2

49 4 0
                                    

            HAWA DA GANGARA

*Daga kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
wattpad: @KhamisSulaiman

                     

                          *page 2*

         Sai su tafi office din gaba dayansu suje su zazzauna.
       Yasir ya kalli Dr. Ra'is, yace "Labarin Yusrah hade yake da labarinmu ni da kanwata Yasira, idan kana son sanin abinda ya sameta yana da kyau kasan labarinmu."
        Yasir ya kalli Yasira, yace "Kin dade kina tambayata labarin iyayenmu, to yau zakiji asalinmu."
        Yasir ya kalli Mas'ud, yace "Dazu da muna tafiya a mota kace tambayeni me yasa bana kula 'yammata da niyyar soyayya ko ba zanyi aure ba, kuma kai da Yasira kunga Yusrah kun tambayeni wacece ita? to duk zakuji amsoshin tambayoyinku" sai ya fara basu labarin:
                        IYAYENMU
     "Iyayenmu 'yan ci rani ne duk da cewa ban san daga garin da suka zo ba, amma dai nasan 'yan kasar nan ne, kuma iyayenmu mu biyu ne kawai 'ya'yansu daga ni Yasir sai kanwata Yasira. Iyayenmu suna zaune a wani gida dake cikin wani dan karamin kauye suna zaman haya.

Sana'ar mahaifinmu ita ce yin ice da ciyawa yana siyarwa yana nemo mana abinda zamu ci, kullum haka yake yi tun fitowar rana har zuwa fadakarwa, bashi da wani mataimaki sai Allah. Mahaiyarmu kuma bata da wani aiki sai dai kullum ta ringa yin wankin kayan masu hali ana biyanta, sannan ga kula damu da kula da gida da 'yan aikace aikacen gidan, idan lokacin biyan kudin haya yayi sai su hada gwiwa su biya.

     Wata rana mahaifin namu yaje daji yin ice da ciyawa kamar yadda ya saba sai maciji ya sareshi, ya dawo gida yayi ta jiyya, ya zamana mahaifiyarmu ita take kula damu gaba daya, ita take nemo mana abinda zamu ci, ana haka har lokacin biyan haya yayi gashi bamu da komai a ajiye, da masu gida suka tambayi kudi babu kawai sai suka tashemu, muka tashi muna ta gararamba har Allah ya bamu wani gidan hayar, muka zauna muka cigaba da rayuwa.

   Muna zaune a haka har mahaifinmu ya warke ya koma sana'arsa ta yin ice da ciyawa, ita kuma mahaifiyarmu tana yin wankau din data saba, ana haka sai damina ta wuce ciyawa ta kare sai dai ice, muna nan kwatsam wata rana aka yi shela cewa duk masu yin ice a wannan gari su saurara saboda ance idan itacen daji ya kare wata rana sahara zata gangaro ta mamaye wurin.

     A haka dai aka hanasu yin wannan sana'a tasu ya dawo gida da zama, wata rana yana zaune sai mahaifiyarmu take cewa da mahaifinmu "Kaga da wannan zaman da idan an kawo min wanki sai mu dinga yi tare, idan an bada kudin sai muyi hidimar gida dasu, idan wasu sun dan ragu sai mu adana saboda wataran"

    Haka kuwa aka yi suka hada karfi da karfe wurin yin wannan wanki, cikin ikon Allah kuwa a shekara guda sai gashi sun tara kudi masu yawa, dama ai ba maraya sai rago kuma Allah ma da kansa yace tashi in taimakeka.

           MUTUWAR IYAYENMU
    wata ranar talata ba zan taba mantawa ba muka wayi gari wasu da ba'a san ko su waye ba suka yiwa iyayen namu yankan rago gaba dayansu, kawai mu dai mun wayi gari mun gansu a haka, a lokacin ina dan shekara goma Yasira kuma watanta takwas a duniya, nayi kuka sosai nayi matukar bakin ciki musamman ma idan Yasira tana kukan nono nakan shiga halin tsaka mai wuya da yawan damuwa, tsananin tausayinta yakan kamani sai in San ta a gaba muyi ta kuka.

     A kwana uku gaba daya muka bi muka rame muka komade kamar wadanda suka yi shekara da shekaru suna cuta, babu wanda yake taimaka masa sai Allah. Mun shiga tsaka mai wuya, rana zafi inuwa kuna, bamu ga tsuntsu bamu ga tarko, ba ci ba sha ba gurin kwana gashi ba uwa ba uba, muka yi ta garari da gararamba a cikin gari, muyi can mu dawo muyi nan yau mu samu abinci gobe mu rasa haka ma idan dare yayi sai dai mu kwana a kasa, wuya da wahala sun zame mana ruwan dare da karfen kafa, don duk inda muka shiga babu sauki.
   
       RAYUWARMU A GIDAN SABIR
    Akwai wani malami a wannan kauye shi ya nemi alfarma a gurin wani mutum mai suna Sabir wanda ke da mata mai jego kusan lokaci daya suka haihu da mahaifiyarmu.

