12

32 1 0
                                    

                 HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                       
                          *page 12*

      

         Da gari ya waye da wuri Mas'ud ya shirya ya tafi asibiti ba wai don duba jikin mamansa bama kawai har da sanin, shin abinda yake ji akan Yasira itama tana ji ko kuwa shi kadai yake ta nutso da malafa.......?

       Da zuwan Mas'ud ya tarar da Yasira tana karatun kur'ani da wayarta, don haka sai wuce wajen Hajiya Hala ya dubata sannan ya zauna a kusa da ita yana satar kallon Yasira, sai data dau lokaci tana karatu sannan tayi addu'a ta juyo ga Mas'ud ta gaishe shi, ya tambayeta mai jiki, sannan ya dan jata da hira suna hirar yake bata labari cikin yanayin bugun ciki.

      "Jiya kwata kwata ban yi barci ba, sai gabda asuba sannan na dan samu na rintsa"

       "Ni kaina daren jiya ban ko rintsa ba yadda naga rana haka naga dare"

       "Ke kuwa me ya hanaki barci haka?"

       "Abinda ya hanaka barci nima shi ya hanani"

     "Eh mana, ba rashin lafiyar mama ne ya hanaka barci ba? nima shine ya hanani, gashi dama kuma ni ban taba kwana a asibiti ba sai yanzu"

      "Gaskiya ne"

       ***            ***          ***            ***

         A can gidan Yasir kuwa, Yasir yana kwance yana barci a dakinsa sai Badrah taje ta buga masa kofa, Yasir ya taso yazo ya bude kofar sai yaga Badrah.

        "Ummi kece da kanki?"

         "Nice, nasa masu aiki sun dafawa  su Yasira abinci ko zaka kai musu?"

         "To Ummi bari nayi wanka na shirya sai na kai musu, daga nan sai na wuce office"

         "A'a Yasir, kamata yayi ka kai musu yanzu don Allah, jiya ma mantawa nayi wallahi ban saka ka kai musu ba"

        "Jiya ai Mas'ud ya kai musu abinci da rana kuma da muka tashi daga office yaje restaurant ya siya musu abinci ya kai musu"

        "Ai abinci restaurant bai kai na gida, kawai ka kai musu idan ka dawo sai ka shirya ka fita"

        "To Ummi abinda kika ce haka za'ayi"

        "Bari nasa a kai maka shi mota kafin ka fito"

        "To Ummi"

        "Kasan da a ce Zayyan ko Rayyan suna nan da daya a cikinsu ne zai jewelry ba kai ba"

        "Na sani Ummi"

       Sai ya koma ciki ya saka jallabiyya ya dauko key ya fito, yana fitowa sai suka yi kacibis da Yusrah ta nufo shi, sai ta ganshi da key.

        "Har ka tashi fitama zakayi kenan?"

        "Wallahi asibiti zan je na kaiwa su Yasira abinci"

        "To jirani na dauko hijabina sai na rakaka nima na dubata"

        "To kiyi sauri"

        Ya tsaya a wajen har ta shiga ta fito sanye da hijabi, sannan suka jera suka nufi motorpark, suna zuwa suka tarar da Shukrah a tsaye a jikin motar Yasir.

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now