3

32 2 0
                                    

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
wattpad: @KhamisSulaiman

                       *page 3*

   Nace "Ni ba wani abinci dana ci!"
   
     Ta kwada min mari tace "Karya zan maka ko a zatonka ba zan gane kaci abinci ba, ga bakinka nan duk maiko, zaka gaya min inda kaci abinci ko sai na yanka ka" ta dauko wukar da take yanka albasa tayo kaina.

Na kurma ihu nace "Sadaka aka yi" sai naji saukar wani marin a kuncina.

Tace "Saboda kana so mutane su la'anceni su ce bana baka abinci shine zaka je kana karbo sadaka to wallahi duk ranar dana kara ganinka ko naji labari, mutumin da yake cikin mai ake soyashi da ransa sai yafi ka jin dadi!"

Nace "Ba zan kara ba"
Tace "ka wuce kaje kayi yowa dabbobi ciyawa"
Nace "To" na wuce na tafi.

Dama tsakaninmu da inda ake yin ciyawa akwai 'yar tafiya, ina cikin tafiya sai na tuna na manta da igiyar daure ciyawar har na juyo na dawo sai kuma kawai na cigaba da tafiyata don nasan in har na koma wani sabon ci mutuncin ne zai biyo baya, don haka sai kawai na tafi, ina zuwa na fara ciro ciyawar kenan sai naga wata mai kyau, naje na zan ban sani ba ashe akwai maciji a labe a ina kai hannu kuwa yana sarana, na fadi kasa ina ta birgima sai ga wani mutum yazo ya ganni cikin mawuyacin hali, har daukeni sai yaga macijin da ya sareni, don haka sai da ya fara kasheshi sannan ya daukeni ya kaini gidansa yayi min magani yayi ta jiyyata, duk ban san inda kaina yake ba sai da nayi mako uku cur, sannan na warke gaba daya ya tambayeni gidan much, da kamar na ki gaya masa nace bani da kowa amma dana tuno da Yasira sai na fada masa, ya daukeni ya kaini gidan ya samu Bushrah kuwa ya bata labarin yadda ya tsiceni har yayi jiyyata.

     Bushrah tayi murna da ganinmu ta yiwa wannan mutumi godiya har da yi masa kyautar kayayyaki, shi kuwa ya ki karba, yace "Aini don Allah nayi masa wannan taimako ba don a bani wani abu ba"

   Bushrah tace "Nima na sani ba don a biyaka kayi ba kuma ma ai babu mai biyanka sai Allah, wannan nayi maka ne don jin dadin abinda kayi min kasan ance yaba kyauta tukuici"

   Yace "To na gode" ya karba yayi mana bankwana ya fita.

    A zatona Bushrah bayan batana halayenta ne suka sauya daga munana zuwa kyawawa ashe ba haka bane domin ina wannan tunani sai saukar mari naji a kuncina na gigice har zan ruga ta rikoni tayi cilli dani cikin tsakar gida tana ta fada da zage zage wai ta aikeni na gudu naje mun hada baki da wani tsohon banza, ta shiga daki ta dauko bulala ta zaneni tsaf sai data gaji sannan ta tafi ta barni anan ina ta kuka babu ko hawaye don wuya har zazzabi sai da nayi, a wannan rana ne na tabbatar da cewar jama'a Bushrah zulwajahaini ce mai yin annamimanci."

      RABUWARMU DA GIDAN SABIR
 
    Wata rana cikin dare ina kwance ina barci sai naji kukan Yasira kamar a mafarki dana farka sai naji ashe ita din ce kuwa sai naji shiru naji ko za'a dauketa amma ba'a dauketa ba ita kuma bata daina kukan ba har muryarta ta fara dashewa kawai sai na nufi falon dama na gaya muku a falon take ajiye Yasira.

  Ita kuma da diyarta suna daki ina zuwa na tarar ta kulle dakin sai na tsaya na buga na buga amma shiru kake ji kamar malam ya ci shirwa ganin haka sai na yanka shawarar na shiga ta taga na daukota haka kuwa aka yi na bude tagar na kama na hau na dira sai nayi rashin sa'a na dira akan wata tukunya wacce take dauke da man gyada a ciki na barar da man nan baki daya.

  Ai kuwa faruwar hakan ke da wuya sai ga Bushrah ta fito ta tarar dani rike da Yasira a hannu.

   Ta daka min tsawa tace "Me ka shigo yi?"
   Nace "Ji nayi Yasira tana kuka kuma ba'a dauketa ba shine na shigo don na rarrasheta"

   Ta kwada min mari tayi ball dani na fadi Yasira ma ta fadi can gefe guda, ta cakumoni tace "Wai kai mai 'yar uwa ko? shine muna Kwance zaka shigo mana kamar barawo, ko ka fara sata ne?"

    Nayi saurin girgiza kai nace "Ni wallahi bana sata!"

Tace "To tsaya nazo" ta shiga daki ta dauko fitila tana dawowa ta haska sai taga an barar mata da mai.
 
