14

33 2 0
                                    

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                           *page 14*

      Da daddare Yasir da Yasira da Yusrah da Shukrah da Badrah  suna cikin cin abinci sai Yasir yace " Gobe Zayyan da Rayyan zasu dawo sun gama karatun degree dinsu na daya, zasu hawo jirgin safe ne don haka da wuri zanje na dauko su a airport"

      Yasira tace "Yaya zan rakaka mu dauko su"

      Yasir yace "To shikenan Allah ya kaimu safiyar da rai da lafiya"

      Yusrah tayi farat tace "Ai kwa nima sai naje"

      Shukrah tace "Nima fa zan je yaya"

      Yasir yace "To iyayen gasa! in dai ku ka ji anyi maganar fita waje, jikinku har rawa yake ku lallai a fita da ku kamar wasu yara, idan kun hakura ai zaku gansu tunda cikinku zasu dawo da zama, ba wai baki bane, ba kuma rakasu zamuyi suyi tafiya ba, dawowa suka yi daga tafiya in ku kayi hakuri kuna zaune zasu dawo su sameku"

       Yusrah tace "A'a mu dai gara muje mu tarosu kaga ma a ce suna 'yan'uwa  masu son su"

       Yasir yace "To da wa yace basu da yan'uwa masu sonsu?"

       Badrah ta kalli Yasir tace "Kaima ka rabu dasu mana da maganar, su basa gajiya da surutu, idan zaka je dasu kaje dasu, idan kuma ba zaka je dasu ba ka gaya musu su hakura"

       Yasir yace "Yauwa Ummi ki sa masu aiki su dafa musu abinci irin wanda suke matukar so a tarbe su dashi"

       Badrah tace "In dai wannan ne ka dauka ma kawai an gama, Allah dai ya kaimu goben lafiya"

      "Amin"

      Da sassafe Badrah tasa masu aiki suka gyara gidan fiye dana kullum, sannan suka kama shirin aiki kayan kwalam na ciye ciye da shaye shaye.

      Da misalin karfe bakwai na safe Yasir ya fito da shirin zuwa ya gaida Badrah, kawai sai yaga Yasira da Yusrah da Shukrah a zaune a falo kowacce tayi kwalliya ta dau wanka, suna ganinsa sai su fara rige rige wajen gaidashi, shi kuma sai ya tsaya kawai yana kallonsu.

      Yasir yace "Lafiya dai na ganku a nan a zaune kun wani kwalliya kamar masu zuwa wajen zaben sarauniyar kyau?"

     Yasira tace "Yaya ka manta ne da dauko su Rayyan a airport jiya fa da wuri kace zamu tafi"

      Yasir yace "Au wai dama saboda zuwa Airport din ne ku kayi wannan kwalliya, don kusa idan mun je a dinga kallonmu, wasu ma suce kalli wani ya kwaso mata yana tallansu, ko tallan kanku kuke?"

       Yusrah tace "Haba Yaya wane tallan kai kuma? mu ai mun siyar tunda muka same ka, ban san ko Yasira ba itace a kasuwa"

       Yasira tayi farat tace "To nima din na siyar, sai dai ki sami wata ki gaya mata haka!"

       Yusrah cikin yanayin tsokana tace "Au kema kin siyar? to wa kika siyarwa? waye shi da bamu sanshi ba?"

       Yasira tace "Ai ba lallai bane sai kin sanshi, tunda dai ni na sanshi kuma yayi min ai hakan ma ya wadatar!"

       Yusrah tace "To! waye wannan kuwa? ko dai wannan Mas'ud din ne abokin yaya, mayen kallonki kullum idonsa yana kanki"

      Yasira tace "Idonsa yana kaina ke kuma idonki yana kansa ko, don in ba haka ba ta ya kika san yana kallona?"

      Yasir ya katsesu da cewa "Ke dahalla ku saurara"

      Shukrah ta kalli tace "Yaya jiya kace da wuri zaka je dauko su, amma har yanzu gashi baka shirya ba"

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now