     Malamin ya nemi alfarmar Sabir ya kaiwa matarsa mu ta hada ta rene tare mu da nata 'ya'yan, itama Kuwait 'ya'yanta biyu namijin shine babba sunansa Mugir shekararsa bakwai sai kuma wannan jaririya tata. Haka kuwa aka yi ya kaimu gurin matarsa mai suna Bushrah ta hada mu da 'ya'yanta ta rike, Bushrah ta tsaneni ta tsani Yasira bata nono yadda ya kamata bata daukarta komai kukanta bata kwaciya tare da ita, sai dai ita da 'yarta su shige daki ita kuma Yasira a falo.

     Ni kuma bani da wani abin yi sai aiki kamar bawa, ni nake wankin kayansu dukkansu ita da 'ya'yanta, ni nake yiwa Yasira wanka ita bata mata, ni nake wanke wanken kayan abinci, ni nake shara ni nake debo ruwa nayi sharar garken dabbobi, kai in takaice muku labari ni nake yin komai na gidan, bani da wani hutu kullum abu daya.

    Wata rana ina cikin sharar garken dabbobi sai naga an shirya Mugir zai tafi makaranta, kafin ya tafi sai nayi sauri naje nace "Ummi nima ina son zuwa makarantar"

      Abinda zai fito daga bakinta shine "Wa ya gaya maka kana da wani 'yancin zuwa makaranta? meye amfaninka ban da aiki? zaka fice ka bani guri ko kuwa!"

    Ta koroni na koma kan aikina, ina yi ina kuka ina tuna iyayena nasan da sunanan da rai da baza su bari a ringa yi min haka ba, ina cikin kukanta sai gata take "Au ni zaka yiwa sharri don Sabir yazo yace dukanka nayi ko kuwa"

      "Ba haka bane"
      "Rufe min baki munafukin banza, shashasha, sakarai, kuma kayi sauri ka gama share garken nan ga wanki can yana jiranka kuma ka wankesu su fita tastas!"

     Wata rana da Sabir zai yi tafiya daga kauyen zuwa cikin birni neman kudi kuma yace zai yi kamar wata hudu, nayi matukar bakin ciki da wannan tafiya tasa domin nasan idan ya tafi mun shiga uku a garin nan da ukubar Bushrah dama don tana ganin idonsa ne take dan ragwanta mana amma yana nan din ma ya muka iya ballantana ace ba idonsa ai sai ta Allah kawai.

     Washegarin da Sabir ya tafi da sassafe ina kwance ina barci ban ma tashi ba domin yawan aiyukan da nake yi idan na kwanta to fa tashi sai dai Allah. Ina kwance kawai sai naji saukar ruwan sanyi a jikina, a razane na tashi na zura da gudu ban gani ba na bangajeta, ta kuwa rukoni ta kwada min mari har sai dana fadi kasa, ta kalleni tace "Sharar garken dabbobi tana jiranka, idan ka gama kuma ka share min tsakar gidan nan kaf, sannan ga wanke wanke can, ga wankin kayanmu ga wankin bandaki, kuma ina so kayi sauri ka gama kafin ka bata min rai, don wallahi idan ka sake bani haushi irin jiya sai na zaneka!"

    Na kalleta nace "Yanzu duk wadannan aiyukan ni zanyi su kuma ni kadai?"

   Ta daka min tsawa da cewa "Kai kadai din zaka yi meye amfaninka? banda aikin, ko kana nufin gaka a zaune zan tafi in yita aiki kuma sannan in dafa abinci in baka! zaka tafi kayi aikin dana saka ko kuwa?"

     Na wuce naje nayi sharar garken dabbobi sannan na share gidan gaba daya sannan kuma naje nayi wanke wanken kayan da aka ci abinci, sai kuma na zauna wanki nayi tayi cikin ikon Allah kuwa a kankanin lokaci na gama kuma sun fita tas, sannan nayi wankin bandaki. Sai naje nace mata "Ummi na gama"
   Tace "To shikenan"
   Nace "Ina abincina?"
   Tace "Wane abinci?"
   Nace "Abincina"
   Tace "Au dama ka bani ajiyar wani abinci ne?"
   Nace "A'a na gida fa wanda kika dafa"
    Tace " Wanda na dafa? kai na dafawa dama ko kai ka sani? to ban ajiye ba don ban dafa da kai ba, kuma ka bace min da gani!"

   Na fito daga dakin kenan na zauna yunwa duk ta dameni, sai gata nan da wata katuwar roba ta miko min tace "Karbi kaje ka debo min ruwa yanzu yanzun nan"

   Na karba na tafi ina kuka cikin ikon Allah sai na tarar da wani gida ana sadakar abinci da yake ranar juma'a ce, na tsaya na karba na ci na cika cikina sannan naje na debo ruwan na kai mata, ina shiga ta kalleni tace "A ina kaci abinci?"

            *Alkhamis KSA*

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now