Sai ta kurma ihu tace "La'ilaha'illallhu! yanzu Yasir man ka barar min? shikenan ka sabautani ka cuceni! wallahi yau sai ka bar gidan nan a cikin daren nan ba sai da safe ba, kuma kafin ka tafi sai baka tukuici"

Ta tafi ta dauko bulala ta dinga zabga min ba ji ba gani, tun ina kuka da ihu har na fara sarewa bata kyaleni ba sai da tayi min laga laga tayi min jina jina sannan ta dauko Yasira dake kwance a kasa itama tana kuka ta cillo min ita ta koromu waje ta kulle kofar gidan.

  Ganin dare yayi sosai sai naki tafiya ko ina muka kwanta anan na cire rigata na lullubawa Yasira sai tayi barci, ni kuma na kwanta a kasa ga sauro amma a haka muka kwana har asuba ko rintsawa banyi ba.

   Ai kuwa asubar fari na dauki Yasira muka nausa daji muka yi ta tafiya har muka zo tashar jirgin kasa, muka zauna a inda almajirai suke zama suyi bara.

HADUWARMU DASU ABDUSSATTAR

  Ina zaune a tasha Yasira tana jikina har na samu tayi barci, sai ga jirgin kasa yazo mutane suka yi ta sakkowa daga ciki, sai wani mutum da matarsa da 'ya'yansa uku maza biyu mace daya kuma jaririya ce kamar Yasira, shi mutumin da matarsa da 'ya'yansa basu fito ba da alama su ba'a nan tashar zasu sauka ba, na tashi naje na leka da niyyar yin bara amma sai na kasa sakamakon abinda na gani, wani barawo na gani ya labe yana yi musu sata, ai kuwa banyi wata wata ba na sanar da mutumin kuwa ya kamashi ya kwace kayansa ya koroshi, shi kuwa barawon yana fitowa ya sameni ya kama duka sai da mutumin ya fito ya kwaceni shi kuma ya hadashi da 'yan sanda, mutumin ya kama hannuna ya shigar dani cikin jirgin ya zaunar dani a kusa dashi ga matarsa da 'ya'yansa.

   "Ya sunanka?"
   "Sunana Yasir"
   "Wannan kanwarka ce?" ya fada yana Yasira.
   "Eh kanwata ce sunanta Yasira"
   "Me kuke yi anan cikin tashar jirgin kasa?"
   "Bara muke yi"
   "To ina iyayenku?"
   "Sun mutu!"
   "To ina danginku da 'yan uwanku?"
   "Bamu da kowa, iyayenmu zuwa suka yi kuma ban san daga inda suke zo ba, a lokacin ina jariri"
   
   Ya jinjina kai cikin yanayin tausayawa yace "To idan kunyi barar kuna samun abincin?"
    
     "Wani lokacin muna samu wani lokacin kuwa bama samu sai dai mu hakura"
     
     Ya kalli Yasira, yace "To wannan kanwar taka an yayeta ne?"
     
      Nace "A'a"
     
     "To me kake bata a matsayin abinci ko itama irin abincin da kake ci kake bata?"
     
      "A'a, da wani mutum ne ya kaimu gidansa wajen matarsa itama tana da jaririya shine take shayar dasu tare, yanzu kuma mutumin yayi tafiya shine matar ta koremu, tunda dama ba'a son ranta aka kaimu gidan ba"
   
    "Tun yaushe ta koreku"
   
    "Jiya da daddare, kuma dama kullum sai ta zaneni, tayi ta zagina tana sani aiki mai wahala"
    
    Mutumin ya kalli matarsa wadda tunda na fara basu labari take zubar da hawaye, yace "Ki kalli ikon Allah, ace yaro kamar wannan shi yake dawainiya da kansa da yarinya jaririya wadda ko shekara ba lallai tayi amma a rasa mai rike su kawai saboda iyayensu sun mutu!"
   
    Idonta fal da hawaye tace "Wannan rashin imani da mai yayi kama? yanzu kenan da in dai bana mutum bane babu ruwan wani dashi?"

    Mutumin ya kalleni yace "Yanzu idan na daukeka na tafi da kai gidana zaka bini, ka zauna a matsayin dana"

   Nayi saurin gyada kai nace "Eh zan yarda!"
  
   Yace "Saboda me zaka yi saurin yarda dani bayan baka sanni ba?"

   Nace "Kawai don kanwata ta samu kulawa ne"

   Yace "To shikenan matata zata reneta ta shayar dasu tare da wannan 'yar tawa" ya nuna jaririyar dake hannunanta.

   Nace "To na gode"

   Yace "Kai kuma zaka zauna a matsayin babban dana wadannan kuma kannenka" ya nuna 'ya'yansa maza biyu dake kusa da matarsa.

    Nayi murmushi nace "Eh zan zauna"

    Yace "Insha Allahu ba zaku rasa abinci ko suttura ko gurin kwana ba, kuma mu ba zamu dinga dukanka ba, ba zamu dinga sa ka aikin wahala ba"

    Matar tace dani "Kayi karin kumallo kuwa?"

   Na girgiza kai

         *Alkhamis KSA*

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now