7

31 3 0
                                    

              HAWA DA GANGARA

*Daga Kundin ✍️📚✍️*
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman

                        *page 7*

       Zayyad yace "A cikin rabon ban ji ka saka kamfani a cikin rabon ba"

       Nace "Eh shi ba'a kai ga raba shi ba"

       Zayyad yace "To shima muna bukatar a raba shi kowa yasan matsayin sa!"

        Nace "Shikenan an gama ai hakkinku ne. Kai kuma meye taka tambayar." na fada ina kallon Dayyab.

         Dayyab yace "A cikin rabon banji ka sa kanka ba kuma banji kasa Yasira ba, ko me yasa?"

        Shukrah tace "Nima abinda nake so in tambaya kenan amma don ganin Ummi tayi shiru shi yasa nima nayi shiru, amma don Allah yaya muna son sanin dalili ba wai don muna jayayya da kai ba, mun yarda da kai mun san ba zaka taba yin wani abu mara hujja ba"

       Nace "Tabbas ni da Yasira babu mu a cikin wannan rabon!"

       Dayyab cikin sauri yace "To saboda me?"

       Na kalli Badrah naga tana hawaye tana girgiza min kai alamun kada na fada, na kallesu daya bayan daya naga kowanne alamun tuhuma a fuskarsa.

      Na mai da kallo ga Badrah nace "Ummi kiyi hakuri ki yafe min amma yau zan bayyana gaskiya a garesu don kauda zargi saboda ranar wanka ba'a boyon cibi"

      Na kalli Yasira naga ta kura min ido dauke da alamun tambayoyi barkatai, sai nace "Gaskiya ne cewa ni Yasir da Yasira kanwata bamu da gado a cikin duk abinda Abba ya bari shi yasa ku kaga ba'a raba damu ba dalili kuwa shine saboda mu ba Abba da Ummi bane suka haifemu......!"

      Kaf dinsu babu wanda bai girgiza ba da jin wannan labari.

       Shukrah ce ta taso gabana ta zube a kasa tare da rike hannuna tana kuka tace "Don Allah yaya kace min wannan labari ba gaskiya bane, ko kuma kace min mafarki ne nake yi....!" bata karasa maganar ba kuka yaci karfinta.

       Badrah da Zayyan da Rayyan suma kukan suke yi mai tsuma zuciya, ita kuma Yasira fuskarta ba yabo ba fallasa ita ba mai bakin ciki ba ita ba mai farin ciki ba, kawai sai muka ji shewa da dariyar Zayyad da Dayyab har da tafawa.

        Zayyad ya kalleni yace "Amma gaskiya mutumin nan kason wuce gona da iri, ashe kai da ba dan gidan nan bane babu abinda ya hadamu kai bare ne, amma shine ka dinga azabtar damu kana hanamu jin dadin rayuwa ka zame mana karfen kafa a rayuwa!"

     Dayyab yace "Kuma yasan bashi da gadon Abbanmu amma haka ya kankane ya rike a wajensa, da bamu ce a bamu namu ba da ban san ko ma cinyewa zai ba!"

       Shukrah cikin bacin rai tace "Kai yaya Zayyad da yaya Dayyab wannan wacce irin mummunar dabi'a ce sai kace......!"

       Zayyad ya katseta da hantara yace "Ke dahalla yi mana shiru ko kuma ranki ya baci yanzu"

       Badrah ta tashi a fusace taje ta mari Zayyad ta mari ta mari Dayyab, tace "Koma dai meye shi dan'uwanku ne babu abinda bai yi ba akanku, kuma har abada shi din danmu ne ni da Abbanku!"

       Dayyab yace "A'a Ummi, wannan maganar taki ma babu ita a cikin abinda yake na gaskiya don haka ki danna zero domin goge ta......!"

      Na tashi nayi kan Dayyab ina cewa "Kai Ummi kake karyatawa.......?"

     Zayyad yasha gabana yace "To kai meye naka a ciki? ai mahaifiyarmu ce ba taka ba......!"

       Badrah ta sake marin Zayyad tana cewa "mutanen banza mutanen wofi!"

HAWA DA GANGARAWhere stories live. Discover now