana neman rufewa, shi kuma Dayyab lebensa ya kumbura sai raina ya baci na hasala ai kuwa muka shirya muka tafi makaranta, muna zuwa muka ci dako a bakin gate Ammar yana zuwa na fara dukansa ba kawai ba gani da kyar aka kwace shi, aka kaimu wajen Displine master.

   "Ku baku aka aka kawo jiya kunyi fada ba shine yau ma ku ka sake yi don kunga ban zaneku ba ko?"

   Ya kalleni yace "Me ya sake hada ku?"

    Nace kirawo Zayyad da Dayyab na nuna masa su nace "Kalli yadda yayi musu da fuska, shikenan kuma sai ya ci banza!"

    "Kai fadanka baya rabuwa ne? da ban sanka da haka ba"

    Nan take ya aika aka kira iyayenmu maza ni da Ammar aka yi mana sulhu na karshe aka ce duk wanda ya sake yin fada to wanda ya fara takalar wani an koreshi.

   Da muka koma gida sai naga kamar ran iyayenmu ya baci, don haka sai na bari sai da suna zaune a tare sannan naje na tsuguna a gabansu na basu hakuri dangane da abinda ya faru, sunji dadin hakan sosai suka ce dama ba laifina bane Zayyad da Dayyab ne sila. Don haka sai aka sauya min makaranta ni kadai, su kuma aka barsu a can, su Yasira da Shukrah ma aka sasu a makarantar da nake don haka sai muke tafiya tare.

   A shekarar dana gama primary na shiga junior secondary school a shekarar babarmu ta sake haihuwar da namiji ranar suna aka sani masa suna Rayyan, haka muka cigaba da zama a gidanmu cikin jin dadi da kwaciyar hankali da zaman lafiya.

  RAYUWAR A GIDAN ABDUSSATTAR

*Alkhamis KSA*
   
 

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now