6

32 3 0
                                    

HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

*page 6*

RASHIN LAFIYAR ABDUSSATTAR

Abbanmu ya kamu da wata irin rashin lafiya mai wuyar sha'ani baya iya yin komai da kansa sai anyi masa, ga tsufa ga rashin lafiya, anyi maganin asibiti anyi na Islamic amma Allah bai kawo sauki ba, don haka sai na yanke shawarar daukarsa aka kaishi kasar waje. Da zamu wuce na kira kowa na gidan muka zauna a falo na fara jawabi:

"Abinda yasa na taramu anan akan rashin lafiyar Abba ne, ciwon nan ya ki ci ya ki cinyewa don haka na yanke shawarar kaishi kasar waje domin nema masa magani, wasu zasuyi mana rakiya wasu kuma zasu zauna a gida, to wadanda suke a gida su rike gidan da amana da kulawa sannan kuma su dage da yiwa Abba addu'ar Allah ya ya bashi sauki Allah ya yaye masa yasa makankarar zunubai ne"

Nan na zabi Dayyab da Shukrah a matsayin wadanda zasuyi min rakiya, nabar Umminmu Badrah da Yasira da Zayyan da Rayyan da Zayyad a matsayin babba a gidan. Suka yi mana rakiya har Airport basu bar wajen ba har muka tashi.

Bayan saukarmu a kasar da muka je kai tsaye wani babban private Hospital muka wuce bayan mu cike duk wasu sharuda da dokoki aka kwantar dashi. Haka muka cigaba da jiyyar Abba na tsawon watanni, na kan koma gida duk bayan one week don ganin yadda harkokin kamfani suke tafiya na kuma duba 'yan'uwana da Umminmu don ganin halin da suma suke ciki.

Da naga abin bana kare bane sai na dawo da Dayyab da Shukrah gida, na kai Umminmu Badrah da kuma Zayyad muka cigaba da jiyyarsa tare, sannan duk wata ranar Monday sai na dawo gida sannan na koma ranar Tuesday.

MUTUWAR ABDUSSATTAR

Wata ranar Monday na dawo kasar nan daga can zuwana kenan gida don ko office din ma ban kai ga zuwa ba, sai Badrah ta tayi min waya tace in koma akwai matsala, hankalina yayi matukar tashi dole haka na koma zuciya cike da fargaba. Bayan na koma naje na tarar dasu gaba daya a wajensa, sai cewa yake yi "A kira min Yasir! A kira min Yasir!! A kira min Yasir!!!"

Na karasa da sauri na tsuguna a gaban gadon na kama hannunsa na rike nace "Abba gani nazo"

Ya kalleni sannan ya kalli Zayyad da Umminmu Badrah ya umarcesu dasu fita, take suka fita kuwa ni kuma na jawo kujera na zauna ina kallonsa.

Yace "Yasir abinda yasa na kirawoka akwai alamun da suke nuna ciwon nan nawa na ajali ne, ba zan tashi ba mutuwa zanyi. Don haka nake son nabar maka wasiyya koda rai zai yi halinsa, ina son ka cigaba da rike gidanku a matsayinka na babba, yanzu dukkanin wani nauyi zai hau kanka, ka rike kannenka ba wani bambanci kamar dai yadda kake yi a da, sannan ka cigaba da rufe sirrin nan ban yarda ka bayyana shi ga kowa ba. Sannan shima kamfani ka cigaba da tafiyar dashi kamar yadda kake yi da ina raye"

Ina ta kallonsa nace "Abba ai duk nisan gari wata ran za'a jeshi, ko ban fadi sirrin nan ba dole idan aka zo rabon gado gaskiya zatayi halinta, don kuwa ni da Yasira bama da gadonka."

Yace" A'a Yasir a hada a raba muku gaba daya har Yasira kada a ware kowa duk daya kuke a wajena duk ina kaunarku"

Nace "Abba ai ba haka Allah yace a yi ba, ni da Yasira bama da gadonka idan kuma har muka ci to mun ci haramun kuma Allah sai ya kamamu kuma ya konamu"

Yace "To ai da amincewata kuma ni nace ayi haka, ba dukiyata bace? ni nasha wahala na tara kayata, don haka ni zan fadi yadda za'ayi da ita, kuma idan an raba duk sauran kannenka ka karbe gadon kowa ka rike masa sai sunyi hankali sannan zaka basu"

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now